NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

A wannan lokacin Aunty ta sani nai wanka na shirya cikin shadda blue colour doguwar riga dinkin yai min kyau sosai, Sumy tai min kwalliya na yafa mayafi na a kai iya kyau kam nayi tubarkallah.


A masallaci kuwa bayan su malam sun iso yaje ya samu limamin masallacin sukai magana.

Kafin a fara daurin auren limamin masallacin yai shelar duk meso da kwai sadaka na mata, nan fa mutane suka fara cried kuce.

Wasu mutane ne manya da saurayi tare dasu suka samu liman da maganar auren da yai shela inda ya hadasu da malam Abubakar.

Gefe suka matsa inda dukkansu suka muka ma Baba hannu sukai musabaha.

Daya daga cikin sune yace “Malam meyasa kake son ka bada sadakar auren yarka.”

Cike da damuwa baba ya fada musu a takaice abinda ke faruwa.

Cike da tausaya wa dayan yace “in ba damuwa ina nemawa dana auren yarka.”

Da sauri baba ya rike masa hannu yace “na baka was muje a daua kawai ya fada cike da farin ciki.”

Gaba yai cikin masallacin ya fadawa limamin yanda sukai.

Daga gurin su mutumin kuwa wanda ya ce zai aura ma dansa maryo ne ya kalli dan saurayin yace “muje kayi video a wayar ka ana daurawa sbd ya zama shaida.”

Dayan ne yace “amma yaya taya zakai wannan danyan hukuncin kawai baka san yarinyar ba da halin ta kace zaka aura masa ita.”

Daga masa hannu yai yace “kayi min shiru muje kawai.”

Bayan an daura auren Walida da angonta musa sannan shelar daurin auren maryo ya karade.

Da sauri Baba yahuza ya mike jin ana cewa AN DAURA AUREN MARYAM ABUBAKAR YAKUBU DA…………

COMMENTS ND SHARE PLZ

MRS A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
        Mrs A.M 

Page 16

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

   AN DAURA AUREN MARYAM ABUBAKAR YAKUBU DA MUHAMMAD NOOR MUHAMMAD AKAN SADAKI DUBU ISHIRIN LAKADAN BA AJALAN BA.

Wani sassanyar ajiyar zuciya baba yai ji yake kamar an cire masa wani dutse kato a kansa, nan fa suka fito ana taya juna murna.

Sirikin Maryo(????) ne ya jawo dan saurayin da suke tare yace “khalifa wannan videon kaje ka nuna ma Noor yasan an daura masa aure kuma a matsayina na ubansa ku zama sheda inhar ya sake ta sai na tsine masa yana sakinta zan tsine masa kawai, sannan sati daya na basa amaryar sa taje ta tare.”

Yana gama fadin haka ya juya gun baba ya mika masa hannu sannan yace “wannan kanin mijin ita maryam dinne kayi masa kwatancen gidan ka sbd sai raka angon yaje yaga amaryar sannan don Allah bana so ta wuce sati bata tare.”

Da sauri baba yace “an gama ko yau kace kana son ta tare zata tare ai shikenan na gode sosai.”

Wuce wa yai kawai sannan baba yazo gun su khalifa ya kara mika musu hannu sukai musabaha yace su biyo sa suje suga gidan.

Har kofar gida suka isa sannan ya fito yai musu Sallama ya shige gidan gaban sa na faduwa.

Umma na ganin shigowar sa tai saurin mikewa ta bi bayansa ganin ya nufi dakin Mamanmu.

A cike dakin mamanmu yake ina zaune a jikin inna sai kara min nasiha manyan suke ni kam lumshe idanuna nai kawai don ban da kwarin jikin budesu ma sbd yadda gabana yake dokawa da karfi.

Shigowa yai ko sallama babu idonsa ya sauke a akaina hakan yasa sa karasowa gun inna, hannu yasa ya dagani sannan ya riko hannuna yasa min kudi a ciki.

“Wannan sadakin kine Maryam yau na daura miki aure amma bada mahmud ba.”

Da sauri na bude idanuna ina kallonsa gaba na na tsananta bugawa tabbas da ace bai rikeni ba ba abinda zai hanani zubewa a kasa.

Muryar mamanmu naji tana cewa “kamar ya malam wacce irin magana kake fada haka.”

Kallon inna yai sannan yace “jiya da daddare kawun Mahmud yazo…….. kwashe komai yai ya fada musu ya dora da fadin ni kuma ganin suna son kunya ta ni yasa na bada sadakar ta a masallaci amma Allah cikin ikonsa sai wani ya nemawa dansa aure kuma na basa an daura Alhamdulillah don haka a matsayina na mahaifin ki na yanke shawarar nan da sati daya zaki tare gidan mijinki insha Allah.”

Dagowa nai ina kallon sa kawai tunda nake da baba ban taba sanin cewa baya kaunata ba sai yau.

A hankali nace “baba kai ne mahaifina kuwa….”

Jinai an yarfamin wani marin da ya dauke min ji da gani na, juyawa nai ina kallon mamanmu dake tsaye a kaina tana huci.

“Mamanmu ko bakiji abinda yace ba sadaka ya bayar dani a masallaci wani uba ne zai ma yar sa haka mamanmu.”

Tsawa ta daka min tace “wuce daki mara kunyar banza mara kunyar wofi ko mahaukaci ya aura miki baxa ki gode masa ba.”

Juyawa nai na kalli mamanmu sannan na kara kallan baba kawai na fita daga dakin.

Inna ce ta kama baba da fada ta inda take shiga bata nn take fita ganin kamar baya jine ma yasa ta ce masa ya fita ya bata guri.

Komawa tai gun mamanmu dake kuka sosai su Hajjo da Gwaggwo Zainab na rarrashin ta.

Zama tai gefen ta ta rike mata hannu tace “kiyi hakuri Hadiza ko wani bawa da tasa kaddarar insha Allah kuma takwara ta baza ta wulakanta ba jikina na ban insha Allah auren nn sai ya zama abin alfaharin mu gaba daya.”

Nan aka taru ana bawa mamanmu baki har tai shiru sai kuma tunanin marin da tai min ya tsaya mata a rai.

Ni kuwa direct gidan su Sumy na nufa, ina zuwa nan ma na tarar dasu cike da tashin hankali sbd baban sumy ya fadawa Aunty ita kuma ta fadawa sumy.

Ina shigowa sumy ta fada jikina ta fashe da kuka, shafa bayanta nake alamun rarrashi kawai ina murmushi.

Ji nake dama nice ita data iya kukan ni nakasa yin sa ma sai wani abu da ya tsaya min a wuya na yaki wucewa.

Aunty ce tazo ta janye sumy daga jikina ta janyo hannuna muka shiga dakinta.

Xaunar da ni tai a gefen gadon itama ta zauna.

Cikin nutsuwa da iya sarrafa kalamai tace “kiyi hakuri Maryo komai mai wuce wa ne insha Allah wannan auren sai kinyi farin ciki a cikin sa ki rarrashi zuciyar ki ki kwantar da hankalin ki kuma, shikuma Mahmud din Allah ya saka miki abinda yai miki don baxa mu yafe ba wallahi.”

Nidai ban magana ba har ta gama ta fita, kwanciya nai ina tunanin soyayyar mu ashe duk karya yake kawai yaudara ta yazo yayi.

Tunanin yai aure ne yasa naji wani kuka mai karfi yazo min, ban hanasa zuwa ba na sake sa……..


Dauke idanun sa daga kan wayar khalifa yai ya mai da sa kan Daddyn khalifa.

Cikin lallashi dady yace “ka kara hakuri akan wanda kake Noor mai hakuri yana tare da nasara insha Allah don Allah kar ka wulakanta yarinyar nn duk da ban santa ba ban taba ganin taba amma ta kwanta min a rai insha Allah alkhairi ne shigowar ta rayuwar mu.”

Shidai bai ce komai ba har dady ya gama masa maganar da zaiyi sannan ya dora da fadin “a matsayina na mahaifin ka kuma zan turo masu gyara su gyara ma gidan ayi fenti duk Inda yake bukatar gyara ayi sa kafin nn da sati dayan.”

Da sauri yace “dady ka barsa kawai ba zan iya komai ma ina da wasu kudade dana ke tarawa.”

“Rufemin baki kai mesaya ka cika taurine kaine ni fa nace zan ma ba wani ba, wuce ma in ga gidan da kaina in duba ko ina.”

Mikewa yai badon ransa ya so ba suka shiga gidan sai da dady ya gama duba komai sannan ya kalli Khalifa yace “kofofin gidan za’a chanja su gaba dayan su sannan asa sababin bulbs sai kuma fankoki don naga a dakin kane kawai da fanka ita waccen gurin sai ya zama nata daki da palour ne amma dakin yayi karami bana tunanin in sun siyi gado zai shiga ciki.”

Shidai Noor bai ce komai ba in banda kara hade rai da yai.

Cigaba da cewa dady yai “sannan ban daki daya ne a gidan kana ganin ba komai Noor?”

Daga masa kai kawai yai yana juya fuskar sa.

Murmushi dady yai yace “kitchen dinma duk sai an rushe an gyara sa ayi sabon cabinet don wannan sun lalace, sannan a sa muku solar wannan sune umarnina Noor ko baxa ka iya ba ne?.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button