NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacin da ya koma gida ya sanar ma Inna ya samu matar aure tayi murna sosai ba bata lokaci aka je akai gaisuwa aka kuma sa biki watabiyu.

lokacin aka musu rabon gado sbd Abubakar yasamu ya kama ko haya a kano tunda ita amaryar tace baxa ta zauna a kauye ba.

Haka kuwa a kayi aka raba musu gado inda Abubakar ya samu katuwar gona, ba bata lokaci ya siyar da rabin gonar aka mata siyar mutunci kuwa tunda zamanin da ne nan ya taho kano da taimakon abokin sa dayai a garin kano sbd zuwa da yake yawan yi ya samu gida a gwammaja gidan na kallon gidan Abokin nasa(baban su sumyy beb????) siya yai kawai bisa shayarar baban su sumy tunda kudinsa sun kai.

Gidane mai kyau mai dauke da kofofi uku kofa ta farko wacce in an shigo gidan tana bangaren dama itace dakin Abubakar daki ne kawai sai bandaki.
Sai kuma kofar dake kallon kofar shigowa gidan ita kuma daki daya ne da falo sai ban daki a falon, a can karshen gidan kuma kofar kitchen ne dan madaidici sai kuma rigiya a farfajiyar gidan sai fili babba.

A haka akai biki lafia aka kawo amarya ta tare cikin gidan ta. Inda amarya ta dinke ita da Amina sbd yadda halin su yazo daya….

Na gaji gaskia ai nayi da yawa????

More comments more typing

Comments nd share plz

Mrs A.M

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

   Written by 
      Mrs A.M 

Page 5

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

A haka rayuwa take tafiya gasu Harira da Abubakar
Tuni Abubakar ya dawo kano da zama bayan yayi mahaifiyar sa itama ta dawo gidansa amma sam inna taki yadda.

Aikin gyaran mota ya fara zuwa yana koya har Allah ya taimake sa kuma yayi suna a harkar, inda in ya tashi kuma zuwa uku na yamma yake zuwa yana gadi a wata islamiyyar masu kudi bayan isha’i ya koma gida(wadannan sana’oin yake yi har ynxu)

Haka har sukai shekara biyu Harira bata samu ciki ba nan fa ta bi ta daga hankalin ta, ta fara shiga malamai akan rashin haihuwar ta suna bata magani.

A haka ciki ya bayyana a jikin ta, farin cikin da suka dinga yi ma bata lokaci ne inda ciki na shiga watan haihuwa ta haifi mace dukda ba haka ta so ba amma tayi murna

Ranar suna yarinya taci suna Walida.

Walida nada wata tara Abubakar ya gano Hadiza lokacin yaje karaye gun mahaifiyar sa, ita kuma jikar makotan su ne.
Nan danan ya fada ma inna yana son ta sbd tana da hankali da nutsuwa da kyau tubarkallah.

Inna tayi murna matuka ganin ya nuna yana son hadiza don ita kanta tana kaunar Hadiza sbd halinta na gari gashi kuma dama basa shiri da hariri, tunda Abubakar ya auri harira sau daya ta taba zuwa ta gaishe ta.

Kafin Abubakar ya koma sai da aka gama komai tsakanin sa da hadiza na aure aka sa wata 3 sannan ya roki inna alfaramar kar ta fadama Amina don inhar taji sai ta fada ma harira.

Bayan dawowar sa ya fito da yan kudaden sa yasa aka fara gina a filin gidan ana irin tsarin gun harira.

Nan fa harira ta daga hankalin ta ganin ana gini a gidan amma sai Abubakar ya kwantar mata da hankali yace inna yake so ta dawo gidan ne
Duk da bata son innar ta dawo amma hankalin ta ya dan kwanta tunda ba kishiyar bace????

Sai ana saura kwana uku biki sannan ya samu damar fadawa harira kuma yana fada mata ya gudu daga gidan ya nufi karaye bayan ya garkame gun amarya

Ba kalar haukan da batayi ba akan auren ta shiga malamai amma duk jnda taje saidai ace mata auren nn sai anyi sa in kuma ta matsa zata mutu sbd rabo ne mai tsanani a tsakanin su, sai dai amma a sa masa tsanar amaryar yaji baya kaunar ta

Da wannan ta samu ta nutsu.

Haka aka daura aure aka kawo amarya ta tare cikin gidanta, sati daya tai kawai na jin dadi amma tunda abubakr ya koma dakin harira shikenan zaman ya daina ma hadiza dadi

Wulakanci suke mata daban daban gashi sai ta koma ma kamar mai aiki itace girkin gida da share sharen tsakar gida. Duk da haka amma duk ranar girkin ta tana zuwa turakar mijin ta don duk asirce san da harira tai a wannan fannin baiyi tasiri ba.

Kusan atare suka samu cikin wanda cikin ma harira tayi kokarin zubar dashi sosai amma Allah bai bata nasara ba
Ita ta fara haihuwa ta samu namiji, farin ciki gun harira da malam bata baki ne tuni harira ta mance da cikin hadiza ma tunda ta haifi namiji
Ranar suna yaro yaci sunan kakansa Yakubu inda harira ta buga tsalle tace sam bata yadda ba sai dai a rufe sunan adinga ce masa faisal.

Bayan haihuwar faisal da wata daya itama hadiza ta haihu inda ta haifo yarinyar ta mai kyau tubarkallah.

Nan fa hassada ta rufe harira ganin kyaun yarinyar wacce malam ya sa ma Maryama ana ce mata maryo

A haka ake rayuwa a wannan gida sam malam baya adalci a tsakanin matansa da kuma yayansa don ya fison yan dakin umma da yaranta.
Inda mu kuma ko oho, Mamanmu tun daga haihuwar muhd bata kara samun ciki ba sai umma ce keta zazzago ya’ya

Tunda na fara girma nasan halin da gidan mu yake ciki nake tausayin mamanmu don ta kasance mai hakuri matuka gashi danginta kaf suna kauye kuma malam baya barinta zuwa sai dai in zamuje gano inna wacce tsufa ya kamata sosai.

A haka nake yan sana’oin ina saida alawar madara carbin malam da albishir sai ynxu kuma dana fara gullisuwa. Jarin dana fara dasu ma yayan su Sumy ne yaban tun waccen sallar shine na fara sana’a

Umma kullum cikin bakin ciki take da sana’ar ganin muna rufawa kanmu asiri don su omo da sabulun wanka duk basa gagarar mu har ma wani lokacin in wani daga cikin mu baya jin dadi da kudin muke amfani gun siyan magani.

Ba abinda zan cema su Sumy da iyayen ta sai godia don suna taimakon rayuwar mu matuka, sbd duk Sallah sai babansu ya mana dinki nida muhd tunda mu namu mahaifin ya daina mana sai dai yan dakin umma.

Chocolate colour ce fata ta wacce take a mulmule kamar ina kwana a AC, ni ba gajera ba kuma da zangaleliya ba daidai gwargwado ina da dan tsayi na, saidai siriya ce ni sosai sai aikin hips kamar an min surgery, Allah ya albarkaceni da kira mai kyau da boobs manya, shiyasa in har ba gani na kai ba hijab ba ba lallai ma kace min sirirya ba sai dai ko in kaga hannayena.
Ina da dogon wuya da siririyar fuska wacce ta dace da yanayin jikina mai dauke da gira siriya kamar anyi shaving da lumsassun ido masu dauke da kwaya blue sai siririn hanci na da bakina mai dan tudu kadan.
Alhamdulillah ni kaina nasan Allah yamim hallita mai kyau shiyasa kullum nake cikin gode masa.
Ina matukar son gashina sbd tsayinsa da santsin sa har tsakiyar bayana gashina yake zuwa, bana kitso sbd tsantsinsa kuma ina boye shi ban son ana ganin min gashi.

Fannin karatu kuwa tun muna kanana muke zuwa islamiyyar dake kasan layin mu mai suna Qabalu???? ynxu haka ina ajin sauka kuma insha Allah mun kusa sauke wa, boko kuwa ta gomnati muke zuwa dama tun daga nursery har ynxu da na ke ss 2 mun kusa fara zana jarabawar shiga ajin karshe, muhd kuma yana jss 1.

Ni kaina nasan kaina baya ja a boko shiyasa ma bana bata muhimmanci sosai don bana daukar kasa data 15 saidai ina gane English sosai amma mayar wa yana dan min wahala don ma ina da courage knn wai.

A islamiyya kam Alhamdulillah don nan ne inda ni kaina nasan guruwa ce ta wannan fannin bama kamar gun fannin karanta Qur’an da kuma sira Alhamdulillah.

A haka bacci ya dauke ni ba tare dana shirya masa ba.


ABUJA

Unguwar Asoroko na nufa inda tun daga nesa na hango wani tamfatsetsan gida wanda ya kusa mamaye unguwar
Cikin gidan na kutsa na shiga dukda security din gidan, gida ne na gani na fada kudai hasaso kawai, kofar danake kyautata zaton shine zai sada ni da ainihin cikin gidan na nufa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button