MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Janafty
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)
Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️
Page 25
Sunaima ta gane kuranta a wajen Sulaiman Ranar daya dawo da Daddare,Daman ai ya fadamata Tunda tace yayi abunda yaga dama in sun koma gida aikuwa bakinta ya yankata Domin datace”Saraki..!
Tana kallonsa sai ya Dage mata gira yana Fadin”Ba wani Saraki malama..Kekikace in muka dawo gida in yi abunda naga dama..!
Dole tayi shuru da bakinta Yaran wajen Magajiya yace ta barsu ta kula dasu,Ita abun ma kunya ya bata Suna ganinta ta Haura Dakinsa ta bar musu yaran washegari koda ta fito Magajiya ta gama yi musu shirin makaranta Dayake suna da Wasu kayan makarantar agida bayan na gidan Inna.
Daga ita har Sulaiman shiryawa sukayi ita tayi Shirin zuwa wajen aiki Shima yayi shirin zuwa Office.
Tare suka fita harda yaran bayan sun karya makarantar yaran suka fara zuwa suka ijiyesu,Daganan Suka biya suka ijiye Sunaima ya kuma mata gargadin in tatashi ta kirasa Sani zai zo ya Dauketa bayason Hawa adaidaitan ne in kuma ta hau to ita da Allah.
Kallonsa tayi alokacin Dayake Fada mata haka dukkansu suna Bayan Mota ne Fuska ta Hade tana Fadin”Ni yanzu Saraki sai ka rika min Allah ya isa ko..?
Kai tsaye yace”Ai bakya jin mgana ne..Mgana baya Horar dake sai an bi daake ta haka..!
Yafada Lokaci Daya yana riko hannunta yana yar dariya Kwace hannunta tayi tana kokarin Bude kofar Motar da sauri ya rikota yana Fadin”Afuwan Anty Sunaima..!
Wani kallo tayi mai kafin tace”Sai ka janye mganarka..!
Kai tsaye yace”Kema sai kin janye Taurin kanki..!
Kallonsa tayi tana fadin”Nice ma mai Taurin kai..!?
Kai tsaye yace”Sosai ma..!
Yafada Lokaci Daya yana Taba kan nata kafin ta ankara ya Sunkuya ya Sumbaci bakinta ido ta waro tana Nuna mai Sani Ido daya ya kanne mata yana Fadin”Barsa in ya gano abunda zai makantar dashi ba ruwana..!
Baki ta Rufe da Hannunta tana Fadin”Saraki…!
Da sauri y tareta da Idanuwansa yana Kokarin kashe mata Jiki wata Murya yace”Ki adana kirana da wannan Sunan yanzu..sai an juma in mun hade alokacin sai naji Dadin amsa miki..!
Kai ta girgiza bata da tacewa domin Saraki yafi karfinta Motar ta Bude ta Fita ya bita da kallo Sai da ta fito kana ta Leka tana Fadin”Na manta ban Fada maka ba..Ina so don AllaH in mun tashi naje na gaida Inna..!?
Ido ya sakar mata kafin yace”A”a ba yau ba..!
Zata kara mgana ya Dakatar da ita”Nace ba yau ba Sunaima..!
Yafada ba wasa a mganarsa bata kara mgana ba ta mtsa baya Sani ya kallah yana Fadin”Mai idon ganin Mata da miji in kagama kallon mu ta madubin muje..!
Sani na Dariya yace”Afuwan yallabai..!
Kai kawai Sulaiman ya girgiza yana Fadin”Allah ya shiryeka sani..!
Daga haka ya tada Motar suka wuce Lokaci daya yana Daga ma Sunaima Hannu itama ta Dagamai.
Ammh taso ya barta taje su yi mgana da Inna ta Fadamata yadda Hajiya Zabba”u ta karbeta wannan karon sai dai Saraki ya hanata Dole ta Hakura.
Karfe Biyu suka tashi aiki ta kirasa ta fadamai ya turo sani yazo ya Dauketa zuwa Gida
Tana komawa akwai gajiya ajikinta,yasa Wanka kawai tayi ta ci abinci ta kwanta sai la”asar tatashi Tayi Sallar ta fita falo ganin bata ga su Wasim ba tatambayi magajiya tace basu dawo ba abun ya bata mamaki har pass 4 sai ta koma Daki ta Kira Sulaiman.
Yana Dauka tace”Su wasim basu dawo ba..!
Kai tsaye yace”Eh Sani nace in ya Daukesu daga makaranta ya kaisu wajen Inna..!
Cikin mamaki tace”Saboda menene..?
Alokacin suna tare da Saifullahi ne yasa ya mike yadan Mai tazara yana Fadin”Saboda Mganar ki ta yau da Safe..Bazai yuyu inaso naci Amarcina yaran na Takurani ba..!
Sai alokacin ta tuna da korafin da tayimai da safe akan yaran ta barsu su kadai wajen magajiya alokacin bai kalleta ba ammh aransa ya gama Tsara yadda zai yi shagalinsa yaran basu Takuramai ba.
Sunaima ta Shagwabe fuska tana Fadin”Kai Saraki…,!
Da sauri yace”Saraki again.?yau kuwa zaki kira saraki sau Dubu In baki yi wasa ba..!
Cikin kunkuni tace”Ni nagaji..!
Yana Dariya yace”Ni kuma ban gaji ba..!
Bata iya mgan ba ta katse kiran Tana Mmamkin Saraki abubuwansa sun fi karfinta Inna ta Kira sukayi mgana Inna tace taji dadin dawo da su Wasim Daman tunda suka tafi gidan ba Dadi sai ta fara kame kame bata so Inna ta Fahimci wani abu abunda bata sani ba Inna ai ita ta haifeta tasan duk wani motsinta aranta Farinciki take daman Akullum addu”arta Allah ya Daidaita Tsakanin Sulaiman da Sunaima.
Inna sai ta bar mganar ta sako mata mganar sakon da Ahmad ya kawo mata,Sunaima ta fara ma Inna bayani ta karishe da fadin”Inna baki ga yadda suka karbeni ba kannensa da Hajiya,tana kuka tana kara Rokona gafara Inna baki ga abun arziki ba abun sai mamaki yake bani..!
Inna na Dariyan Farinciki take Fadin”ba bu abun mamaki da ikon Allah Sunaima..Fadin Allah ne Hakki ga wanda aka Zalunta in baka da Hakki akan Mutum kana zaune sai Allah ya Fitar maka da Hakki..Abaya ta tsaneki ta so Diyar kawarta yanzu kuma da akayi sai Allah ya bayyana Sakayar..!
Sunaima tace”Hakane Inna..!
Inna ta cigaba da Fadin”Shawaran da zan baki shine ki kama mijinki Hannu Bibbiyu da Danginsa Musamman Ita Hajiya Domin wannan Damarki ce Allah ya riga ya warware miki Dukkan Matsalolinki Sunaima..!
Da wadanan yan nasihun suka yi sallama da Inna bayan sun gama waya ta Zauna tana Tauna mganar Inna gaskiya ta fadamata Ya kamata ta Shiryama kanta ko sau Daya tayi ma SAraki wani abun alheri cikin Dimbin Alherinsa gareta da iyayenta.
Zumbur ta mike ta Fice sai Kitchen magajiya da Samira nata aiki Gaisheta suka hau yi ta amsa tana Fadin”Me kuke Dafawa na Dinner ne..?
Magajiya tace”Farar shinkafa da Miyar kaza Hajiya..sai Ferfesun kayan ciki..!
Fuska ta yamutsa kafin tace”Samira ki karisa wannan girkin..Magajiya fitomin da Naman Dake cikin Fridge ki Tafamin Tuwo zan yi da miyar yauki..!
Tana gama Fadin haka ta fice suka amsa mata Daki ta koma ta kara Kiran Inna tace Ahmad na gida Inna tace yana Shagon dayake koyon aikin kafinta Sai tace bari ta Kirashi ta Fadamai yazo wajen Inna ta bashi Bushasshiyar Kubewa yazo mata dashi Inna tayi Dariya aranta Tana Hamdala ta tuna Farkon Tarewar Sunaima gidan Sulaiman duka wadanan Dake daken Tani tayi mata shi daga Zuntu ta kawo mata sanin Sulaiman ma abocin cin tuwo ne Tun Sunaira nada rai tana yawan Siyansu Musamman Tani ke tada yaro Daga Zuntu zuwa Kaduna saboda kuka,kubewa da su Daddawa.
Alokacin da Inna ta Nuna ma Sunaima Fuska ta bata tana Fadin”Inna da kin bar abunki ko na kaisa gidan nan sai dai ya lalace..Ni dai ba girki zan yi ba..Komai hadiman gidan keyi abunsu..!
Alokacin bata matsa ba sanin Taurin kan Sunaima ammh aranta tasani akwai watan wata rana da Sunaima Zata nemesu ko domin Farantama Sulaiman.
Sunaima ta kira Ahmad ta Fadamai ba Dadewa ya koma gida ya karba Sakon wajen Inna wacce ta juye mata Duka na wajen nata ta hada mata Harda Daddawa Akuma aranta tayi alkawarin Zata Kira Tani duka ta Daka mata saboda Sunaima din Lokaci yayi da komai ya Daidaita Sunaima ta karbi kaddaranta Duk da bata Fito ta mata bayani ba sai dai ance Labarin Zuciya a tambayi Fuska.
Sunaima taji dadin ganin har da Daddawa Ahmad bai zauna ba ta bashi kudin mota ya koma gida,sai ga Sunaima an zage an shiga Kitchen alokacin bata tuna da Mijin kanwarta bace Ita kawai tana Hango yanayin Farincikin da Saraki zai shiga yau yana son Tuwo fiye da kowani abinci kuma hakan ya samo asali ne saboda Zabin Maimartaba ne shima Tuwo yana Daya Daga cikin Abincinsa.
Ana kiran mangariba suna gama Komai Tuwan Semo ne tayi da Miyar Kubewa dataji Daddawa,da Nama har da manshanu sai tashin kamshi take suna gamawa ta hada komai awani Katon Tire Harda Zobon data Hadamai Ta bar su samira suna gyara Kitchen din ta sumgumi Farantin zuwa Dakin Saraki aranta tana jin wannan Lokacin ya zama daga shi sai ita ne.
Dakinta ta koma ta yi wanka tayi sallar sannan ta shirya Cikin Daya Daga Cikin Dogayen Riganun da Hajiya karama ta bata saboda ya gani yaji Dadi tayi rolling din mayafin Rigar Yau har dasu shafa jan baki tayi kyau sosai matuka Tana jiran Dawowar Sulaiman,Dakinsa ta koma ta dan kara gyarawa ta Turara Dakin ta shiga Bedroom din ma ta gyaraahi Tsab yana tashin kanshi Kiran Sallar Isha”i yasa ta fito ta koma Dakinta tayi Sallar Isha”i.
Shuru bata ji Sulaiman ya Dawo ba sai ta fara Damuwa Bini bini ta Dauki wayarta tana Dubawa ta fara Tunanin an ya Lafiya wata zuciya tace ki kirasa kiji ko lafiya Sunaima..?
Batasan ma ta Lalubi lambarsa ba sai jin Mganarsa kawai tayi tana Tsaka da Tunani ashe ta kirasa bata sani ba kunya ya kamata da Sauri ta Datse kiran tana Dafe kanta Afili ta Furta”Kash..Me na ke yi ne haka ni Sunaima..!?
Bata samu mai bata amsa ba Sulaiman ya Dawo da kiran sai da ta kusa katsewa sannan ta Dauka Cikin basarwa Tana Daga Kiran yace”Anty Sunaima How far..?kin ga ban dawo da wuri ba ko..?nima fa inata Sauri ne na dawo afara kirana Saraki Saraki ina jin Dadi..!
Baki ta rike tana Fadin”Saraki..!
Dariya ya kwashe dashi yana kallon Saifullahi Dake Driving yana fadin”Saifullahi ma yace lalle Saraki kai mai sa”a ne..!
Da Sauri Sunaima ta kashe wayarta Kunya ya kamata Saraki baisan kunya ba sam wlh,tana ji yana kira taki Dagawa chan sai ga sakon sa.



