MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

A Daran…!
7:00pm
Area:Malali Gra kaduna..!
Ta fito katon Haraban Gidan kenan tana Kiciniyar saka Dogon Hijabin Data ke Sanyawa Tana Rufe Jikinta In zata tafi wajen aiki ta makara kamata yayi Tun 6:pm tana asibiti ammh Rigiman Wafiyya yasa bata samu Damar Tafiya akan Lokaci ba
Yau Wafiyan tana jin Rigima ne Tunda Ta Daukosu Daga makaranta suka Dawo Gidan ta yi musu wanka ta basu abinci Wasim yana ta wasansa bayan ya gama ta kunna musu Cartoon suna kallo Banda Wafiyya Dataki barinta ko nan da man chan in Tiolet zata shiga Tana Biye da ita in kuma Tace Zata ijiyeta sai ta Fara kuka.
Ta Tattaba Jikinta ba alanun Rashin Lafiya tasan rigimar ta ce tatashi,Yau din Anty take da ita sosai haka ta Nanike mata yarinyace yar shekaru uku duk inda ta saka Kafa Tana Rike da ita Tana Kiran sunan ta Anty.
Wasim shi ya fita wayau shekararsa Biyar da wani abu shiyasa bai Cika Rigima ba Tunda ta dawo suna Dakinta bata Fito ba Abinci ma Magajiya ce ta Biyosu dashi Kuma har Lokacin bata Huta ba Tana Wahala kan yaran ko kayan makarantasu Data wanke a compound din Tsakar Gidan Wasiyya kin yarda da tayi Magajiya ta Riketa tayi Tare sukayi wankin Duk ta Jika Jikinta Sai ta gama ta sunkuceta sukayi Dakinta Tana ganin Sabuwar mai aikin da akawo Daga Kargi Samaira Tana Lekensu bata bi ta kanta ba daman ita Tun zuwan Samira bata yarda da ita ba tasan akawai manufar zuwanta bata taba Bita kanta ba Tana jira wata Rana ta Shiga Gonarta ne ta gane bata da wayau.
Allah ya taimaketa bayan ta mata wanka ta bata madaranta Sai ta samu Barci itama wankan tayi a gurguje ganin ta makara ta gama Shiryawa kenan Wasim ya kawo mata Tarkacen Homwork dinsa na makaranta bazata iya Ture Aikin ya”yan nata ba yasa ta Zauna ta koyamai tare sukayi aikin basu barta ta Fita ba sai da ta Kira Magajiya ta Dauke hankalin Wasim kana ta Fice Jaka a hannu Hijabi ma haka ko Sallar mangariba bata yi ba ta bari sai ta isa asibitin tayi achan Tunaninta Daya na yadda Zata samu abun Hawa a wannan Daran
Tana Fitowa da Samaira ta Fara Cin karo kamar wacce ke gadin Lokacin Fitarta,tana kuma ganinta ta koma Cikin Dakin da aka Sauketa Tun zuwanta Sunaima ta tabe baki bata Damu ba ta Fice zuwa Haraban Gidan
Sai da tagama Daidaita kanta kana ta Karisa suka gaisa da Megadi ya Bude mata karamar Kofa ta Fice yana mata Fatan dawowa Lafiya Lokaci daya yana mamakinta Duk Tarin Motocin Dake Haraban gidan Tunda yake da ita Tun kawota gidan amtsayin matar yallabai bai bata ganinta a Mota ba sai dai adaidaita,Gaskiya hakan ba Dacewa bane Tunda Yallabai yana dashi hakan kamar bata sunan Asalinsa ne da nasabarsa.
Sauri take ta Zabgawa ganin anguwan tsit daman ai haka take ba Jama”a,Sai Wurgar Manyan Motoci na alfarma bama Adaidaita balle ta saka Ran hawa ta isa da wuri daman in ta samu sai dai da Rna in sun shigo da pasinja ammh ba irin wannan Lokacin ba.
Tafiya take yi har tayi nisa Gajiya Tayi ta Dakata Tana kallon Siririn agogon mata na gayu Dake Hannunta 7:20pm har ta wuce kanta ta Dafe Tana Tunanin mafita domin tamakara yau bataje wajen aiki kuma batasam Wani Lokacin zata bata kafin tasamu abun hawan ba.
Yana gaban Motan yau bai shiga baya ba Ransa ne abace yasa kwata kwata baya Cikin natsuwarsa Wayarsa yake Tabawa Hankalinsa baya saman Hanya Sani kuma na Faman Tukinsa Cikin kwarewa.
Sun karyo kwnaar Layin Kayattacen Gidan nashi Ya Dago kansa yana Fadin”Sani wai ba mai amotar ne da kake Tafiya sannu sannu..?mintinmu nawa da baro kamfani har yanzu bamu kawo gida ba..!
Yafada daidai Lokacin da Idanuwansa Cikin Haskem Lantarkin Daya Zagaye ko”ina na gidajen Dake wajen ya Haskomai Fuskarta Tana Tsaye Gefen Titi Tana gyara zaman jakarta Tana kuma kallon Titi sosai kamar tana Jiran wani abu.
Wani Takaichi da Malolin abu ya Taso ya Rufeshi Daman yana Cikin Bacin rai sai ta karamai har bai ji sanda Sani ke faman bashi hakuri ba.
Bakincikinsa Daya sai an dangatashi da ita In banda Salon Cin Mutimcin mene wannan..?yarinyar nan ba karamar mara Mutumci bace ya gama Lura da ita Tsaf.
Dauke kansa yayi kamar bai ganta ba Har suka Gotata Sani Ne ya ganta sai yadan Rage Gudun Motar yana Fadin”Yallabai kamar fa Hajiya nagani Tsaye bakin Titi..!
Wani kallo Sulaiman ya sakarmai Dayasa ya Take Motar bai Shirya ba.
Hon Sani ya Zuba Megadi ya taso ya Bude get din suka Sulala Ciki kusa da Mota Kirar 4matic suka Tsaya Ko Jira bai yi abudemai ba ya Bude da kansa ya Fito ko kafin megadi ya kariso yana gaishesa ya Rika ya Bude Gidan baya ya Dauko karamar Jakar Briefcase dinsa da Madaran youghourt na kamfaninsa a leda da Tambarin kamfanin,Dazu kafin ya baro kamfani yayi ma Habib waya manager sa mai kula da Kamfanin nasa yace ya bama Daya Daga Cikin aget dinsu ya kawoma Madara DA Fura Office guda Biyu ya Dauki Daya ya bama Saifullahi Daya domin duk kwanan Duniya bai kwamciya bai sha Madaran nan da Fura ba.
Sama sama yake amsa gaisuwan na Auwalu maigadinsa kafin ya Fara Taku zuwa Kofar da sadasa da Babban Falon Gidan nashi Sai kuma ya tsaya Cak kafin ya Juyo yana kallon Sani Cikin Kaushinsa yace”Kaje ka Dauketa…!
Sani Dayaji abun kamar Daga Sama yace”Ita wa..?
Hararansa Sulaiman yayi kafin yace”Bansani ba!
Yafada yana juyawa ya Cigaba da Tafiya Sani kansa ya shafa yana Dariyan Dramansu da ogan nasa ai ba yau suke Tare ba yasan Halinsa Ciiki da bai
Juyawa yayi ya shiga Motar ya sake Ficewa Daga Gidan Tana nan inda suka Barta bata samu adaidaita ba Agabanta ya Tsaya kafin ya Sauke Glass din Motar yana Fadin”Hajiya barka..Shigo muje..Yallabai yace nazo nakai ki..!
Tsam tayi tana kallonsa Yallabai.?
Dazu fa ta gansu sanda suka wuceta Domin ai ta gane motar bakar Prado ta Zamani ganin basu nuna sun ganeta ba yasa ta kauda kanta da ace Tana da wani Zabi bazata shiga Motarshi ba ammh Tuna bata dashi yasa ta Bude Gidan gaba ta Zauna Tana cema Sani Tagode Daganan bata kara mgana Har yakai ta Bakin asibitin tace ya Dakata ta Sauka wannan Shine karonta na Farko Data Taba Shiga Motar tasa.
Shi kuwa yana Taka Kafarsa da bakaken Sawun cikin Takalminsa na Fatar daminsa yana ayyanawa aransa “Ko bakomai Saboda Noory..Ammh ba Domin Halinta ba..!
Haka yake fada har ya Taka Matattakalan Hawan saman Bene Inda Jerin Dakinsa yake Tun a baya kafin Rayuwa da kaddara ta Juya Da rayuwarsa ahaka.
Shakira
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)
Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️
Kuyi hakuri da Rashin jina kwana Biyu wani Sabgace tatasomin ban yi alkwarin samun update kullum ba sai dai ku karbesa duk lokacin da kuka gansa..Nagode..!
Page 3
Sai da yayi wanka yayi Sallar Isha”i ya saka Madaransa da Furansa cikin karamin Fridge din Dake Falon nashi kana ya fito Domin ganin ya”yan nashi Sanye yake da Tattausansun Riga da wando na barci masu ruwan Duhuwa na kamfanin PJM,hannayensa Cikin aljihun wandon Barcin ya sauko kasa da Magajiya yaci karo Tana ta Safa da marwa Tsakanin Kitchen da Kayattacen bangaran makeken Dining din cin abincin Dake chan yammah da Falon.
Har ya sauko bata ma Lura dashi ba Magajiya mai aikinsu ba yarinya bace a kallah a shekaru zata bama arba”im baya Daga garin kargi take Mijinta Rasuwa yayi kuma bata taba Haihuwa ba kuma Mijin nata shine mai kula da Dabbobin Maimartaba alokacin bayan Rasuwarsa Magajiya ta Dawo Karkashin kulawar Fada cikin Hadiman Uwargidan Sarki Fulani Shime bayan Haihuwan Aliyu Wasim kenan da Shi sulaiman din ya Bukaci Samun mai taimaka ma Sunaira awanchan Lokacin Maimairtaba yabada Umarnin a basu Magajiya.
Tun achan baya akwai Girmama juna a tsakaninsu dagashi har sunaira suna mata kallon Uwa ce shiyasa take jin Dadin Zama dasu Tayi kukan Rashin Uwardakin iri Hajiya Sunaira,Ammh ko ayanzu bazata Dora komai game da Sabuwar uwar Dakin nata ba abu Daya ta sani bata da kwarammiya da Yawan mgana kamar Sunaira a kowani Fanni suna da bambamci Dabi”u da kuma Hallaya.
Ta duka tana Jera Filet din saman Dining din taji mganarsa Daga sama.
“Magajiya Barka da aiki..!
Yafada cikin kyakyawan Sautinsa da Hanzari ta Juyo tana kallonsa Lokaci Daya ta maida kanta kasa tare da dan Rankwafa Tana Fadin”Barka da Fitowa Sarakin Maimairtaban Kargi..!
Haka take Kiransa daman dan Murmusawa yayi kafin yace”Magajiya bana son Sarakin nan fa..Maimartaba Kadai ke iya Kirana na amsa..Sunana Sulaiman kuma don Allah ki Daina Ramkwafamin in zamu gaisa nan fa Gidana ne..Ba Fadar Sarkin na Kargi ba!
Ya karishe Fada Muryansa da alamun Zolaya ammh bai nuna saman Fuskarsa ba Kasa ta karayi da kanta kafin tace”Amin afuwa Ranka ya Dade..Bana iya kiran sunan mai garin Kargi gabadayane..Sunan yana Daraja da Kima awajena..!
Bai mata mgana ba illah kafada Daya Daga Daidai Lokacin da Samira ta Fito Daga Dakinta wani kallo yayi mata mai Cike da Tsana da gargadi Daya sata Zubewa tana mai barka da Fitowa kallo Daya yayi mata ya kauda kai Daidai sanda Magajiya ke Fadin”Saraki nan Zakaci abinci ko na Haura maka dashi saman Dakin ka ne..?
Kansa ya Girgiza yana Fadin”Am ok..Fura zan shan kafin na kwanta Ina yaran nan suke..!?
Magajiya tace”Mai sunan Hajiya tayi barci Tun dazu Datagama Rigima Hajiya ta mata wanka sai ta samu Barci..Mai sunan babban Mutum kuma yana Dakin nasu yana kallon yan aljanun nan nasu..!
Jim yayi yana kallonta batare da yayi mgana ba Har zai ce wani abu sai ya Fasa ya wuce ya Fara Taka Lallausan Cafet din kasar Italian Dake malale atsakar kayattacen Falon Dayaji kayan More Rayuwa.
Bayaso yayi mgana saboda yar aiken Hajiyarsu dole ya Fara Kafa Kafa da ita Domin bashi da ikon korarta faruwar hakan kamar ya siyan ma kansa Tikitin Fadan Hajiya ne da kuma Kudirinta akansa Da Fara Kokarin Tabbatar dashi.
Dakin su Wasim din daya zama Mallakinsu tun dawowarsu gidan,Wafiyya Dakin Magajiya take kwana Hatta Wasim din ma wani Lokacin sai dai shi ya fita Sakin jiki kuma baida Rigima ita ga ta yarinya sannan ga Kiyuwa da Rigima kala kala bata iya kwana batajita Lafe jikin Mutum ba
Koda ya shiga Dakin Wasim barci ya kwasheshi nan Tsakar Falon ga Talabijin nan a kunne ana Haska Cartoon din yara,gabansa kayan wasa ne su Ninja da superderman,da Bindogogi Daga gani dasu ya ke wasa kafin Barci ya Daukesa Tsausayinsa da Tsausayin Ya”yansa ya kamasa Allah Sarki Mutuwace mai Tonon asiri da ba domin Mutuwa ba da yanzu Wasim suna tare da Mahaifiyarsu tana basu kulawa shi kanshi da Rayuwarsa bata zama a Tagayyare ba
Ya kara Tattabar ma kansa Hasashen su Maimartaba akansa ba Daidai bane in suna Tunanin sun kakabamai auran Yayar matarsa saboda sun yi mai gata to wlh kara Gurgurta rayuwarsa sukayi,Domin shi dai bai ga amfanin hakan ba matar da bata wani da amfani acikin Gidan da Lokacin Datake nan da batanan duk Daya yaransa sun wuni Cikin Kadaici su kwana cikinsa Tana chan yawonta da sunan wai aikin asibitin gwannati aikin banza aikin Wofi Shidai Wlh an gama Kasheshi ba Tun yau ba ya Dade da Sanin ya Juyama Rayuwar jin Dadi baya Tun sadda Sunaira ta bar GidAn Duniya.
Cicciban Wasim dim yayi ya Rumgumesa yana kokarin kokuwa da Rauninsa Na Lokaci kafin ya maidasa kan gado,Kayan Jikinsa ya Ciremai ya isa ga karamin Durowansu ya Zaromai kayan barcinsa ya sakamai Barcinsa yayi nisa shiyasa bai Farka ba ya Dade yana Shafa kansa yana Tofamai addu”a ya Dade adakin kafin ya Fito sai da ya Ragemai Hasken Dakin ya karamai karfin A.C saboda garin akwai Zafi sosai Tunda yaga bai ga Wafiyya ba,Tana Dakin wanchan yarinyar mai girman kan tsiya alhalin shi kuma bai Tabataka Kafarsa zuwa Dakin ba Tun bayan Daya tashi ana Sunaira ya koma nata din Har Abada