NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallonsa nai naga sai kallo na yake hakan yasa na watsa masa dara daran idanuna masu dauke da wasu sinadarai???? na ce nawa wannan.

Washe baki yai yace dubu uku yan mata amma tunda kune kannena ki bada dubu biyu da dari biyar kawai

Dubu biyu da dari biyar din na dauko nace kaga wannan sune kudina zai siyi waya ta dubu biyu nasai charger mai kyau ta dari biyar wacce baxa ta lalace da wuri ba.

Irin kallon danaga yana min ne yasa nace kaga malam ni bani zan siya ba mamanmu ce ta aiko ni kayi sauri plz tace kar mu sake muyi yamma.

Shikenan toh kawo kudin na hada muku hadda charger, mika masa kudin nai shikuma ya hada min wayar da charger ya miko min.

Dudduba wayar na tsaya yi sai da na tabbatar komai yana yi sannan na na ciro sim din mamanmu wanda dama ni ta bama na ajiye mata nasa a wayar na kunna.
Cikin farin ciki na duba contact naga komai nanan na dudduba sannan na kalle sa nace malam ina zan samu inda ake siyar da katin waya na MTN.

Kawo ina ma siyarwa na nawa kike so, dari biyu na fada ba tare dana kalle sa ba ina mika masa kudin.
Katin ya ban nasa nayi wa Sumy flashing a wayar ta kasan cewar ita tana da waya amma ita ma keypad ce baban su ya siya mata lokacin da muka shiga ss2 tunda tana da samari ita.

Sallama mukai masa muka fito, adaidaita muka hau sai murna muke don nasan yau mamanmu ba karamin samana albarka zatai ba dukda tana samana ma.

Muna sauka wata mota ma tazo tai parking a kofar gidan mu, ina lura da motar tun daga farm centre din take biyo mu.

Assalamu alaikum wata lafiyyayyar murya ta fada……


Abuja

Zaune take a palourn tana kallo gefe daya kuma amsa waya take gaban ta kuma center table ne wanda aka dora wata kosasshiyar gasashiyar kaza guba taji hadi sai maiko take tana kamshi ga holandia a gefe an zuba wani cub an ajiye.

Cikin kissa irin ta manyan mata ta muskuta katun katun din mazaunan ta ta ce “darling mana”

Daga dayan bangaren naji wata murya ta babban mutum cikin nutsuwa yace babyna menene????♀️

Kara muskuta mayan duwaiwanta tai tace “har ynxu baka dawo ba kuma kasan yadda nake cikin bukatuwar ganin ka kuwa hmm ji nake kamar nai tsuntsuwa na ganni a office dinka darling”

Daga dayan bangaren wanda aka kira da darling yai murmushi yace “babyna ina hanya ynxu xaki ganni kinji amma mai kika tanadar min”

Murmushi tai tana wani fari da mitsi mitsin idonta tace “sai ka dawo tukun don komai na tanadar maka shi”

A haka sukai sallama cike da kaunar junansu, bayan ta ajiye wayar ta juyo kan kazar nan amma abin mamaki kafin minti talatin tuni ta cinye wannan uwar kazar da holandian nn kaf.

Dagowa tai jin ana sallama wata matashiyar budurwa ce ta shigo wacce baxa ta wuce shekara 18 ba fara ce tas don har yellow yellow take amma kana ganin kasan natural ne

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
       Mrs A.M

Page 7

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Cikin nutsuwa budurwar ta ke tafiya har ta matso kusa da matar da take zaune.
Tsugunnawa tai tace Mummy ina wuni

Harara ta galla mata tace da ban wuni ba zaki ganni anan shegia munafuka kawai, dallah tashi ki ban waje.

Mike wa tai da sauri ta shige wani lungu da zai sadata da ainihin part din mahaifisar ta.

Wacce aka kira da Mummy ce ta kara jan wani dogon tsakin tace yar iska kawai yarinya sai shegen kyau kamar bala’i haka dai zaku kare daga ke har uwar taki.
(Haj Suwaiba knn uwar gida kuma amarya a gidan Alh Muhammad Sombo sananne kuma fitaccen da kasuwa wanda aka ji dashi a fadin naija da kawayen ta)

Matashiyar budurwar kuwa tana shiga palourn nasu ta tsaya ta share hawayen ta tsaf tana kare ma palourn nasu kallo wanda yaci wasu shegun Royal chairs golden nd white she kamshi yake da sanyi.

Murmushi tai tana alfahari da Ammin ta duk gidan ba inda yakai part din Ammin ta kamshi da nutsuwa sai kam part din Abba shima kuma sai in ranar girkin Ammin ne.

Dakin Ammi ta nufa don tasan anan kawai zata same ta

Tana shiga kuwa ta ganta zaune kan sallaya da charbi a hannun ta tana ja
dagowa tai yana kallon yar tata tai murmushi tace salma har kin dawo kinyi sauri yau amma.

Kara sowa tai tana kallon mahaifiyar tata wacce idonta sukai ja-ja alamun tayi kuka knn.
Riko hannun Ammin tai tace Ammina kuka kikayi koh.

Da sauri ta kau da kanta daga kallon salman tana kokarin shanye hawayenta da damuwar dake son dole sai ta nuna akan fuskar ta tace ba kukan da nai kuma dakika sani a gaba da tambaya haifata kikai ne.

Yar siririyar dariya tai tace oh Allah Ammi yau kuma da fada kika tashi koh nara na gudu dakina gaskia ta karashe tana mikewa.

Murmushi ammi tai tace Allah ya shirye ki gaskia.

Ameen Ammi na ta fada tana fita a dakin.

Direct dakin ta ta nufa wanda nan ma ya hadu iya haduwa tana zuwa ta fashe da kuka ta zauna akasan carpet din dakin tana kuka amma mara sauti don kar Ammi taji.

Tana matukar tausayin kanta da Ammin ta akan kaddarar data same su kullum cikin addua suke akan lamarin.

Duk Ammi tabi ta rame duk da dama ba mai kiba bace amma tana da jiki daidai gwargwado jikin ta mai kyau ne da baya nuna shekarun ta dukda ta yi hamsin amma halik da suka tsinci kansu a ciki yasa kullum kaga Ammin sai ka tausaya mata.

Amma ahaka Abbansu baya jin tausayin ta yake zuwa har part dinta wataran ya kare mata tana di tsaf.

Da kyar ta lallashi kanta ta mike ta nufi bandaki don yin wanka


Fitowa yai daga dakin sa yana kulle kofaf don ya makara zuwa gun aiki amma ahaka sai yanga yake gun kulle kofar da kwado.
Sanye yake da riga mai gajeran kalar Ash sai wando dogo wanda bai matse saba black colour kayan duk da masu saukin kudi ne amma sun amshe shi matuka.

Yana gama kulle kofar ya janyo mashin dinsa mai kyau ya ajiya a kofar gidan sannan ya rufe kofar gidan ya hau mashin dinsa ya nufi garejin da yake aiki.

Yana zuwa ya shiga da mashin dinsa cikin garejin ya ajiye sannan ya sauko ya kashe mashin din.

Cikin nutsuwa yake tafiya duk wanda ya gansa zai gaishe sa amma sai dai ya daga masa hannu kawai yai gaba mutum ne shi mara son hayaniya.

Cikin nutsuwa ya fara gudanar da aikin sa sbd basirar da Allah yai masa gun gyara shi kansa ogon su tunda yazo ya fara aiki a garejin gurin ya kara daukaka don yasan aikinsa duk wata mota ya iya gyarata kuma yasan kan Wayoyin wuta sosai.

Bashi ya gama gama ba sai bayan magriba ahakan ma da kwai wasu motocin da suke a ajiye bai taba suba.

A gajiye ya isa gidansa yana zuwa ya bude kofar ya shiga kulle.


“Waalaikumussalam”

A tare muka amsa masa mu uku.

Cikin sauri ya tawo kusa da muhd ya mika masa hannu, da sauri muhd ya mika masa hannu shima sukai musabaha sai murmushi yake ganin babban mutum ya mika masa hannu.

Sakin hannun muhd yai ya kalle sa yace abokina ya sunan ka? “Muhd” ya amsa masa yana kara washe bakinsa.

Sunan ka mai dadi abokina, da sauri muhd ya sa dariya cikin jin dadi.

Kallon mu yai yana murmushi.
Ki kam na kare tamke fuska ta don kar ya kawo min zancen raini????

Kallon sumy yai ganin ta danfi sakin fuska yace kanwata sannun ku “ina wuni”

Da sauri mu duka muka kalle sa sai kunya kuma ta rufe mu, yana kallon mu yana cigaba da nazar tar mu.

Cikin sauri muka hada baki gun ce masa ina wuni.

Hakan da mukai yasa ya jara jin dadi a ransa don daga yadda mukai yasan an bamu tarbiyya mai kyau.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button