NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina zama wayar mamanmu tai kara, tashi nai da sauri na dauka ina shigewa daki ko lura da mamanmu dake zaune tana kallona banba(nace soyayya dadi????♀️????)

Zama nai gefen katifa ina dagawa.

Cikin shagwaba nai Sallama.

Amsa min yai yana cewa afuwa Gimbiya ban kiraki ba tun dazu koh kiyi hakurj aiki ne ya rike ni wallahi naje gidan gona zan fitar da kwai.

Cikin shagwaba nace amma Habibi fa kai kace ina dawowa zaka kirani.

Sorry Gimbiya kimin afuwa kina raina bazan ita daukar waya a lokacin bane.

Turo baki nai kawai ina kunkuni.

Murmushi yai yace ni kike turo ma baki koh bkm yarinya lokacin kine wannan bakin zaiyi bayani ne.

Hannu nasa na rufe fuskata nace nidai ba ruwana Habibi.

Haka muka sha hirar mu yace gobe insha Allah zai shigo sbd jibi zaiyi tafia.

Cike da kewar sa data fara kamani tun kan yai tafiyar nace Allah ya kawo min kai lafia kuma kaika lafia habibina.

Ameen Gimbiya ta kuma sarauniyar zuciyata.

Murmushi nai ina kashe wayar na rungume ta a kirji na ina jin wanj sabon sonsa yna kamani.


Khalifa kar ka kuma mun wannan zancen bana son ji ya fada cikin fada da karaji.

Amma Noor kayi hakuri mana don Allah iya….

Katse sa yai cikin tsawa data fi ta farko yace nace ma na tsane sa bana ko san jin sunan sa…….

Comments and share plz

Mrs A.M

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by
        Mrs A.M

Page 9

Dedicated to Daughter????(Fiddausi)????

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 A hankali khalifa ya dafa sa, cikin kwantar da murya yace kayi hakuri Noor komai mai wucewa ne abinda nake so ka gane shine ka masa uzuri ba lallai ma yana cikin hayyacin saba.

Dago idonsa yai da sukai jajir ya zuba ma Khalifa, kada kansa kawai yai yana janyo pure watern da ke gefensa ya fasa yana sha.

Hmm, kawai khalifa ya iya cewa yana kara jin tsoron Allah na kara ratsashi.

Ranar a gidan ya kwana a dakin Noor.
Da sassafe tun bakwai Noor ya mike ya shiga bandakin dake tsakar gidan, wanka yai ya fito daure da towel a kugunsa dayan kuma ya sakala shi a wuyansa yana goge dogon gashin sa.

Lokacin da ya shiga dakin a zaune ya samu Khalifa yana danna katuwar wayar sa, ganin shigowar sane yasa ya ajiye wayar yana kallonsa.

Shikansa yasan Allah yayi halitta a gurin kuma tun tuni ma ya fara tausayin matar da Noor din zai aura????

Tsaki yai ganin kallon da yake masa ya juya yana kallonsa, hade rai yai yace fita min a daki tunda ka zama dan iska????

Hangame baki Khalifa yai yana jin ikon Allah cikin danne dariyar dake son fito masa yace ynxu maza nine dan iskan.

Harara ya watsa masa yace inba dan iska ba meye zaka tsaya kana kare ma halitta ta kallo.

Hmm kwantar da hankalin ka ni meye nawa dazan tsaya kallon ka kawai ina tausayin matar da zaka aura ne wallahi maza don nasan ubanta kawai zata ci.

Wani shegen murmushi yai na gefen baki, Subhanallah tsarki ya tabbata ga Ubangijin dayai wannan halittar, wasu irin dimples ne dashi na dukkan gefen kumatun sa suka lotsa sosai gashi fararen hakoransa da suka bayyana abin saidai san barka.

Tabbas shidin mai tsada ne shiyasa ko murmushin sa ya kasance ba kowane yake iya gani ba.

Juyowa yai yana kallon khalifa bayan ya sa riga da wando bakake ya kuma rufe kansa da wata huta kamar ta sanyi sai kamshi yake.

Kai nifa shiyasa kaga baxan auri yarinya ba, yar shekara 27 zuwa 30 zan aura don in na auri yarinya kashe ta kawai zanyi ni nasani.

Dariya khalifa yai yace amma kai dan iska ne wallahi wato kashe musu ya zakai.

Dage girar sa yai yace yessss, jakar aikin sa ya dauka ya goya wacce kayan sa dayake sawa a gun aiki suke ciki da yan abubuwan da zan bukata na amfani.

Fitowa sukai bayan ya rufe gidan, har zai hau machine dinsa sai kuma ya kalli gidan dake makwabtaka da nasa, shima dai gidane dan daidai kuma na talaka mai rufin asiri.

Kofar gidan ya nufa yana dan kwankwasa kofar duk da kofar a bude take.

Bude kofar akai inda wani saurayi ya fito ganin Noor yasa sa sakin fuska sosai ya mika masa hannu yana cewa ina kwana Yaya Noor.

Amsa wa yai yana dan matsawa ganin saurayin na kokarin mikama Khalifa hannu shima.

Gaisawa sukai kafin ya kalle sa yace salim inna ta tashi.

Eh Yy Noor ta tashi ai tun dazu kamar kasan kuwa dazu ta gama maganar ka tace kwana biyu ka daina lekowa ma.

Murmushi yai yace muje mu gaisa sauri nake yi.

Cikin gidan suka nufa, innar na ganin su ta mike da sauri tana fadin lalle marhaban dan gidan Inna ashe kana tafe dannan ai da har nayi fushi nace toh na dena auren dakai tunda baka zuwa kana ganin na.

Murmushi yai yana zama a kan tabarmar da Salim ya shinfida musu.

Gaishe ta sukai ta amsa cikin sakin fuska tana kwalawa jikar ta kira kanwar salim.

Da sauri Binta ta fito tana gyara hijab dinta tace gani inna, bakiga yayanki bane da baxa ki gaishe su be iyee nifa bana son fitsara da rashin kunya ayi yarinya sai uban nuku nuku toh da baki gaishe suba me zai rageki dashi ko ya kara miki.

Murguda baki tai tana dan matsawa daga kusa da innar tace wallahi inna ki rage masifa haba da farar safiya ma sai kin cika ma mutane kunne da masifar ki.

Ubanki Yusufa kike rashin kunya bani ba, banza kawai ke dalla matsa ni ko na mangare ki agun aba uwa tsinke.

Hade rai tai tana juya wa gunsu Noor, gaishe su tai wanda khalifa ne kawai ya amsa yana tambayar ta school.

Mikewa tai don kawo musu kofin da zasu sha kunu ganin inna ta kawo masu jug din kunu da kuma plate dake dauke da kosai.

Da kanta ta zuba musus ta tura musu gabansu, ganin ba wanda yasha yasa ta mike tana kada zanin ta ta lalubo lalitar ta dake jikin rigar ta ta ballo goro ta bantara, karkace kai tai tana tabe baki tace toh tunda baxa ku sha kunun ba ku tashi ku fita.

Da sauri khalifa yace zamu sha inna ya fada yana daukar cup din yana kurba, shina gogon dauka yai yana sha a hankali tuni suka tashi da kunun da kosai, inna kuwa ta sasu a gaba sai zance take musu.

Hmmm kana jina mai baban suna(tana nufin Noor) ai ina fada maka kakan su Salimu ba karamin dage wa yai kafin ya nemo soyayya ta ba, nifa da ina budurwa sai kaga samari fin ishirin suna layi a kofar gidanmu in naje na tsaya da wannan naga bai min ba ko yana tsami sai na tsalle sa naje ga na gaban.

Kedai Inna kiji tsoron Allah samarin har ishirin ne ke layi a gidanku.

Yo don ubanki karya zan muku ko me toh har dan dagacin kauyen mu shima ya kaunaceni kamar zai mutu don ki san irin kyaun da nake da shi.

Dariya khalifa yake kawai don daga ganin tsohuwar tana da abin dariya ga masifa kuma.

Bayan sun gama sallama sukai musu inda NOOR ya ciro dubu biyu a aljihunsa ya mika ma inna yace gashi inna ku kara ana cefene.

Anya ayi haka kuwa dannan gaskia rike abinka kawai bana karbar maka kudiba.

Bin ta da kallo binta tai kawai ganin tasa hannu ta karba amma kuma sai cewa take baxa ai hakaba ya karbi kayansa.

Girgiza kai yai kawai yana murmushi suka fito daga gidan, a kofar gidan sukai sallama da khalifa shi kuma ya nufi gun aikinsa.


Cikin nutsuwa nake shiryawa ina sanye da doguwar rigar material anmin dinki mai sauki da arha ne amma kayan sun min kyau don sun kamani hakan ya fito da kirata tubarkallah.

Hoda na murza da jan baki sannan na janyo hijab dina kalar toka na sa, turaren da Mahmud ya kawo min wancen satin na fesa ina lumshe ido don kanshin sa yamin Allah yayi ni dason kanshi yanayin gidan mune yasa bana siya amma duk da haka ina zuwa shagon masu turare in basu dari biyu zuwa dari hudu su zubamin dan duri.

Wayar mamanmu dake hannu na ce tayi kara, kallon wayar nai inda sunan Yy Mahmud ya bayyana, murmushi nai ina dagawa cike da yanga

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button