NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Amincin Allah ya tabbata a gareka ya farin cikina.

Murmushi yai yana cewa tare da naki Gimbiya ta, kiyi sauri ki fito na ganki don na mastu nayi to tozali da kyakyawar fuskar ki mai cike da kwarjina.

Kara kashe murya nai nace nima na matsu na ganka Sahibina gani nan zuwa insha Allah.

Kashe wayar nai na fito, mamanmu yana waje wai na fada ina kauda kaina daga kallon mamanmu.

Itakam zuba min ido tai ganin hadda su Jan baki, abinda tasan bana yi don bana son kwalliya amma tunda na hadu da Mahmud kullum zaizo sai na shafa powder da jan baki dama kwalli kam wannan wajibi ne kullum sai nasa.

To kar ki dade dai kinga anyi isha dare yayi.

Insha Allah mamanmu.

Fitowa nai ina zuba kamshi, Aa kanwata kanin nawa ne yazo.

Hade rai nai ina juyawa gun dana ji muryar sa

Suna zaune duka yan dakinsu sun zagaye umma shi kuma yana daga gefe yana cin tuwo.

Kara hade rai nai nace kaifa matsala ta dakai kenan faisal ka iya rashin kunya ynxu Yaya Mahmud dinne kanin ka?

Don uwarki inba kanin saba yayansa ne ba kanwar sa yake neman aure ba.

Kallon umma nai, har na bude baki zan magana mamanmu ta daga labilen palourn ta kalleni, hanya ta nuna min tana cewa wuce bana son shirme.

Wucewa kawai nai raina a bace duk yadda nake farin cikin ganin habybyn nawa sai naji raina ya baci bana ma son fitar.

Ina fitawo na gansa jingine a gefen motar sa suna gaisawa da Umar saurayin sumy, tana gani na kuwa ta taho guna tana dariya taci kwalliya itama cikin riga da zani sai mayafi babba data yafa.

Kallona tai tace kaga manyan mu a soyayya, juya idona nai ina cewa yasan ranki.

Dariya tai tace amma waya bata miki rai ne duk irin dokin da ake na ganin sahib.

Na bude baki zan magana kenan naji………

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
        Mrs A.M 

Page 10

Dedicated to ????Noor???? Fans Club

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 Muryar Mahmud naji yana cemin Gimbiya ku gaisa da Umar din

Juyawa nai gunsu ina rike da hannun Sumyy, cikin mutun tawa muka gaisa ina tsokanar sa kan yadda ya mallake zuciyar aminiyar tawa.

Cikin sauron gidan mu muka shigo bayan habybyn nawa yai ma su Umar sallama.

Kan tabarma muka zauna, cike da so da kauna muka shiga hira wadda yawancin hirar Mahmud ne ke yinta yana fada min yadda zai nuna min kulawa bayan auren mu.

Lokacin da ya tashi tafiya alawar madara da gullisuwar da nai masa na basa, idona duk sun cicciko da hawaye don tun kafin yai tafiyar ma na fara missing dinsa.

Kallo na yai yace “ki kulamin da kanki kinji Gimbiya ta kar ki damu baxan dade ba fah wata 1 ne kawai kuma kinga lokacin da zan dawo har an zo an bani ke koh”?

Rufe fuskata nai da Hijab dina ina murmushi, murmushi yai shima yace “kar ki manta ki fadama baba fah cikin satin nn suka ce zasu zo sai ya fada ranar da zasu zo.

Ji nai gabana ya fadi bansan dalili ba amma kawai sai nake jin wani strange feeling akan zuwan su.

Haka mukai sallama muna jin kamar kar mu rabu.

Ina shiga dakin mu Muhd ya shigo hannun sa rike da ledoji guda biyu daya babba daya karama, mamanmu ya mika ma.

Ajiye wa yai a gefenta ya zauna yana cewa “mamanmu yace ynxu zai kira wayar ki wai ki dauka, ko rufe baki bai ba kuwa wayar mamanmu ta fara kara.”

Daukar wayar tai sai sunkuyar dakai take kamar tana gabansa????????.

Cikin girmamawa ya gaishe ta.

Amsawa mamanmu tai tana cewa ya su maman, ka gaishe su sosai

“Zasu ji insha Allah mamanmu, dama mamanmu waya na siyo mata nace amma bara na kira na roki alfarmar a barta tai amfani dashi mamanmu don Allah.”

Shiru tai sannun tace “ban ki ta taka ba amma dawainiyar tai yawa.”

“Mamanmu bkm ai nima danki ne dama alfaramar da nake nema mamanmu kuma su Baban nawa sunce cikin satin nn zasu zo amma a tambayi baba yaushe yake ganin ya dace suzo?”

Murmushi ne ya bayyana a kamilalliyar fuskar mamanmu yana washe baki cikin farin cikin da ya kasa boyuwa tace “toh bkm Allah ya saka da alkhairi ya kara arziki mai albarka ya raba ka da iyayen ka lafia, zanma Malam din magana duk abinda yace zata fada ma insha Allah”.

“Ameen mamanmu Allah ya kara girma”.

“Ameen sai da safe ka gaida su maman taku”

“Zasuji insha Allah Mama”

Ajiye wayar mama tai tana kallona, harara ta zuba min ganin yadda na tsura mata ido ina kallonta.

Tsaki tai kawai tace ke kam Maryo baki yo halina ba baki da kunya sam, ynxu ina waya da saurayin naki ne kuka zuba min ido ba ko yar kunyar nn ta fulani ki tashi ki shige daki.

Dariya nai kawai ina ninke Hijab dina, daki na shiga na cire kayana na shanya su akan murfin wardrobe dinmu.

Rigar dana ke sawa in zan bacci na dauko, material ne ya tsufa ya kode shi nasa bayan na cire bra dita don bana bacci da ita, hula na sa da sauri jin muhd na kwala min kira cikin dauki.

Da sauri na fito daga dakin ina kallon sa, yana tsaye hannun sa rike da kwalin waya yana tsalle.

Ganina da yai yasa sa tahowa da sauri ya miko min wayar yana dariya.

Yy Maryo kinga Mamanmu tace taki ce kema ynxu kina da waya kuma babba ce zaki dinga mana hoto a ciki koh kuma kina sa mana kallo muna kalla.

Kallon kwalin wayar nai sannan na kalli mamanmu gabana na faduwa don banson mai zata ceba.

Itama kallona tai tace ki karba mana ai ya kirani ya nemi alfarmar a baki, kawai nidai abinda zan cemiki shine kiji tsoron Allah karkiyi amfani da wannan wayar gurin sabama mahalliccin ki tunda zamani ya lalace ynxu itace hanyar da ke saurin bata ma mutane tarbiyya.

Insha Allah mamanmu baxa ki same ni da aikata wani abu makaman cin haka ba.

Allah yasa ta fada tana bude dayar ledar da ke dauka da kaza guda biyu manya da holandia shima guda biyu sai kayan chocolate.

Karbar wayar nai daga hannun muhd ina jin wani farin ciki na ratsa zuciya ta, wai yau ni Maryo ni ce ke dauke da waya babba kuma tawa.

Kallon wayar nai ina cirota daga kwalin ta Samsung S8+ ce golden, wayyooo Allah bansan lokacin dana buga tsalle ba cikin murna na matso gun mamanmu ina muna mata wayar.

Karba tai itama tana sa mata albarka sannan ta mika ma muhd dake ta miko hannu yana so a basa.

Dawowa yai kusa dani ya zauna yana ta shafa wayar muna cikin haka baba ya shigo da sallama.

Amsa masa mukai ina kallon sa, tunda na fara zance duk ranar Saturday sai ya shigo dakin mu don yasan Mahmud zai kawo wasu kayan makulashen, shikam zai shigo a basa kason sa har wulakanci ya rage ma mamanmu duk ranar da zan zance tunda ya taba zagin mamanmu ranar da zan zance akan bata gama girki da wuri ba da daddare wanda kuma laifin sa ne bai kawo abinda za’a dora ba sai bayan magriba.

Ranar da yai zage ta kuwa da daddare dana dawo daga xancen bayan mamanmu ya ajiye masa namansa a leda daukewa nai na boye, da ya shigo kuma ya ganmu muna cin naman amma masa da mamanmu ta ajiye an name sa an rasa, tunda ga nan duk ranar asabar zaka ga har wani nan nan yake da mamanmu????

Zama yai yana amsa gaisuwar mu sai washe baki yake ganin kaza akan plate, kallon mamanmuce yai yana fara’a yace Hadiza ina nawa ne ni tun da na shigo sai kamshi nake ji.

Miko masa ledar da aka sa masa nasa mamanmu tai, da sauri ya karba ya bude ledar wata dariya yai ganin kaza katuwa a leda sai holandia hadda chocolate biyu a ciki.

Ganin yana cikin nishadi yasa mamanmu cewa malam yaron nn Mahmud dama ya ce na fadama, ganin haka yasa na kama hannun muhd muka shiga daki.

Kallon mamanmu yai yace ina jinki mai yace shi saurayin uwat tawa?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button