MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Sulaiman kuwa tunda ya shige Dakinsa bai kara fitowa ba sai da ya samu natsuwa yayi wanka ya sauya kaya gabadaya yana jin kansa kamar bashi ba Dakin Laila ya koma ya Binciki wayoyinsa duk sun mace ba Chaji sai ya koma Dakinsa ya jonasu achaji kana ya sauko kasa Da su magajiya yaci karo domin tun bayan Fitar Laila suke nan falo cirko cirko Magajiya na ganin Sulaiman ya sauko ta saki Hamdala acikin Ranta gabadayansu suka Zube suna gaishesa ya amsa cikin Sakewarsa kamar koyaushe yana sanye cikin Riga da wando na wani Farin yadi sai dai duk ya rame kamar bashi ba.
Magajiya ta dago kanta tana Fadin”Barka da dawowa yallabai..!
Mirmishi yayi bai ce komai ba yana dai Wurga idanuwansa acikin Falon Lokaci daya kafin yace”Ina su wasim ban ji motsin su ba ko Sani yakai su makaranta ne..?
Kan Magajiya na kasa tace”A”a Ranka ya dade ai sani ya dade rabonsa da gidan nan Sai ranar dayazo ya kaiku Siyyayya kai da Hajiya Laila..!
Shuru yayi yana Tuna Ranar shifa abubuwan ganinsu yake kamar amafarki.
Kada kai yayi kafin yace”Suna ina..?
Da sauri tace”Suna gidan su Hajiya Sunaima ranka ya dade chan takai su Saboda Zirga zirgan kai su makaranta..!
Sulaimsn wani bakinciki sai da ya Ziyarcesa idanuwansa suka kara Kadawa Cikin Damuwa yace”Magajiya bani labarin duka abubuwwn da suka faru..!
Dagowa tayi tana kallonsa ya gyada mata kai alamun Tabbatarwa kanta na kasa ta fara Rattabamai tunda daga Ranar farko da Laila ta tarasu da karbe key din mota da sallaman sani da Duka Dokokinta da yadda aka Daina kai su wasim makaranta da luch dinsu da Dawaniyar Sunaima akan yaran da duka abubuwan da suka Faru.
Kafin ta gama Sulaiman ya kusa suma Saboda Takaichi harda zuwan Habib da Saifullahi da abubuwan da suka Faru Laila ta Cutar dashi Cutar da Har Abada bai jin zai iya yafe mata bai kara mgana ba sai da ya wucesu kamar zashi Dakin sunaima sai ya Fasa Domin wata zuciya ta sanar dashi ba yanzu bane Lokacin Daya Dace ba..Lokacin daya dace yana zuwa in kagama da wannan mtsalan Dake gabanka yanzu..
Tunanin haka yasa ya juyo yana Kallon su Samira dako kwakwaran Motsi basu yi ba yace”Ina su Hajiya..!?
Magajiya ce ta mike ta numamai da Hannu bai kara cewa komai ba ya Juya ya Fara takunsa cikin natsuwa har zuwa Dakin da su Hajiya ke Ciki da Sallama ya shiga Lokaci Daya da Sallama yana sawo kai ya iske Hajiya na Waya tana kuka Cak ya Tsaya yana kallon Safiya ita kuma da Sauri tace”Abba ne..!
Kai ya kada kafin ya gyara Tsayuwa Jingina yayi da bangon Dakin Lokaci Daya Hannayensa kan Kirjinsa Hajiya kuwa na jan majina tana Fadin”Abban su bansan haka zata faru ba..Ban taba Tunanin haka ba ashe kasan abunda ke Faruwa har waniLokaci da saninka ka Boyemim..?
Abba Dake shashen Hajiya karama Dawowarsa kenan ya shiga wajen Hajiya batanan shine shigowarsa kenan tace sun fita da Safiya haka kurum yasan Fitar bata Lafiya bace Tunda ai ya barta kwance ba Lafiya da Safe yana Kiranta Tun kafin ya Tambayeta ta fara,kuka tana Zayyanamai abubuwan dake faruwa da wanda suka faru yau din nan..
Bai goyi bayanta ba ya cigaba da mata Fada yana nuna mata Kuskuranta Daga karshe ya sanar da ita Habib yazo Har Office dinsa ya Fadamai komai,Abba ya kara da cewa”Aranar da naso naje kargi nayi ma maimartaba bayani kika tsshi da Rashin Lafiyar nan Dalilin dayasa ban je na Fadama takawa ba..!
Hajiya tana share Hawayenta tace”Ni yanzu daganan kargi zan wuce..Ta inda aka hau ta nan ake sauka..Wlh Tsakanina da Salame Allah ya isa Duk da kanwarka ce sai na fada taci Amanata.!
Abba yace”Kada ma ki saka haka aranki..Salame koda tana kanwata ta aikata abunda yake Haramun ne Zabba’u ba ga D’ana ba dake matata ba Nafi jin Zafin yadda taci Amanar kaunar Dake tsskaninku Zabba”u yadda kikaso hada jini da ita bai dace da ita ba sam kuma na Tabbata Maimartaba zai Dauki mataki Daidai da yadda zai Hukunta kowa..Saboda haka ku isa kargi nima gobe nida Hajiya karama muna Hanya da yardan Allah..!
Hajiya na sharan majina tace”Shikenan Abbansu.!
Daga haka suka katse kiran kana ta Dago tana kallon Sulaiman wanda ya kariso gabanta ya Durkusa ya saka Hanny yana share mata hawaye Cikin Rauni yace”Hajiya ki Daina kuka komai ya wuce..!
Hannunsa ta Damke tana Fadin”Hakane saraki..ba ina kukan komai bane sai na kukan ashe dan”uwanka wanda kabama yarda zai iya cin Amanarka..?
Dan yake yayi kafin yace”Halin dan Adam kenan Hajiya..!
Hajiya tace”Saraki ka yafemin..Ka yafemin duk nice silar shigarka halin daka shiga da ace na barka da matarka wacce Allah ya baka da duk haka bata Faru ba don Allah…!
Da sauri ya Rufe mata baki ya girgirzamata kai cikin rawar murya yace”A”a Hajiya ni bakimin komai ba..Sau tari daman wani abun na Faruwa damu ne saboda mu hankalta mu koyi Darasi Hajiya..!
Kai ta gyada alamun Tabbatarwa kafin tace”Tabbas..!
Safiya na gefe tace”Ina fatan ta kama Hanyar Jos yanzu.?
Kai ya gyada kafin yace”Ta tafi..!
Hajiya tace”So nake kafin ta isa gaban Salame mu isa gaban Maimartaba mu warware masa komai Saraki..Haka ma Abbanku yace shima shi da Hajiya karama suna tafe goben..!
Cikin Amincewa yace”Yadda,kikace Hajiyarmu.!
Yafada Lokaci daya yana Mikewa Kafin yace”Bari naje na duba wayata na Jonata achaji gabadaya saboda kira Chajin ya kare..Ina so na Kira sani yazo ya kaimu chan kargin..!
Da sauri Safiya tace”Basai ka kirasa ba Tare muke da Direban Abban Hidaya..!
Kallonta yayi kafin kuma ya kada Da yaso Hajiya tabari sai gobe saboda yana so yaje yaga su Wasim yana kewarsu,Sannan yana so yaga Habib da Saifullahi sai dai kuma wannan mtsalan tasha gaban komai bari su tafi in ya isa chan sai ya kira su suyi mgana.
Sunaima tana cikin batasan halin da ake ciki ba Da La”asar sulaiman da Hajiya da Safiya suka Dauki Hanyar Kargi a hanya ne ya kunna wayarsa sai da ya kusa kwallah Saboda ganin kiran mutane Kamar me duk baisan anyi ba Kiran Farko Abba ya Kira sukayi mgana Abba godiya kawai yakema Sarki Allah ya bama Hajiya karama da su Sadiya suka gaisa daahi duk da Hajiya karaman ce kadai Abba yayi ma bayani sama sama ita kan ta kara Tsorata da Rayuwa su Sadiya kuwa karyan Ciwo Abba ya lankayama Saraki saboda mganace ta Zumunci bai kamata yara su shigo Ciki ba.
Daga Abba Saifullahi ne Mutum na Biyu Daya Kira alokacin yana Ma”aikata yana Tsaka da aiki sai ga Kiran Sulaiman mamaki ya kamasa sai kuma Farimciki ya Biyo baya yana Dauka yace”Megarin Kargi kai ne..?
Saboda ya tabbatar da shine yace”A”a sai dai maigarin karaye..!
Saifullahi ya kyalkyace da Dariyan Farimciki kafin tace”Allah mun godemaka..Wlc back Mr sulaiman Aliyu kargi..!
Sulaiman yace”Nagode Saifullahi..Yanzu muna Hanyar kargi ne..!
Saifullahi yace”To fa me ya faru Haka da gaggawa..?domin Sunaima batayimai bayanin komai ba
Sulaiman yace”Is a long story..In ta kama kaima gobe zan ce ka taho ayi komai agaban ka ka wuce aboki kai Dan”uwana ne..!
Daga haka suka cigaba da mgana kafin su yanke Daganan bai kara Kiran kowa ba ya bari komai ya Daidaita ya kishigida da Kujeran Motar shi yana gidan gaba ne Sunaima kadai yake Tunawa Duka Momment dinsu bai bacemai ba su ke dawomai yana Tuna daman ita din mai kirki ce shine bai sani ba ya sani dawowa Hayyacinsa da yayi kashi Tamanin Duk kokarin Sunaima ce yaushe zai manta da Kokarinta akansa..?
Sun isa Kargi da mangariba Sulaiman masallaci ya wuce tunda maimartaba na chan su kuma suka shiga cikin gida Dakin Fulani suka sauka sukansu sunyi mamakin ganinsu haka Kodaga ganin Hajiya Zabba”u ba Lafiya duk ta Fige.
Bayan gabatar da sallah da cin Abinci Sulaiman na tare da maimairtaba Dayaji Dadin ganinsa afada saboda shi yasa aka tashi fada da wuri,Karfe Tara na Dare suna Falon cikin gida na maimartaba,Sai da sukaci Abinci tare suka koahi kana maimartaba ya Sauke Rawanin kansa yana kallon Sulaimam cikin Dattakonsa yace”Saraki me ya faru..?Domin nasan hakanan baza kuyi zuwan yammah ba..Gashi kacemin tare kuke da Mahaifiyarka da kanwarka kafin nan ma Ina ka shigene kwana Biyu har wayarka na kira baka Daga ba Ina Fatan kana Lafiya duk da naga Duk kayi Dan wuya ina Fatan bangaram matan naka lafiya da wajen aikanka ko.!?
Kan Sulaiman na kasa Har maimartaba ya gama bayaninsa sannan ya Dago Cikin Rauni yana Fadin”Ba Lafiya ba Ranka ya Dade..Duka Tambayoyinka ne Dalilin zuwarmu wajenka..!
Maimartaba ya Kuramai ido yana Nazarinsa kafin yace”Me ya Faru Saraki Daure ka fadamin kafin Hankalina ya tashi..!
Bai yi musu ba ya gyara zama kansa na kasa ya Rattabama maimartaba komai Harda neman masa mganin da Sunaima tayi ya fadamai da abunda ya Faru yau da labarin da yaji wajen magajiya da wanda Hajiya ta Fadamai Habib yaje yasanar ma Abba kafin ya Gama maimartaba ya katsesa Cikin Bacin rai”Yanzu ita Salamatun ne takai Jinin Zabba”u gidan Boka..?
Kamsa na kasa ya gyada kai yana Fadin”Eh Ranka ya Dade duk tsawon wannan Lokacin bana cikin Hayyacina da Taimakon Allah dana addu”an Mutane akaina yau din komai ya kare..Na riga na Tura ita lailar din gida Ranka ya Dade..!
Maimartaba yayi shuru ya Dade bai ce komai ba Kansa ya Kulle Ransa ya baci acikin zuru”arsa Yarsa ta Cikinsa Abu Daya yafi Raunanasa bai kamata Salame tayi ma Zabba”u haka ba in yayi Duba da duka Soyayyar da kaunar dake Tsakaninsu.
Lalle Salame taci Amana kuma zata gane bata da wayau.
Cikin Shakewar murya yace”Kiramin ita Mahaifiyarka taka da ita kanwar taka..ku dawo tare..!
Ba Musu ya mike zuwa Cikin Gidan Yana shiga Dakin Fulani ya iske Hajiya na waya cikin Fushi take Fadin”Salame bani da sauran mgana Tsakanina Dake..Mu hadu gaban Maimartaba shi zai mana wannan Hukuncin sannan Daga karshe na barki da Allah Salame..!
Fulani tana Dakin Baki kawai ta Saki tana kallon Zabba”u abunda basu taba jin kan Salame da zabba”u ba Sulaiman bai damu ba yana da Tabbacin Laila ta isa jos kenan ta warware ma Mata komai ta kira Hajiya tana kukan munafurci tana Rokonta ta bari tazo su daidaita kada ta fasa mganar Hajiya tace ta makara.
Jin kiran Maimartaba yasa Hajiya da karfin gwiwanta ta isa Falon takawa bayan gaisuwa Maimartaba ya kalleta kai Tsaye kafin yace”Abunda Saraki yazo min dashi gaskiya ne Zabba”u..?
Kawai sai Hajiya ta saka kukan Cikin kukan take fadama maimartaba komai Duk maimaicin na Sulaiman ne ta karishe da fadin”Ni yau diyar salame taci ma Zarafi Ranka ya Dade..Har mari ta kawo hannu zatayi yarinyar nan Sunaima ita da Sulaiman suka tare ranka ya Dade..Raina yana kuka Ace yau ni Salame zatakai sunan D’ana wajen Boka da sunan Yarta ta mallakeshi Ranka ya Dade Saurin me Salame ke yi ne..?in tayi Hakurin Tunda Akayi auran na Tabbata Saraki bazai Wulakanta Laila ko Saboda ni ammh yau ji sakayar datayimin cin Amanar Raba Saraki da komai nashi fa..!
Ta karishe cikin kuka Maimartaba bai ce komai ba illah Safiya daya kallah kafin yace”Safiya me kika sani kan wannan mganar..?
Safiya ta karkace zama ita ta kora nata Jawabin ta karishe da Fadim”Ranka ya dade nasan kai adali ne kuma zakayi adalci kuma baka yanke Hukunci sai da Hujja..Saboda haka zaka iya bincikawa Tundaga kan ma”aikatan Dage gidan ya Saraki zaka san gaskiyan sannan ita Lailan da bakinta ta fada Ranka ya Dade ka Kirata katambayeta da kanka kaji daga bakinta Allah ya taimake ka..!
Maimartaba yayi shiru bai kara mgana ba kafin chan ya dago kansa Wayarsa Dake gefensa ya Dauka yayi latse latse kafin ya saka a kunne ba jimawa ya amsa sallama kafin yace Cikin Dattakonsa murya cike da bacin rai”Salamatu gobe dake da Yar wajenki da Megidanki ku iso kargi ina son ganinku.!
Daga haka ko cewarta bai jira ba ya kashe wayar dagachan bangaran Hajiya Salame ta kalli Laila Dake kan gadonta Zazzabi ya Rufetaa tunda ta iso saboda kuka ta Dora Hannu akai tace”Shikenan Laila kin kashemu..Yanzu maimartaba ya Kirani yace gobe yana neman mu a Fada da gaggawa..!
Laila daga kwancen ta fashe da kuka Tana Fadin”Mommy me yasa kika jefamu cikin wannan halin..?
Hajiya Salame ta Dafe kanta sai yanzu Nadama ya shigeta da Tunanin da wani ido zata kalli Zabba”u da mijinta da iyayenta..?tasan Halin takawa Indai ya kamata da wannan Laifin batasan irin Hukuncin da zai Dauka ba kaiconta Tun sanda Laila ta iso da Labarin Lalacewar komai take gudawa ta kira Hajiya Zabba”u saboda su warware komai Tsakaninsu kuma bata saurareta ba tayi ta Kiran Hajiya Zaliha wayarta akashe ita alokacin ta nausa Niger cikin Agadez bazata sameta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button