NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi yai yace “duk suna lafia Gimbiya suna gaishe ki don mama tace min in tabbatar na kirata kun gaisa kafin na tafi”

Dan dagowa nai na kalle sa jin abinda yace, shikam ganin yadda na kalle sa yasa sa dariya.

Nima sai na samu kaina da sunkuyar da kaina kasa ina murmushi????

Cikin nutsuwa yace "min da farko dai sunana Mahmud Auwal ni haifaffen garin kano ne ina zaune da iyayena a unguwar sharada mu biyar mama ta haifa sauran mata ne kuma duk an musu aure sai ni kadai tunda nine auta kuma da dukkan alamu nima na kusa zama ma gidanci Insha Allah, na gama karatuna nayi degree akan kasuwanci kinsan yadda kasarmu ta koma ynxu sai addua, na nemi aiki amma ban samu ba ga takadduna sunyi kyau shiyasa baba kawai yaban jari na fara kasuwanci ina da shago na saida wayoyi da laptop a farm centre kuma ina da gidan gona fatan zaki karba ni a matsayin abokin rayuwar ki".

Cikin kunya na kara sunkuyar da kaina kasa.

A haka ya dinga jana jira tun ina amsa masa da eh koh a’a har na dan fara basa ansa, abinda na lura Mahmud yana da barkwanci sosai gashi yasan yadda zai yi mu’amala da mutane.

Muna cikin hirar Muhd yazo ya kawo dan farantin da mamanmu tasa pure water da lemon .

Hannu ya mikama muhd sukai musabaha yana ta tsokanar sa wai mamanmu zata basa shi yai mana zaman daki.

Muna cikin hirar walida ta shigo tasha matsattsen riga da skirt sai dan guntun mayafi data yafa a kafada tayi daurin ture kaga tsiya.

Burki taja ta tsaya tana kallon mu dama tunda ta doso layin taga mota a kofar gidan sai take ta sauri taga wane mai mota ne yazo gidan, sai kuma gashi taga muna zance ashe saurayin Maryo ne.

Mahmud kallo daya yai mata ya dauke kansa don ganin irin shigar dake jikinta gashi tai wani fauu sbd bleaching din da take.

Kallona ta tsaya yi wanda nima naba banxa ajiyar ta ina wasa da hannuna.

Ganin ba wanda ma ya nuna yasan da zuwan ta yasa taja tsaki ta shige gidan cikin sauri kamar zata tashi sama.

Tana zuwa ta samu Umma a zaune a palourn ta da mamaki take kallon umman don tasan bata zama a palourn duk sanyi ko zafin tana tsakar gida har sai baba ya dawo.

Ita kuwa umma abinda yasa ta shigo daki tunda taga fitowar Maryo da sumy kuma taga Maryo tasha kwalliya tasa kayan salllar ta tasan zance zataje gashi Sumy ta rakata soro ta dawo nan fa hankalin ta ya kara tashi don tabbas ba sai an fito an fada mata ba saurayi ne yazo gun Maryo.

Cike da hassada walida ta kalli umma tace “umma kinsan me nake gani kuwa saurayi ne yazo gun maryo fah kuma mai kudi wallahi don har da motar sa mai kyau yazo.

Zabura umma tai tace “me kika ce mai mota kuma”?

Tsaki tai kawai tace “toh karya zan miki ne abun da ynxu na wuce su ko kallona baiba”.

Zagaye dakin ta fara yi sai gumi take kamar wacce ke nakuda cike da tashin hankali ta dafa kafadar walida tace “ki kwantar da hankalin ki waleena ko zanyi yawo tsirara wallahi Maryo baza ta taba auren miji mai wadata ba……….”

Nikam bayan wucewar walida na dauka ko zai min maganar ta sai naga sabanin haka, don yi yai ma kamar baisan da wanzuwar taba.

Munsha hira sosai ganin ya kira min mama mun gaisa yasa nace” masa zan tafi kar dare yayi sosai mamanmu zata min fada”.

Dan bata rai yai yace “Gimbiya ban gaji da ganin kiba fa”.

Sunkuyar da kaina nai na rasa mai zan cemasa.

Cike da shagwaba yace “toh kin yadda na dawo gobe”?

Ware masa idona nai ina kallon sa baisan sadda ya fashe da dariya ba yana dauke idonsa akaina don baxai iya jure ganin kwayar idonta ba tai masa kwarjini da yawa.

Turo baki nai wanda ban masan nayi saba.

Lallabani ya hau amma sai na cemasa saina yi shawara da mamanmu duk abinda tace zan fada masa.

Har ransa yaji dadi don da dukkan alamu yaga mamanmu a tsaye take akan mu.

Number wayar mamanmu yace nasa masa yana miko min wayar sa, babba ce wayar Samsung mai kyau cikin nutsuwa na sama sa na ajiye wayar akan tabarmar ina tura masa ahankali ni nan wai dabara nai kar garin mika masa hannun mu ya hadu dana juna????

Sarai ya fuskan ci mai take nufi sai yai murmushi kawai.

Mikewa nai shima ya mike yana nannade tabarmar y miko min hannu biyu nasa na karba ina ce masa ya gaishe da mama da baba.

Shima sakon gaisuwa yaban kan na gaishe masa da mamanmu bayan ya jaddada min in rike wayar mamanmu a hannu na zai kirani.

Cikin gida nai ina murmushi, ai kam ina shiga dakin mu sumy ta kanannadeni sai murna take hadda tsallen ta wai da dukkan alamu ya samu karbuwa.

Murmushi kawai nai don kuwa ba karya tai ba ya kwanta min a rai????

Ina cikin fadawa mamanmu duk abinda ya faru yaro musa yai shiga da sallama a bakinsa(kanin sumy ne kuma sa’an muhd ne kamar yadda iyayenmu suke aminai kuma nida sumy muke aminai haka ma musa da muhd suke).

Gaishe da mamanmu yai nima ya gaishe ni sannan ya ajiyr ledar dake hannunsa yace mamanmu Ya Mahmud ne yace na kawowa Yaya Maryo.

Kallonsa nai kawai na mike na shige daki don cire kayana.

A palourn kuwa sai da mamanmu ta gama yan fade faden ta wai daga zuwa zai yi wahala haka???? sannan ta janyo ledar ta bude.

Gasashiyar kaza ce guda daya sai ice cream roba uku manya da kayan su chocolate.

Tuni Muhd da musa suka fara murna ganin kayan kwadayi haka.

Kashi uku mamanmu ta raba ta daukar ma Aunty kashi daya ta samusu a leda, muma ta ajiye mana kashi daya kashi dayan kuma ta raba gida biyu ta dau daya tasa a faranti ta bama muhd yakai ma Umma dayan kuma ta ajiye wa baba.

Ko da muhd ya kaima umma sai da tagama zage zagen ta wai ita ba mayunwaciya bace da za’a kawo mata wasu shegen kaza da ko pieces 4 basu kaiba, ta gama gorin ta kuma ta karbe????????

Bayan tafiyar Sumy ba dadewa kuwa ya kirani har munyi shirin bacci.

Miko min wayar mamanmu tai ta cemin sai da safe sbd baba ya dawo a lokacin kuma girkin tane.

Daga wayar nai cikin nutsuwa nai masa sallama

Amsa min yai yana cewa ya gajiyar dawai niya dashi.

Murmushi nai na fara masa ya yaje gida sannan nai masa godia kuma nace masa mamanmu tayi fada sosai akan hakan.

Hira muka sha tun ina dari dari har na saki jiki na muka sha hira sai tsumani yake da kalaman love yana kara sani ina jin ba ta biyu na duniya????

Bayan mamanmu ta bama baba duk labarin Mahmud, har ya soma fada kan an rainasa ba’a fada masa ba.

Ganin yana son tashin hankalin yasa ta fara basa hakuri cikin nutsuwa tace malam na fada ma tun jiya daza ka fita da safe saidai ko baka ji ni bane.

Haka ya gama kumfar bakinsa amma yana ganin leda sai ya washe ya fara cewa ashe yaron kirki ne da nake so na kore sa.

Girgiza kai kawai mamanmu tai, bayan ya gama cin komai dake cikin ledar ya wanko hannunsa a bandaki ya janyo matar sa jikinsa????????


Hara rayuwa ta cigaba da tafiya duk ranar Saturday Mahmud ke zuwa wanda zuwa ynxu mun saba sosai kuma ba karamin kaunar sa ya dasa min a zuciya taba, ina jin baxan iya rayuwa ba tare da shi ba.

Soyayya muke mai tsafta wanda ni da bansan ma na iya kalaman Soyayya ma sai da na hadu dashi, tuni na zama malamar Sumy gun Soyayya don ynxu ma ni nake koya mata yadda ake kashe murya da kalamai????

Zuwa lokacin yasan ina sana’ar gullisuwa da alawar madara don in har yazo zance sai na basa nace ya kaima mama, yana daga cikin dalilan da yake sashi kara ganin kimata da daraja yadda nake girmana masa iyaye.

Cike da gajiya na shigo gidan ganin mamanmu zaune a kofar kitchen yasa ni nufar ta ina gaishe ta amsa min tai tana hura wuta.

Kallona tai tace jeki ki watsa ruwa don daga ganin ki ansan kin gaji sosai.

Hmm mamanmu maganar gajiya ynxu ai sai hutu kuma yau fa muka gama jarabar kinga sai an koma kuma ana komawa zamu shiga ajin karshe na karasa ina sakin murmushi.

Allah ya sani na matsu na gama wannan makarantar.

Allah ya bada sa’a ya bada sakamako mai kyau

Ameen mamanmu.

Hannu nasa mata a girkin dan wake ne tai nan danan muka gama ta shiga daki ni kuma na tsaya na kintsa kitchen din nai wanke wanke na shige daki nima.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button