NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Fitowa nai na kalli yaron da yace shike masa gyaran gida, yaro ne karami don baifi sa’an Muhd ba.

Kallon sa nai nace “ya sunan ka?”

Da sauri yace “Ina kwana Aunty sunana haruna”

“Lafia qalau haruna baka da islamiyya ne ynxu ko sai anjima.”

“Ynxu xan tafi Aunty sai 12 muke tashi daga nn kuma mu shiga karfe 1 mu dawo karfe 5.”

Kallonsa nai nace “to Allah ya bada sa’a in ka taso sai kazo ka karbi abinci koh.”

Cikin murna yace “toh Aunty ngd sosai Allah ya saka, daga haka ya juya ya tafi.”

Rufe kofar gidan nai na tafi daki na kwanta.
Ko minti 5 banyi da kwanciya ba naji ana buga kofar gidan.

Fitowa nai ina mita a raina ashe haka ake auren duk abi a dame ka da buga gida haba.

Ina budewa naga bintu tsaye sai wani ciccin magani take, tuni nima na hado duk wasu wulakanci na da nake da har da wasu sababbi na yafa a fuskata.

Kallon idanun ta nake naki magana kawai ina mata wani kallo dake sa mutum saduda matukar yana ganin kwayar idanuna hakan ya faru da ita kuwa don da sauri ta sauke idanun ta daga kallo na.
Miko min flask din hannun ta da Jug tai tace “gashi inji Inna tace za’a kawo na rana.”

Karba nai nace “kice mata mun gode sosai Allah ya kara lafia, daga haka na juya na kulle gidan na nufi kitchen.”

**
Shiru bintu tai tana kallon kofar dana rufe ta dauka zata ji tsoron ta kodan yadda take mata kallon yarinya amma abinda tai mata yanxu yasa taji tsoron ta ya kamata.

Juyawa tai ta shiga gida jiki a sanyaye, tana shiga gida Inna dake zaune tana yanka alayyahu tace “har kin shigo”

“Uhm” kawai tace ta shige daki, tabe baki inna tai don ta lura da wasu sabbin dabi’un da bintu ta fara.


Kitchen na nufi da flask din ina zuwa na ajiye akan durowar kitchen din, dan lungun dake kitchen wanda yai kamar store na nufa nan naga kayan abincin daya siyo, shinkafa karamin buhu dai carton din taliya, macaroni, indomie gasu Maggi, onga, egg, dankali, doya har da albasa.
Kusan komai ma ya siyo tattasai da tumatir ne kawai za’a siyo sai wasu kananun abubuwan.

Gyara su nai yadda nake so sannan na fito akan turowar naga wasu ledoji wadanda ban kula dast dazu bama, budewa nai naga nama ne sai kaji guda biyu da bushashen kifi.

Ajiye kajin da naman nai a fridge sbd fridge din mai hade da freezer ne, shi kuma bushashen kifin nasa a fridge.
Flask din da inna takawo ba bude kosai ne sai kunu a jug din, diba nai na ajiyewa Haruna wagowar daki na wuce naci na koshi don dama yunwa nake ji.

Ina gama wa na kai plate da cup din kitchen na wanke.


Noor kuwa yana fita daga gidan gurin aiki ya wuce a machine dinsa don dakwai motocin daya ke son gyarawa, kudin account dinsa yayi kasa sosai sbd kayan abincin daya siyo.

Ahaka ya isa gurin aikinsa yana tunanin wannan nauyin daya hau kansa.

Yana karkashin mota khalifa yazo hakan yasa shi fitowa, wanko hannun sa yai da fuskar sa sannan yazo gun khalifan.

Musabaha sukai inda khalifa yake tsokanar sa da ango ango.

Wani banzan kallo yai masa yace “ka iya bakin ka don kasan bana son raini.”

Dariya Khalifa ya fashe da ita yace “sannu babana wai ma mai yasa ka zuwa gun aiki ne na dauka kana can kana shan amarci ai.”

Shafo kwantaccen gemun sai yai yana tuno maganar inna hakan yasa shi girgiza kai kawai yace u’re not serious man.

Tun khalifa na tsokanar sa ganin baya biye masa yasa shi kawai yi masa maganar daya kawo shi

Sun dade suna magana wacce bana ji sannan Noor ya dauko wata leda mai dan girma ya basa ban ji mai yace masa ba haka sukai sallama ya tafi shi kuma ya cigaba da aikin sa.


Walida ce zaune a gaban katon murhu ta daura babar tukunya kamar wacce take cin kwana ukun shinkafa, gefenta kuwa uwar masu gida ce tsaye akanta.

Cikin mugunta uwar masu gida ta dala mata dundu a bayan tace “don uwarki baza ki tsince mana shinkafa dakyau ba sai munzo muna ci da buntu.”

Share hawayen ta tai duk fuskar ta ta kumbura sbd dukan data sha da safe gun matan gidan da yaran su yan mata daka sun ce mata ta dama kunu da safe tace bata iya ba suka hadu suka zane ta kuma suka sata dole ta dama kunun amma ko yan mata basuyi ba.

Haka ta dafa jalof din shinkafa kwano daya duk sai gumi take wai ahaka don ma uwar masu gida na tsaye akanta haka ta gama uwar masu gida ta raba wa kowa nata itama aka yafa mata.

Da daddare kuwa tana jiran ace tazo ta daura abincin dare amma shiru ganin 8 tayi gashi tana jin yunwa yasa ta mikewa ta fita tsakar gida.

Ganin su tai dukkan su zaune wasu nashan gari wasu nashan kunu wasu kuwa awara ce a gaban su.

A hankali ta nufi gaban uwar masu gida tace “naga har dare yayi ba’a daura komai ba mai zan dafa ne?”

Tsaki uwar masu gida tai tace “bama girki da daddare in anyi girkin rana kowa ajiye wa yake yaci kadan don har na dare ake hadawa.”

Shiru Walida tai tana kallonsu ba wanda yaji tausayin ta ko ya sammata wani abu haja ta gaji da zama ta koma dakin ta.

Shiru tai tana kallon kwanon saman dakin nata kawai ta fashe da kuka, duk kalar muguntar da suka dinga wa mamanmu da maryo suka shiga dawo mata.

Duk abinda suke wa mamanmu basa hana su abinci amma fa suna zuba musu kadan kuma ga rashin mutunci sai gashi ita tana kishi da sa’annin babarta ga duka ga yunwa……….


Bangaren mamanmu kuwa dukda yadda auren yazo amma hankalin ta a kwance yake sai kewar maryo da suke itada Muhd.

Tuni gida ya dawo ba baki duk sun tafi sai kewar amare da suke don ko ba komai ynxu sun rasa mai musu girki mai dadi har baba shi kansa yayi kewar su.

Hankalin ta kwance ynxu take abubuwan ta ba ruwanta da shiga shirgin umma wacce bata da aiki kullum sai habaice habaice ita ala dole yar ta ta tafi dubai ana mata bakin ciki..


Karfe 12 haruna yazo karbar abincin sa, abincin dana ajiye masa na dauko na basa.

Anan ya zauna yacinye ya koshi ya wanke min kwanukan a fanfon tsakar gidan, yana gama wankewa yace “Aunty ba abinda zan miki ynxu”

Kwanikan inna na basa nace “kasan inna aiko?”

Daga min kai yai hakan yasa na basa nace ya kaimata.

Bayan kamar minti 5 ya dawo yacemin ya kai mata daga haka ya juya ya tafi.

Gurin karfe 3 na rana Bintu ta shigo dauke da kula guda biyu, godia nai mata kawai na dauki kular nakai kitchen.

Ganin zata fita yasa nace mata ta fada wa inna basai ta kawo mana abincin dare ba wannan ma ya ishe mu, gyada min kai tai kawai ta fita.

Karfe shida ta dawo taci kwalliya, tana shigowa ta saki fuska sosai muka gaisa ta zauna akan kujerar palourn tana danna wayar ta.

Ana kiran sallah Ya shigi gidan hannun sa dauke da leda.
Da sauri ta mike ta fito ta nufi gunsa tace…….

Mrs A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

   Written by 
      Mrs A.M 

Page 22

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

   Cikin sauri da yanga ta ce "ina wuni Yaya an dawo lafia?"

Ko kallonta baiba yace “lafia,” daga haka ya shige dakinsa, ko mintu 3 baiba ya fito sanye da jallabiya da hular data rufe kansa.

Toilet ya shiga ya dauro alwala daga nan ya fice daga gidan.

Ina ganin ya fita na fito da sauri na shiga bandakin, lumshe idanuna nai jin wani kanshi mai dadi da yake, ahaka na dauro alwala na fito.

Kallon bintu nai dake tsaye har ynxu a gun tabe baki nai na wuce don tsaf ynxu na gama karantar yarinyar wato kwalliya tai ta daidai ce lokacin dawowar sa ta shigo.

Ina zaune a daki ina sallah naji ya shigo gidan, hakan yasa ni kara nutsuwa sosai.

Shikuwa Noor yana shigowa ya dan tsaya yana kallon bintu dake tsaye a inda ya barta da dukkan alamu ko salla bata yima.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button