MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

After 1 Month…!
Kwance taki a Dakinta Daga Dakin Sulaiman ta gudo daya shiga wanka acikin yan kwanakin nan ta kasa gane kanta kwatakwata,ita dai ajikinta Lafiyarta kalau sannan batajin wani Ciwo sai dai abu daya bata kaunar Sulaiman yace zai rabeta Koda na dan Lokaci ne yanzu zataji ranta ya baci Kafin agama kuwa har ranta takejin wani Kuna tarasa meke damunta Tun tana Daurewa baya Lura har ya Fara ganewa tana Gudunsa bai kawo komai ba yazata irin Normal din nan ne Tunda ba Laifi yana Damunta sosai Kuma yasan tana Kokari.
Yau din ma ya dawo aiki ne ita yau bataje aiki ba sai gobe zata koma Mrning,Har wani Salama ta samu Daya Fita itafa ko Kamshinsa batason ji kwata kwata Tafiso ta zauna ita Kadai wanka yace tayimai taki yimishi bai damu ba ya shiga wanka agurgije ta fitomai da kayan da zai saka ta gudo Dakinta sai dai bata Tsira ba sai gashi ya shigo Tana Daga kwancen Sai ta fara barcin karya gabanta na Faduwa Kada yace zai yi wani abu da ita.
Shi kuma harga Allah bai Fahimceta ba Gadon ya haye bayan ya Zare jallabiyan Jikinsa yana Fadin”Shine kika gudu ko..?na lura a kwanakin fa kin fara zama Raguwa ko muguntar taki ce tatashi..?
Yafada yana Rabawa ajikinta tana jinsa tayi kamar bataji ba Numfashi ta Dauke Kamshin Turaransa har hawa kanta yake yi yanzu ganin taki Motsi yasa ya fara Shafata yana dan matsa Jikinta da Saman Nonuwanta Taki ko Motsi sai abun ya bashi mamaki Tashi yayi ya kunna Wutar dakin Haske ya bayyana Abun mamaki Hawaye ya gani acikin Idanuwan Sunaima Cikin Mamakinta yace”What all dis Sunaima..!
Shuru tayi ta kasa mgana sai kuka Saboda batasan me zatacemaiba, ganin haka yasa ransa yayi zafi Cikin Karyewan Murya yace”Saboda zan kusance ki yasa kike kuka Sunaima..?Saboda zan karbi Hakkina yasa kikayi min mgana kikayi banza dani..?wato ga Dan iska naje na karata..!ko..?
Tana jin haka ta Dago tana kallonsa ta Bude zatayi mgana ya Tashi Daga kan gadon yana Fadin”Shikenan baxan matsa miki ba..Ammh ki sani In dai Hakkina ne kuma kika hanani keda Allah Sunaima!
Da sauri ta Dago Jikakkun Idanuwanta tana kallonsa kafin tace”Saraki Allah ya isa again..?
Kai tsaye ya juyo yana kallonta kafin yace”Nidai ban ce ba..Nace dai in da gayya kika hanani abunda Allah ya Hallatamin keda Allah..!
Daga haka ya wuce Tiolet yana Banko kofar sai da ta tsorata Tunda suka karbi Kaddaransu bata taba ganin Fushin Saraki haka ba sai yau kuka ta fashe dashi me zatace mai..?bataso ya Rabeta tana jin Haushi..?ai sai abun ma yafi haka ta rasa meke damunta kamar wacce akayi ma asiri ta kuma rasa wazata fadamawa ta bata shawara sai ta koma tana kuka Sosai tana jinsa ya Fito ya saka Jallabiyansa ya hau gadon ya kwanta chan gefe ya Juya mata baya bayan ya Rage hasken Dakin yau ne rana ta farko da suka Raba Jikinsu da juna wajen barci Kowa bai samu wani barcin Kirki ba ita kuka ta kwanayi shi kuma Juyi yayi kwana Tunanin wani abu yayi mata Zata Dinga gudunsa duk a iya Tunaninsa bai samu ba.
Asuba nayi ya fice bai sake bi ta kanta ba wajen aiki ma Sai da Sani ya kaisa wajen aiki kana ya Dawo ya kaita Ko gaisuwan da tayimai da Safe Dakyar ya amsa tana so ta bashi Hakuri bata samu Fuskar haka ba Dukkansu da Bacin ran juna suka tafi wajen aiki.
Karfe Biyu zata tashi aiki,Lokaci nayi ta Kira wayarsa daman haka take yi ta Fadamai sun tashi sai ya Turo mata Sani sai dai tamai kira yafi Biyar bai Dauka Shedan sai ya Zugata Ranta ya baci kan me zai mata wannan Wulakanci daman bata saka aka ba Bata Damu da mganarsa na in ta kara Hawa adaidaita bai yafe ba ta Fita bakin asibitin ta Hau adaidaita zuwa gida.
Abunda bata sani ba Sulaiman ya ganta Sanda ta hau adaidaita Suna da Meeting yau yana wajem Meeting din kuma wayarsa na Silent bai ji ba Sai da suka fito Sani ya koma gida baya jin Dadi Sulaiman yace yaje asibiti adubasa Daganan ya je gida ya Huta key din Motar na hannunsa Ganin kiranta yasan tatashi aiki ko Mgana ba basu gama da bakin nasu ba ya bar ma Saifullahi Sallahu yana sauri ya Hau Mota yaje ya Daukota kwata kwata Fushin Dayake da ita bai kai ya Wulakantata ba
Daidai yazo bakin asibitin ita kuma suka fito ita da Aneesa kowacce ta Hau adaidaitan barayinta Har Aneesa na mata tsiyan yau ina Direban Mijinta bayanan kawai tace batason wata mgana yasa tace haka.
Ran Sulaiman ya baci Sunaima bata taba bashi Haushi irin ranar ba wato Ita zata nunamai iyakarsa bari ta hau Yadade bai ce ita da Allah ba.
Saboda bacin rai ma yasa ya juya bai nuna ma ya ganta ba ya koma kamfani Ransa abace bai kirata ba Sako ya Tura mata.
“Kin fi so Allah ya kamaki akan laifin da mijinki yace keda Allah in kika kara..?
Haka kawai yace mata tana Gida alokacin dataga sakon bata Dade da Shigowa ba wanka kawai tayi magajiya ta shigo mata da abinci aranta tana mamakin waya fadamai ta hau adaidaita kamar ta Damu sai Wata zuciyar tace wayaja..?kawai sai watsar dashi Aranat har ya dawo bai nemeta ba Haka itama bata nemesa ba Kuma washegari ma bata jirasa ba ta Shirya taje ta Hau adaidaita tatafi asibitin aranta tana Fadin Allah bazai taba kamata ba Tunda Laifi na wajebsa shi kuma wannan Taurin kan nata ne ya bakanta mai rai ya Fita batunta Satin kaf basa shiga Harkan juna Kowa na Dakinsa gaisuwa kuwa sai in sun hadu Gad da gaf Sunaima ta gaishesa ya amsa adakile ko yan aikin sun Fara Fahimtar akwai matsala haka ma Saifullahi ganin gogan ya Rage walwala sai dai shima Daya tambayeshi yace bakomai.
Kwana Uku suna wannan gabar Matar Saifullahi Khadija ta Haihu aiki akayi mata asibiti.
Janafty
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)
Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️
Page 27
Sunaima batasan Matar Saifullahi ta haihu ba har sai da akayi kwanaki uku da Haihuwar tasani Shima Hajiya ta kira awaya su gaisa sai take Fadamata suna Hanya zasu karaye su yi barkan Haihuwan matar Saifullahi Sunaima mamaki ya kamata Cikin Karfin Hali tace”Matar Saifullahi ta Haihu ne Hajiya..?
Hajiya batayi mamakin Tambayan Sunaima sai tace”Hala tun bayan tafiyarsa baku waya bane..?Don nima Rabona dashi tun ranar daya isa Lagos din..!?
Da farko Sunaima bata gane Mganar Hajiya ba sai da ta karishe mganarta sai ta gane inda ta dosa data kwafsa da tana shirin cewa Shi wane..?sai tayi Saurin gyara bakinta Cikin Sanyin Murya da mamakin Sulaiman tace”Eh gaskiya Hajiya…Inaga shiyasa bai Fadamin ba..!
Tafada tana kara mamakin Sulaiman ashe baya ma agidan bata sani ba yana Lagos lalle ashe shi da gaske yake yi Fushin dayake yi da ita abayana tana Dauka wasa ne sai yanzu tasan da gaske yake yi ita har ga Allah bata Dauka bayanan ba Da kwana Biyu tadaina jin motsinsa ta zata yana kai Dare ne kafin ya dawo tayi barci.
Hajiya ce ta cigaba da fadin”Dayake kisan Taron yan kasuwa ne Abbansu bazai samu zuwa ba sai ya Turasa Kafin ma Matar saifullahin ta Haihu tare suka Tsara tafiyar washegari sai ga Haihuwar yasa ya tafi shi kadai..Shiyasa ma ban kiraki ba nasan in ya dawo zai kawoki..!
Sunaima tace”Insha Allahu Hajiya..Allah ya kaiku lafiya ki gaishemin da Hajiya karama in kun isa Zan kira Hajiya ina so nayi ma Mejego barka..!
Hajiya ta amsa mata Daganan suka yanke kiran Sunaima ta koma ta kwanta Duk kuma sai jikinta yayi sanyi Ta fara kokarin Tattara abunda ta Faru waje daya tsakani ga Allah in tana son gaskiya itace bata da gaskiya itace take kasan sa shi shugabane gareta bai kamata ba sam sai alokacin Taji bata kyauta ba sai alokacin ta san cewa tana cikin Fushin Ubangiji sai alokacin ta gane kuskuranta zamanta da Sulaiman bai taba bata mata da gangan ba Kokarinsa ya ganta Cikin Farimciki ya faranta mata ya Mutumtata ita da iyayenta Shin Sulaiman ya Chanchanci wannan Hukunci a wajenta..?
Bai kamata ba bai kuma Chanchanta ba Sulaiman ya wuce wannan awajenta ya kamata ta nemeshi ta bashi Hakuri ya yafe mata.
Gida gashi ita kadai daga ita sai yan aiki ita tana Daki nan take wuni sai in Zataje wajen aiki tana Dawowa kuma tana Daki bata fitowa falo ko abinci Daki Magajiya ke biyota dashi,Abunda ta samu shine karatun Novels Aneesa ta koya mata sai dai bata bari ya taba Ibadarta ba.
Yanke hukunci kiransa tayi sai dai kira biyu tayimai bai Dauka ba sai kuma Jikinta yayi sanyi sai ta yanke Shawaran Turamai sako.