MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Sulaimam bai samu kebewa da Sunaima ba sai bayan tafiyar su Baba Sani ya tafi kaisu gida Dagachan zai kai Samira gida shi kuma Sulaiman Saifullahi zai maidasa sun Fita Waje shi da magajiya su bama Baban Yaro Daman ganawa da matarsa.
Sai da ya Dauki yaron ya Kuramai ido yana kallonsa Allahu akbar wannan Rabon ne Silar Faruwar duk abunda ya Faru Ciki harda Rasuwar Sunaira Allah ya jikanta da gafara sai da ya share kwallah Jikinsa yayi sanyi ganin kamar yayi kaki.
Sunaima na Zaune an saka mata Filo abayanta ta kallesa Cikin Mirmishi kafin tace”Saraki..Ya haifi Saraki yau..!
Kallonta yayi kafin ya isa Gefen gadon ya Zauna dora mata yaron akan Cinyarta yana Fadin”Ya kika gansa.?me zaki ce ma Allah ayau Sunaima Daya bamu wannan kyautar..!
Kan yaron ta shafa Dake Cikin kayan Sanyi masu kyau da Tsada tace”Allah ya rayasa Cikin addinin Islama..Godiyata kuma ga Allah Daya azurtamu da wannwn kyautar..Sannan ina kara godemai Bisa Kaddaran data Ratso ni Cikin Rayuwarka Sannan ina Fatan Allah ya Haskaka kabarin yar”uwata ya Sadamu agidan Aljanna Firdausi..!
Sai kuka shima kamar yayi kukan ya Hadasu Dukkansu ya basu wani Rumguma mai karfi yana Fadin”Ameen Ameen..Allah ya raya SULAIMAN..MAimartaba yamai Lakabi da Sadauki sannan yace yana Miki Sannu da albishirin din Da kansa Zai zo yayi ma Takwaransa Huduba..!
Sunaima ta Dago kanta Cikin Hawaye tace”Au Saraki ya Haifi Sadauki zan ce..!
Yana Share mata kwallah yace”Acikin Satin da Sunaira zata bar Duniya Tayi Fatan ta samu Ciki ta Haifi me Sunana Sunaima..Ni kuma ban manta wannan Burin nata ba Shiyasa na Cika mata shi..!
Hannayensa ta Damke tana Fadin”ni kuma da mace na Haifa ni kadai araina nace zan Rokeka ka Sanya mata Suna SUNAIRA domin itace Silan Kaddaran data Hadamu waje Daya Saraki..!
Da Sauri yace”Insha Allahu Zaki Haifa mana Sunaira..Da izinin Lahi zamu Hada Sulaiman da Sunaira aduniyarmu Sunaima..!
Dukkansu Hawaye suke suka Rumgume juna Sulaiman na Fadin”Tanque Sunainma..Allah yayi miki albarka..!
Kamar kada ya barsu haka yakeji ammh Dole ya tafi gida Saifullahi nata Kira Sallama yayi mata Magajiya Zata kwana Dasu zuwa gobe
Tun da garin Allah ya waye Sunaima ke amsa wayoyin Mutane masu barka Hajiya da ya”yanta Kaf sun kirata har da Abba su Sadiya kuwa sun ce suna nqn tafe in suka Biyo Hajiya sai bayan Suna zasu koma.
Karfe 9:00am na Safe aka Sallamesu suka koma gida Sulaiman da kansa yazo ya Daukesu Suka koma Gida.
Suna komawa Gida ba Dadewa sai ga Inna Tani ta iso ita da Habiba Diyarta Gidan Inna suka fara Biyawa kafin su yada Zango Gidan Sunaima Tazo da kayan wanka ma masu jego kuma Daman Daga asibiti Sunaima Direct Sabon Shashenta Sulaiman yace ta Zauna.
Inna Tani tayi ma Sunaima wanka Ta gyara Jariri tas kamar ba ita ba Gida ya Kaure da Kamshin Masu jego da Turaran wuta tasaka akayi mata Ferfesun kan Rago ta tasata ta Cinye ga Kunu da Tea mai kauri Tana Fadin sha Haihuwa kikayi Sunaima na Tura baki Habiba na mata Dariya.
Sulaiman kuwa kamar Wannan ne Haihuwarsa na Farko yadda yake Rawan Jiki Inna bata zo ba ammh Ahmad ya kawo su Wasim sun zo haka suke Murna Wafiyya Harda Rigiman sai an goyamata Shi Sai da Inna Tani ta Lallasheta Saboda Darajan Haihuwa da kuma Hutun da yaran suka samu tace don Allah abar mata su Saraki yace ai shi yanzu komai tace ba Gaddama.
Habiba ba yanzu zata koma ba sai an yi Suna Sunaima na kwana Uku da Haihuwa sai ga Hajiya karama da Su Sadiya da Saddiqa da Safiya da Fatima dasu Radiya kaf dinsu harda su Sadiq sunxo barka da kayan Arziki akwatuna Biyu Cike da kayan sawa na Sunaima da na Jariri.
Haka suke Daukan yaron bakinsu yaki Rufuwa suna ta ma Sunaima Sannu da godiya sai dai tayi Mirmishi batacewa komai.
Basu kwana ba Aranar suka koma sai dai Sadiya da Saddiqa suna nan sai an yi suna Washegari sai ga Tawagan yan kargi su Hajiya uwa suma da kayan arziki sai wanda ya gani.
Suma basu kwanan ba sun yi barka suka koma Gida ya cika sosai Samira da magajiya ba zama suna ta Fama da Hidima.
Kwana Biyar da Haihuwa Hajiya tazo ita da Aminiyarta Hajiya Salame Allah Sarki,Amana batace haka ba Hajiya tace kafarta kafar kawarta ita ta kirata Tun jiya tazo Abujan yau suka Zo Barka suma Kayan arziki kamar Sunaima zata Bude shago in ji Tani Turman Atamfa uku Super wax hajiya Salame ta kawo mata da Kayan Bby harda 20k ta Dora mata abun sai wanda ya gani suma basu jima ba suka Wuce kargi Chan zasu kwana sai Gobe zasu koma.
Ana gobe suna Baki suka Cika Gida Khadijar Saifullahi tazo ita da Mama da tayi barka ita ta koma Jidda ta Fara Zama harda koyon Tafiya itama da nata kayan arzikin,Dangin Inna ma sunzo yan Zunti Sunaima ta rasa ina Zata kanta don Farimcikin ganin yadda aka Taru duk Saboda ita.
Ga kawayenta Yan wajen aikinsu Tare da ita su Aneesa da Fatima ga Matar Habib Salaha itama tazo.
Da yammah sai ga Maimartaba yazo da kansa Lalle wani Kaya sai Amale Sunaima tasha Lallunbi ta Sauko Falon kasa ta Zube gaban Maimartaba Sulaiman ya karbi Jaririn ya mika masa ya karba yayi mai Huduba bayan ya Bashi Dabino da Ruwan Zam zam ya mikama Sunaima yana Fadin”Allah ya raya Sulaiman Sadaukin kargi!
Gabadaya aka amsa da Ameen Fadawa nata Kirari maimartaba mai Dade ba ya fita bayan sun zo da Shanaye da Ragunan da Gobe za”a yankama Takwaransa Sunaina ta Zama yar gata ta ko”ina da Daddare sai ga Ahmad da Sakon Baba da Inna Kaya sukayi mata nagani na Fada ita da Sadauki Sunaima sai kuka Domin adaran Sulaiman ya Damkamata key din sabuwar Motarta 4matic baka Tana Haraban gidan sannan da Sakom Abba na 100k Cash da ban Hakuri yana nan zuwa ganin Mai Sunan Maimartaba.
Washegari aka tashi da Hidiman suna daman Tun jiya Matar Habib ta mata Kitso da kunshi Dayake ta iya Sosai mejego ta fito ras da ita Sai walwali Take Cikin kayanta ita da Jariri batasan asadin kyautan data samu da wannan Haihuwan ba sai godiya ga Allah kawai duk inda tabi kallonta kawai ake yi ana yabama wannan kyau da Zatin da tayi.
Anyaka Raguna Biyar Shanaye uku,Dole aka Dauko Hadimai Daga Fada su marliya saboda aikin nama da Abinci ga Matan Sani Direba dama Iyalan Auwal megadi suma sun zo sunan nan suna ta Taimakawa.
Anyi abinci kala kala sai wanda ka Zaba Nama ko har da gashi akayi ga Madara da Fura nan sai Badali akeyi Sulaiman kuma sun Shirya Walima a Kamfani suma an ci an sa”a an yanki Gashin nama da Fatan Allah ya Raya Sulaimam Sadauki.
Sai yamma suka zo Gidan akayi ta Hotuna da Baban,Sadauki da Uwar Sadauki sun sha kyau kamar ka Sacesu ka gudu abun sai wanda ya gani.
Kwana akayi ana ta Hidima sai Washegari sannan aka Fara Raguwa bakin Zuntu suka koma Da Kayan arziki sai wanda ya gani Haka ma yan Kargi suma Duk sun zo sunan Harda da Su Safiya dukkansu kannensa sun so sunan suma sai Washegari suka koma da Naman sunan da aka bama kowa,Kawayen ma su Aneesa suma sun tafi da irin Arzikin da Sunaima ta Samu,Khadija dai sai ta takara kwana Tatafi ita da Matar Habib sunaima ta Gode musu sosai ta kuma saka aranta Sune kawayenta Daga yanzu.
Habiba ma aranar ta koma Zuntu da kayan arziki aka bar Inna Tani Tana kara kula da mejego.
Gida ya Rage Daga mejego sai ya”yanta sai su Magajiya da Samira sai Sadiya da Saddiq sunce sai sun koma makaranta zasu tafi.
Dole Sulaiman ya bar musu Shashen Sunaima shi kuma yana Shashensa sai dai su Sadiya su kai mai Sadauki ya gansa in ya Dawo.
Haka suka Cigaba da Jegonsu Inna Tani na kansu tana Kulasu koda wani Lokaci Hajiya na kira tana jin Lafiyarsu,Sannan Abba ma yazo yayi barka yaga Sadauki Hajiya ta dawo ita da Hajiya karama.
Inna dai batazo ba sai da Sunaima tayi arba”in ta kai mata Sadauki da kanta Zuntu kuwa su suka maida Inna Tani gida da abun arziki kamar zata Bude shago har sai da tayi hawaye Godiya kuwa kamar bakinta zai Cire haka ta Dinga yi musu.
Su Sadiya sun koma Gida Shiyasa bayan sun dawo daga Zuntu ta tafi Abuja wajen Sati Daya tayi Duk da Saraki yaso ya hana tacemai yayi Hakuri Ta zaga Duka Gidajen Kannensa sai da taje ita da yaran su Wasim.
Bayan ta dawo Kargi taje ta kara kaima Maimartaba Saraki dasu Fulani kwana Uku tayi ta dawo bayan taje ta gaidasu su Hajiya uwa nan suka Hadu da Hajja Bilki tazo suka gaisa taga Sadauki.
Taje Karaye Wajen Khadija ta kwana Daya itama suna ta Shirin Dawowa nan kaduna Mama ta amince,Sannan taje tayima Salahar Habib Wuni da ita dasu Aneensa da Fatima Domin sun mata Hallaci Sosai bazata yada su ba
Sai da tagama yawon Dangin da Gaisuwan ban gajiya kana ta Samu Zama agida su Wasim sun koma Gidan Inna Daga ita sai Sadauki sai su Magajiya bata da mtsalan Reno Matar Sani sun dawo Nan tare dasu matar mai Kirki Karime ita ke Shigowa tana Tayata Kula da Sadauki.
Inna Tani bata koma Zuntu ba sai da ta gyara Yarta sosai kana ta koma Ranar da suka Hade da Saraki Kamar
Ya Haukace mata tasha Sambatu da Surutu kamar me sai da tagaji ta Danne mai Baki sannan yayi Shuru.
Wata Biyu da Haihuwarta ta koma aikinta,ba ason ran Sulaiman ba sai da Hajiya ta Saka baki ya barta ta koma in tana da aikin kwana Kamar kada ya barta Haka yakeji wai Zata kwaso ma Sadauki sanyi da Cizon Sauro ita dai nata Shuru bazatayi mgana ba yace ta bar aikin gabadaya..Duk da babu abunda ta rasa ammh aikinta na Fannin lafiya ne ba Domin Dukiya ko wani abu ba Saboda Taimakom mata ne.



