NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsaiii dada tai tana kallon saudat sannan ta juya ta kalli Ammi kawai ta fashe da kuka tace Allah sarki dan albarka na????

Hakan data fada yasa daga Ammin har su saudat jikinsu yin sanyi kawai sai suka fashe da kuka suma, shiru Ammi tai tana share hawayen da ke zubo mata itama…….


A kwana a tashi ba wuya wajen Allah gashi ynxu muna rubuta waec inda bikinmu ya rage saura wata daya.

Ta ko ina gyara ni Aunty take dukda ina da kwarewa gun girki da tsafta amma haka Aunty kullum sai ta kara min darasi akan tsafta da yadda zan mallake mai gidana.

Nida sumy take wa nasihar tunda itama sumy an kawo kudin ta saidai basusa lokaci ba.

Har wannan lokacin Aunty bata daina ban maganin sanyi saidai ta hada min da kayan fruits ynxu kullum sai ta kirani ta sa musa da muhd sun siyo mata kankana ta dari in zauna a gaban ta in sha, tun ina jin haushi kasancewar kankana bata dame ni ba har na saba ko bata aika bama ni ina aikawa a siyo min.

A bangaren siyyaya kuwa Mamanmu ta fito da ajiyar ta sbd gonar ta wacce ta kasance gadon tane ta siyar aka bata dubu 120 kasancewar gonar ba wata babba bace.

A cikin kudin ta ware dubu 50 ta bawa Aunty ta siyo kayan kitchen sauran dubu 70 din ma Aunty ta bawa ta ajiye in yaso in bikin ya matso aka je aka ga gida sai ahada da kudin zancena a siyo gado.

Sam bata sa baba a lissafi sbd komai ya samu Walida kawai yake siyawa kamar ba yarsa bace ni.

Da mamanmu ma tai masa magana dubu 20 ya bata yace gashi nn taje ta siyo min komai shi bashi da kudi.

A kudin da mamanmu ta bawa Aunty itama ta hada da nata muka je kasuwa ni da ita da sumy muka siyo kayan kitchen.

Mun siyo O-gas dan madaidici sai set din flask guda biyu da flask din tea guda daya babba, su spoons, fork, knife duk mun siya masu 12.
Sannan muka siyo plates guda 12 masu kyau da cups 6 sai abinsa spices da nagani yai min kyau na dauka.

Haka muka siyo kayan mu ganin sha’awa daidai talaka, a gidan Aunty duk ake ajiye wa.

Gashi wani turare da Aunty ta ke min na yan maiduguri har ya kama jikina ko taya na gifta ka saika ji wani sanyayyen kanshi yana tashi.

Nidai duk wannan Abun da ake dauriya nake kawai amma ina cikin tashin hankali gaba daya mahmud ya canja min tunda ya dawo daga tafiyar da yai ya chanja sai tai sati biyu bai zo gidan muba waya kuwa baifi ya kirani sau daya ba a rana abinda da sai ya kira yafi sau goma.

Sai dai in naga abin zai dameni ni na kirasa amma ina kiransa ma baya wani bani hankalin sa zai fara cemin yana da aiki ko kuma customers sun shigo.

Duk nabi na kara ramewa sai hanci da ido, duk wanda ya ganni yasan na rame amma ba wanda ya kawo ko wani damuwa ce ke damuna kowa dauka yake fargabar aure ne.

Hatta sumy tai tai na fada mata abinda ke damuna ansa daya ce bkm tun tana magiya har ta zuba min ido kawai.

Itakam mamanmu dama bata ma bata bakin taba duk da tasan sarai ba fargabar aure ce ba.

A haka muka gama zana jarabar mu ta waec wanda ya rage saura sati biyu a daura mana aure……


Zaune yake a kan katifar sa yana irga kudin da yai yau, dubu 17 yai don ba karamin aiki yasha ba tun da ya fita da asuba sai bayan isha’i ya dawo gida gaba daya ya gaji.

A hankali ya mike ya bude karamin fridge dinsa dake dakin, pure water ya dakko guda biyu ya ajiye a gefen katifar sannan ya janyo ledar abincin daya siyo.

A hankali ya fara cin tuwon shinkafar miyar Alayyahu da gyada yana ci yana duba wayar sa sbd da kwai inda yake son zuwa gobe Insha Allah gashi kuma sunyi da khalifa tare zasu je amma har ynxu khalifan bai kirasa ba.

Yana gama cin abincin wayar sa ta dau ruri, sai da ya bari ta kusa tsinkewa sannan ya dauka……

More comments more typing

Comments nd share plz

Mrs A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
       Mrs A.M 

Dedicated to Noor fans club???????? ina jin dadin comments dinku Allah ya bar zumunci????

Page 14

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Kara wayar yai a kunnen sa yai shiru ya ki magana.

Daga dayan bangaren khalifa yace “sorry maza wallahi traffic ne ya rike ni kasan a mota na zo fah.”

Dan tabe karamin bakinsa yai yace “na dauka ka fasa zuwa ne ai.”

“Ni na isa ynxu na shigo gari mai kake so na taho ma dashi, ya karashe maganar yana marairai cewa don yasan tsaf Noor zai karta masa wulakanci in yan tsiyar na kansa.”

Shiru kawai Noor yai masa bai magana sai da ya kara maimaita masa tambayar sannan yace “masa ka taho min da pure water nawa ya kare kuma dare yayi bana jin fita kar ka manta pure water na cema leda daya ba bottle water ba.”

Ajiyar zuciya ya sauke yace “ngd ma hakan maza gani nn shigowa insha Allah.”

Zama yai a tsakar gidan bayan ya shinfida tabarma, bai dade da zama ba yaji ana buga kofar gidan mikewa yai ya bude masa.

Shigowa khalifa yai ya ajiye ledar pure water guda biyu daya dakko sannan ya koma ya kara shigo da wasu sai da ya shigo da leda goma sannan ya janyo kofar gidan ya rufe da mukulli.

Zama yai ya ajiye ledar hannun sa yana kallon Noor dake ta banka masa harara ganin abinda ya siyo.

Cike da nutsuwar da ya azama kansa don lallashin Noor yace “maza ban siyo don na raina neman ka ko baka da yadda zakai ne, na siyo ne sbd kai din dan uwa nane kuma ba laifi bane don na siya ma Abu ko.”

Kallon sa Noor yai wannan karan yana kallon sa ne cike da wani yanayi mai wuyar fassaruwa.

A hankali yace “Maza kaima kasan ba don komai ne yasa bana son wani ya taimaka min ba sai don gudun wulakanci da gori gaba kafi kowa sannin abin da ya faru.”

Dafa sa khalifa yai yace “har abada ba zance wulakanci ko gori tsakanina da kai maza kai din dan uwa nane kuma amini na gaka yayana.”

Murmushi Noor yai wanda ya kara bayyana sirrin kyaunsa.

Bude ledar khalifa yai ya ciro abinda ke ciki kaxa ce lafiyyayya tasha kayan hadi sai maiko take tana kamshi sannan ya fito da yoghurt guda biyu masu sanyi ya ajiye.

Duk da bai dade da gama cin abinci ba sai da yaci wannan kazar sbd kaunar dake tsakanin sa da kaza…

Bayan sun gama ci sukai brush suka kwanta wanda kafin suyi bacci sun dade suna maganganun da bana ji sbd a hankali suke yinsu.


Zaune nake a tsakar gidan mu ina wanke alayyahun da zansa a jalof din shinkafar da nake kasancewar girkin mamanmu ne.

Zama na gyara ina juya shinkafar da ta kusan nuna ma, shigowa walida tai ita da hafsa yar gidan gwaggwo Amina.

Ko kallon su banba duk da inajin yadda suke sakin habaici.

Hafsa ce ta kalli walida tace “amaryar Alhaji wai dama amare suna zama a gaban murhu ne duk bakin tukunya ya gama sasu tsami.”

Dariya walida tai tana mika ma hafsa hannu suka tafa sannan tace “kinsan amaren ma kala kala ne dakwai wadanda ake ji dasu da kuma wadanda ake ko oho dasu”

Nidai ko kallon su ban ba na cigaba da abinda nake son basa gabana abinda yake damuna yafi karfin in tsaya ina biye musu.

Bayan na gama girkin na raba kowa na zuba masa nasa na mike ina wanke hannu na, kallon su Meenal da ke zaune suna wasa nai nace suzo suyi wanke wanke.

Shigewa daki nai na zauna ina kallon waya ta tun shekaran jiya bamuyi waya ba ko na kirasa baya dauka.

Dafa ni akai juyawa nai ina kallon mamanmuce dake tsaye a bayana.

Zama tai gefena ta rike hannuna tace “Maryo nasan kina cikin damuwa sosai na kyale kine naga ko zaki zo ki same ni amma naga baki da alamar hakan shiyasa nace ni bara nazo na same ki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button