NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Ai kuwa ta shaka har ta bude baki zatai magana ko mai ta tuna kuma sai tayi kwafa kawai ta shige dakinta.

Mu kuwa ranar yini mukayi muna danne danne a wayar nida Sumy, wacce itama kamar hadin baki umar dinta ya kawo nata Huawei jiya mai kyau.

Anan muka shanta ke da Faisal yana ta tura mana indian hausa da games, whatsapp ya turo mana da Snapchat bai bar dakin mu ba sai da ya bude mana whatsapp dukkan mu da Snapchat ya nuna mana yadda ake amfani dasu.

Ai kuwa mun ji dadi don sai murna muke, a ranar na fada wa Mahmud wanda tuni ya sauka a China lafia.

Bayan munyi waya dashi nake fada masa sakon baba akan yace suzo ranar Thursday, ai kuwa murna agunsa ba’a magana don kamar an daura auren haka yaji, tun ina biye masa har yasa na fara jin kunya kawai na kashe wayar.

Zaune take a gaban wani mutum gabjejen gaske yana sanye da gajeran wando duk yayi dukun dukun, ga katon tumbi wanda ya zauna da kansa mummuna ne na gaske bakikirin da idanun sa jajir.

Bude katon bakin sa yai yace ya ke la’ananniya me kike so ayi mata ynxu.

Gyara zaman ta tai tace so nake a raba su Mai share min hawaye na kai kadai ne kake biya min bukata ta tun tsawon shekaru masu yawa shiyasa na kara dawowa gunka ya shugaba na.

Dariya ya saki yana dukan cinyar sa, kallon ta yai yace me kike so ayi musu ynxu yake la’ananniya.

So nake a raba su yaji ya tsane ta kuma kar a bari wannan auran ya tabbata ita kuma ayi gaggawar tunzira zuciyar malam ta yadda zai aura mata talaka, sannan ya shugaba bana in son samu ne ma shi din a dawo da zuciyar sa kan yar wajena Walida kawai ya aure ta.

Duba kasar gabansa yai yayi wajen minti 5 yana zane akan kasar kafin ya dago ya kalle ta, cikin muryar sa kamar ana tada inji yace baxai taba auren yar wajen ki ba don ba matar sa bace in kuma kin matsa sai ya aure ta tofa baxa tayi ko wata 1 ba zai saketa.

Cikin sauri tace abar sa kawai in yaso ita kuma sai a bata maganin farin jiki wanda zai sa masu kudi suke mata layi, amma fa masu kudin ma wadanda zasu aure ta Shugaba.

Dariya ya kara saki yace angama, sannan ya hade rai kamar bai taba dariya ba yace tabbasa za’a rabasu kuma baxa ta aure sa ba amma sai kin kwantar da hankalin ki sbd abin zai dau lokaci sai an kusa auren sannan komai zai watse kuma ki sani ita yarinyar baza’a iya biyowa ta gunta ba sbd tana riko da addua sosai kuma uwar su ma a tsaye take akan su dama kinsan wannan koh.

Daga masa kai tai tana jin wani sanyi ya fara ratsa ta sbd tasan tunda yace haka toh fah anyi an gama kawai(wa’iya zubilla)

Saidai ki kwantar da hankalin ki ta wajen sa zamu biyo don naga wana da wasa da ibada kuma baxa ta aure saba amma fa a abinda nake gani in kika hanata auren zata auri wani talaka amma…..

Cikin sauri tace Ya shugaba na tunda baxa ta aure sa ba ta auri koma waye kuma talaka kawai.

Jinjina kai yai yana kallonta yace an gama ajiye duk abinda kika zo dashi ki wuce la’ananniya.

Dubu biyar ta ajiye masa shi kuma ya miko mata wani leda mai dauke da magani

Hannu tasa ta karba, cikin katuwar muryar sa yace ki bata wannan ta zuba sa acikin turare na gwangwani duk lokacin da zata fita ta shafa turaren a goshin ta da kafafun ta baxa tai sati ba wani hamshaki zai fito.

Kuma ki tabbatar yana fitowa kar ayi wata ba tare da manya sun shiga zancen ba.

Cike da murna tace an gama kanin shedan godia nake Ya shugaba na. Da baya da baya take tafiya tana zabga masa kirari har ta fita.

(Allah ya tsare mana imanin mu ya kare mu daga sharrin zuciya Ameen)

Ranar Alhamis kamar yadda baba yace iyayen mahmud suka zo a gidan su sumy aka sauke so don mu agidan mu bamu da dakin saukar baki sai sauron gidan mu.

Bayan an gama komai sun kawo kudin zance 50k da kuma goron sa rana, aka sa biki bayan na gama WAEC da sati biyu wanda ya kama nan da wata hudu knn.

Basu kayan snacks din da akai musu akai har sun mike zasu fita kanin baban Mahmud yace………..


Cike da masifa dada tace shidai madu ban san me yake so ya koma ba wallahi duk son dayake ma Halimatu ashe karya yakw tunda yaudarar ta kawai yake.

Kallonta saudat tai hakan yasa dada hade rai tace toh karya zan miki ne ba yaudarar ta yake ba ji fah daga auren wannan katuwar mata ya juya ma halimatu baya sai kuma ta kara dora hannaye akai ta mike ta buga tsalle ta rushe da ihu tana ware kafafu kamar wacce zatai dambe.

Ganin haka yasa salma da saudat kwanciya suna kara fashewa da dariya

Ita kuwa dada cikin kuka tace ya kuke dariya kuna ganin da ni kaina rabon da Madu yazo ya gaishe ni wajen wata 5 knn sai dai duk karshen wata ya aikoma da kayan abinci toh don ubansa ce masa nai mayunwaciya ce ni eh, ta karashe tana buga kirji

Haka tai ta matsifa har sai da ta gaji sai kuma ta zauna akan lallausan carpet din palourn ta daga hannu sama tana hawaye tace Allah ya shirya min kai Madu na ya dawo dakai hayyacin ka

MORE COMMENTS MORE TYPING

MRS A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

       Written by 
           Mrs A.M

Page 12

Dedicated to Daughter Princess????????

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Kanin baban Mahmud ne ya tsaya yana kallon Baban Sumy kasancewar shi baba ya bawa wakilcin auren Maryo, cikin dattako yace “muna kara godia a kan wannan karamcin da kuka nuna mana Allah ya tabbatar da alkhairi insha Allah kuma baxa ku sami wani matsala a gare mu ba.”

Murmushi baban sumy yai shima yace “insha Allah muma ba wani matsala sbd yarinyar nn tana da hankali da girmama manya Allah dai ya tabbatar mana da alkhairin sa.”

Hada baki su mai dukkan su suka ce “Ameen.”

Bayan sun rakosu waje sun tafi baban sumy ya kalli Liman yace “akaramakalla ga wannan, mika masa 50k din yai wanda hakan yasa baba saurin kallon sa.”

Shima kallon sa yai yace “a matsayi na na baban Maryo kuma waliyyin ta shiyasa na bawa liman ajiyar kudin nn in Allah ya kaimu lokacin bikin sai yai mata amfani dashi gun siyayyar aure.”

Shiru kawai Malam yai basa da bakin magana don yasan ko me zaiyi baza su bashi kudin ba kuma bai isa ma yace baban sumy ya basa ba tunda yasan halin da gidan sa yake ciki.

“Hmmm” kawai baba yace kafin ya kara mika musu hannu sukai musabaha ya wuce nashi gun.

Kallon baban sumy liman yai yace “amma yahuza kayi dabara da baka yadda ya tafi da kudin nn ba, ni kai na tunanin da nake knn wallahi taya za’a bassa da kudin don ba lallai ma ya bama uwar yarinyar ba.”

“Shiyasa liman dama ai tunda aka ban kudin naki yadda suje hannun sa don in suka shiga hannun sa baxai bayar ba.”

“Allah dai ya shirya sa,” ahaka suka wuce masallaci suna tattauna halin Malam Abubakar.


Waya tace tai kara, kallon ta nai naga sunan Habyby ya bayyana murmushi ne ya subuce min wanda yasa sumy dala min dundu a baya tana cewa “shegia mara kunya”.

Gantsarewa nai ina dariya don dukan ya shigeni, daukar wayar nai na sa a kunne.

“Salamu alaikum Habybyna”

“Waalaikumussalam Gimbiya ta kuma matata”

Gabana ne naji yai rassss jin abinda yace wanda har sai da na lumshe idanuna.

“Uhmmm” kawai na iya cewa.

Dariya yai yace “jikin ya fara sanyi ne sbd kin kusa shigowa fada ta, kar ki damu Gimbiya kike fah mulki zaki zuba ni kaina bawan kine”

Murmushi nai wanda ya bayyana fararen hakora na cike da nutsuwar da in har zan magana dashi take shigata nace “kai din sarki ne a wannan tsaftatacciyar fadar ni kuma Gimbiyar ka ba yadda za’ai na barka ka zama bawana snd kai din me tsada ne kuma Mijinaaaa Insha Allah.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button