MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

MURFI…
Bayan Shekaru uku..
Bayan shudewar Shekaru uku abubuwa Dadama sun Faru na Samu dana rashi,Na rashin Shine Rasuwar Fulani hakika an yi rashi Sosai,Sannan an samu Cigaba sosai ta Fanni Rayuwa da arziki Sunaima ta kara Haihuwan Mace taci sunan Sunaira suna Kiranta Bibi sai kuma yanzu Datake Dauke da Wani Cikin dan wata Biyar ajikinta..
Arzikin Sulaiman ya kara Hauhawa Kamfaninsa na Madara ya Zarce sa”a da Tsara yakai Inna da Baba Hajji Domin yace har abada bazai iya Biyansu ba,Sannan yaje shi da Sunaima da yaran kafin ta Haifi Bibi Sunje har Kasheshen Duniya irin su India,America,China Da Sauransu a wani Karshen Shekara da sunaima ta Samu Hutun Annual leave.
Sannan yakai iyayansa Abba da Hajiya da Hajiya karama Maimartaba dai Tsufa ya zo sai Fatan gamawa da Duniya Lafiya ya Nada Saraki Saurata Wato Sarakin Kargin gabadaya Sannan yana kokarin yin Murabus ya Dora Daya cikin ya”yansa Tunda shi dai yanzu an kwana Biyi aduniya.
Sunaima ta siya ma su Inna Sabon Gida da kudin aikinta ta kuma kai Ahmad Makarantar Sojoji,Har zuwa Lokacin su Wasim suna wajen Inna Sai dai Hutu ke Kawo su gidansu.
Ayanzu da Wasim keda Shekaru goma sha Daya aduniya yana Primary 6 sai Wafiyya Dake da Shekaru Takwas tana Primary2 Sadauki ma an sakashi a makaranta yana Nursry 1 shi.
Khadijan Saifullahi sun dawo nan anguwan Mu”azu da Saifullahi ya mallaki gida suna kwancensu su uku gwanin sha”awa da Matar Habib Salaha.
Kannen Sulaiman sunyi aure Sadiya da Saddiq rana Daya Sadiya tana nan kaduna Saddiq ne tayi aure anan Abuja Sadiq ya gama makaranta yana Service Kamfanin A.S kargi ya kai wani matakin Kololuwa Riba kan Riban da Abba bai Taba Tsammani ba Har Taron karramawa ya shirya musu Shi da Saifullahi abun sai wanda ya gani Da kyauttukan kudade Makudai da Gidaje da Motocin hawa Cikin su ba wacce bata Hawa Mota mai Tsada Sunaima ta iya Driving ita take Tuka kanta zuwa wajen aiki ko zata Fita ko kai yara makaranta bata da mtsalan komai agida su magajiya na taimakawa Duk da Ita ke shiga tayi ma Saraki girki da kanta.
Sannan ga karime matar sani na Taimaka mata da Dawainiyar yaran sai abubuwa suka Ragun mata.
Sulaiman ya gaji da korafin aiki ya Daina mgana Domin yaga aikin Taimako ne shiyasa ya kyaleta Tanayi ba Domin ta rasa komai Tunda Duk wani jin Dadi sai dai Ta samma wani Cikin jin Dadinta.
Laila ta sake aure da wani Abokin Babanta A lagos yake matansa uku itace ta Hudu chan Lagos din take da Zama Amarya Hajiya Salame ta Haihuwa,yan Biyu na Farko Hassan da Hussaini suna nan Dole ta Zauna tayi Hakuri daman ance in bakayi Sharan masallaci ba kayi na kasuwa.
Hajiya Zabba”u bata Ja baya da Salaha ba suna aminci sosai sai dai wani abu ne da Hajiya take kiyeyewa yima Allah Shishshigi.
Sunaima ta zama Tauraruwa wajen Mijinta da yan”uwansa Hajiya ko ya”yanta yanzu ta Daina Shawara dasu sai da Sunaima Domin itace komai ayanzu agidan haka Hajiya karama ta Dauketa Abba ma kamar Sulaimam haka suka Dauketa Kullun inna Hamdala suke yi da ita Baba suna kara Godema Allah Daya Daidaita Duka al”muran.
9:00am
Jiya jumma”a aikin Dare tayi Shiyasa yau da Safe tana Dawowa gidan ta Ke adaki tana Barci Rufe Bedroom dinta tayi bataso Biba ko Sadauki wani yazo ya Dameta ta gaji ga aiki ga Nauyin Jiki Dakyar ta iya bari tayi wanka ko kaya bata saka ba Daga ita sai Towel ta Fada kan gado tana Barci.
Sulaiman yana Shashensa Shima yana Hutun karshen mako,baima san Sunaima ta shigo gidan ba sai da su Sadauki suka zo suna Rigimansu shi da Bibi ya taso daga Cikin Daki Sanye da Jallabiya Sadauki ya kara Kiba da Fari kamar bashi ba Jikinsa Likwai likwai alamun yana samun Hutu da jin Dadi.
Biba ya Dauka ya saba yana kama Hannun Sadauki suka fito Falo yana Fadin”Ina Anty Sadauki..?
Haka su wasin ke kiranta ya kama bakin kowa har su Sadauki sun kama kowa anty.
Sadauki da muryansa ta yara yace”Cha kulle kofa Daddy..muna kiranta bata jo ba..!
Sulaiman yayi Dariya bai ce komai ba ammh aransa yana so yayi mganin Sunaima tasan fa Jiya haka tata fi ta barshi Shikadai ammh tana Dawowa taje ta kwanta ko ta nemesa.
Kasa suka Sauka shi da yaran Samira Dake gyaran Falon ta Duka ta gaisheshi ya amsa yana Fadin”Samira yaran nan sun yi breakfast kuwa..!?
Kanta na kasa tace”Tun Safe suka sha Tea ranka ya Dade..Kuma yanzu suka gama cin Dambun naman da Anty tayi Shekaran jiya..!
Biba na ganin Samira ta Fara Zillo ya Saketa ta isa gareta tana Nuna mata baya Samira na Dariya tace”Bambu ko Biba..?
Kai ta gyada mata itama kuma ta Dauketa ta goya Sulaiman na kallonsu Cikin Shagwaba da Rigima Sadauki yace”Daddy ni ma Bambu..!
Sulaiman yace”To Sadauki ai bayan ta Daya kuma ta goya Biba..kana gani Anty kuma kasan bazata iya goyo ba yanzu sai dai in ni kake so na goyaka..?
Da Sauri yace”Eh Daddy..!
Sulaiman ya batarai kafin yace”Sadauki ka zama Lukuti zaka karyama Daddy baya..!
Yadda yafada yasa Dole ya Kyalkyale Da Dariya sai ga Magajiya ta Fito suka gaisa da Sulaiman tana Fadin”Taho na Giyaka Sadaukin kyale Samira muma ai muma da baya..!
Da gudu ya Nufeta yana Fadin”Mama..bumbun..
Daman haka Sunaima tace su rika Kiran Magajiya bayan ta ya Dane yana Dagama Sulaiman hannu ya Dagamai yana Fadin”Bayan Daddy ya Huta..!
Sulaiman ya kalli Samira yana Fadin”Sani ya same da mganar kun Daidaita da gaske ne..?nasan Sani da Shiririta nake sai naji ta bakin ki..?
Kai ta sunkuyar cikin jin kunya ta kasa mgana Magajiya tace”Ai soyayyar bata yanzu bane yallabai ta Dade..!
Sulaiman yace”Shikenan zan yi mgana da Maimartaba..In sun Daidaita kansu ni zan zame musu uba Sunaima uwa ayi komai agama Tunda Daga Sanin Har Samira Duka suna Cikin Ahalina ne..!
Nan da nan magajiya ta Fara godiya Itama Samira nan ya barsu da yaran ya Koma sama Direct Dakin Sunaima ya shiga yaji Bedroom din a kulle Dakinsa ya koma ya Binciko key yazo ya Bude kwance ya ganta da Towel Mirmishin mugunta yayi yana Fadin “Yes Saraki mai Sa”a..!
Jallabiyansa ya Cire Dagashi sai karamin wando ya Haye gadon ya Zare Towel din ya Jawota Jikinsa ya Rungume da karfi Cikin magagin barci taji an riketa tace”Waye..?
Da Sauri yace’MIJIN KANWARKI NE..!
Cikin rada ya fada yasa tana jin muryansa ta Bude ido sai akan Gwarzonta Saraki Baban Sadauki da Biba.
Mirmishi ta saki kafin tace”Kace MIJIN KANWATA…Kaddarata..!
Matseta yayi yana Fadin”Uhmm
Kimsan ni kaddaran ki ne kika barni Jiya Baki Bude yauma haka ko..?
Tana gyara kwanciya kan jikinsa tace”na gaji ne Saraki..!
Yana Shafa Cikinta yace”Ni na gajiyar dake..?malama bana son wannan mugutar taki gwalemin kayana na Shige..!
Kirjinsa ta Daka tana Fadi”innalillhi Saraki..Saraki..!
Yana Dariya yake fadin”Yo karya nayi..?ba gwalemin kike yi ba Hajiyata..?
Bakinsa ta rufe da nata suka Tallafi juna na wani Lokaci kafin ta Sakeshi Tana Fadin”Wannan bakin naka sai na Konasa da wuta kafin yayi Linzami..!
Tafada tana jan bakin Dariya yayi yana Tura mata bakin yana Fadin”Nidai kafin ki koma shi da Wuta Fara konashi da bakin ki..Bayan kin gwal..!
Bata bari ya karisa ba ta Dinga Dukan Kirjinsa tana Fadin”Saraki Saraki..!
Dariya yake yi yana kare kansa Lokaci Daya yana Fadin”Sunaima..Sunaima..Gwaleee min….!
Tammata Bihamdillahi…godiyata ta tabbata ga Allah Subuhanahu wata”ala Daya bani ikon Fara Rubutu Labarin nan cikin ikonsa gashi yau ma acikin ikonsa na kamallah Godiyata ta tabbata ga Annabinmu muhammad sallallahu alaihi wasallam tare da iyalansa da Sahabansa gabadaya