NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Lumshe ido yai sbd yadda taja mijin sai da tsigar jikin sa ta tashi, “uhmm” kawai yace yana kokarin saita kansa????

“An sa ranar bikin fah wata 4 insha Allah bayan kin kammala waec da sati biyu zaki amsa sunan matata zaki zo mu rayu tare nida ke cike da kaunar juna”

Lumshe idanuna nai ina jin wasu hawaye na taruwar min wanda ni kaina bansan ko na mene ba.

Jin shirun danai yasa sa kiran sunana cikin wani sauti yace “Gimbiya ta naji kinyi shiru.”

“Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa ya bamu zaman lafia ya kade dukkan wani fitina.”

Ameen Gimbiya ta.
Haka yai ta min hira nikam duk jikina yai sanyi wata 4 fah ynxu nan da wata 4 xan bar mamanmu da muhd na tabbata ranar da ace inada saurin kuka da nayi shi yafi a kirga…..


Cike da nutsuwa yake fadin “kiyi hakuri Ummina komai mai wuce wane insha Allah kuma ki rage damuwa akaina ina cikin koshin lafia ki tambayi ma Khalifa.”

Wata kamilalliyar murya ce tace ina kokarin kwantar da hankalin nawa Boy amma na kasa jurewa tsawon shekara nawa bansa ka a ido ba kaima baka sani ba, ni nasan kokari kawai kake sbd baka san a nuna min gajiya war ka.

Lumshe idonsa yai yana shafa kwantacciyar sumarsa jin ta kirasa da boy, sunan da duk duniya ita kadai ke kiransa dashi da sauri ya bude idonsa jin wasu hawaye sun taho da gudu.

Uhmm Ummina insha Allah watarn zaki ga kamar hakan bai taba faruwa ba a garemu kaddarar muce ahaka Allah Ubangijin ya bamu ikon cinyewa.

Ameen boy Allah yai maka albarka ya kare ka daga sharrin mutum da Aljan, Allah ya daukaka ka ya dafa ma Boy.

Ameen Ummina Ameen ina gaishe da kanne na.

Insha Allah zan fada musu boy, ya gurin aikin naka komai yana tafiyya dai dai koh?

Alhamdulillah ummi komai yana tafiya gashi ynxu ina ta kara samun daukaka ba iya garejin mu nake aiki ba ynxu wasu suna zuwa suna daukata ina musu gyara suma.

Alhamdulillah boy Allah ya kara daukaka.

Ameen Ummina, haka sukayi ta hira wanda kana ji zaka san da kwai shakuwa mai karfi tsakanin su amma daga jin muryar su kasan dakwai miki a rayuwa su????

Bayan ya ajiye wayar hannu ya daga sama yana addua a ransa wanda hakan ya hanani jin mai yake cewa sai dai kawai ganin hawaye nai suna zuba a kan kyakyawar fuskar sa(My NOOR????)


Cike da kwarkwasa take takawa tasha riga da siket matsatsu sai dan fililin gyale data yane kan ta dashi, fuskar nn tasha makeup gashi kuma dama anyi bleaching anyi haske tayi kyau ba laifi kam

Horn din data ji a bayan tane yasa ta tsaya wa tana jiran taji ita ake ma ko kuwa Jin tsayuwar mutum tai daga bayan ta hakan yasa ta juyawa dan ganin waye………

Mrs A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
       Mrs A.M

Dedicated to Maryam Abdullah????????

Page 13

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Babban Mutum ne don zai kai shekara 40 zuwa 45 yasha manyan kaya sai gyara babbar rigar sa yake.

Kallon sa walida tai tun daga sama har kasa, ba laifi yana da dan kyan sa daidai gwargwado.

Cike da kwarewa gun yima yan mata magana yace “sannun yan mata barkan ki da hutawa.”

Murmushi tai tana gyara fuskar ta Allah ya sani ba daban jan kunnen da umma tai mata ba akan in har wani ya tsayar da ita kar tai hauka da ba abinda zai sata zunduma ihu don murna.

“Lafia qalau Allah lafia kuwa?” Ta fada tana kara gyara muryar ta don kar ta kwafsa.

“Lafia qalau yan mata da farko dai sunana Alhaji Bashir kuma na ganki ina son ki soyyaya kuma da aure fatan zan samu gunki koh.”

Wayyooo Allah kiris ya rage walida ta zube a cikin kwatar da ke gefen titin, cike da wani yanga da iyayi tace “Alh Bashir naji uzurin ka amma gaskia baxan iya kula ka ba sai kaje gun mahaifina ka nemi izinin sa.”

“Ahaf yan mata ai abinda nake so knn kar jiki komai ina ne gidan naku in yana nn ma ni ynxu xan je bana son abin ya dauk lokaci ma in har kin amince da ni.”

Motar sa suka shiga tana nuna masa gidan, ai kuwa sun ci sa’a suna zuwa suka ga baba zai fita masallaci.

Shigewa gida tai da gudu in da ta bar su suna magana.

Tana shiga gida ta fada dakin umma, a zaune ta same ta tana cin shinkafa da miya ga tsire nn a gaban ta tana yaga wanda Malam ne ya siyo mata.

Rungume umma tai tace “albishirin ki Umma”

“Goro fari kar yarinya ta farar mace mai farar aniya.”

Farrr tai da idon fa sannan ta labar tawa umma duk abinda ya faru ta dora da fadin “ynxu dai umma tare muka zo suna tsaye tare da Baba kuma yace baya son abin ya dau lokaci.”

Wata uwar guda umma ta saki ta mike tsaye tana kwaso shokii, itama walidan taya ta tai sukai ta tikar rawa.

Suna cikin haka baba ya shigo, zama yai kan kujerar umma yana dariya yace “zauna kiji Harira fitar yarinyar nn alkhairi ya jawo mana yau.”

Zama umma tai yana kallon baba.

Kudi ya fito dashi a aljihun sa yace “kinga wannan dubu 30 ne saurayin walida ya bani wai fa kyauta ya ban.”

Da sauri umma ta miko hannun zata wafta yasa baba saurin mayar wa aljihu yace “meye haka kuma ai sai ki tsaya kiji abinda ke faruwa koh”

Koma wa umma tai tana gyada kafa tana ayyanawa a ranta baxa ta yadda malam ya rike wannan uwar kudin ba shi kadai.

“Yace min gobe iyayen sa zasu zo a sa biki baya son bikin yai nisa amma na fada masa dama da bikin yar uwar ta za’ai kawai sai a hada ko ba haka ba.”

Da farko umma botsare wa tai ita wai baxa a ahada bikin yar ta dana hadiza ba amma data tuna yadda sukai da boko sai ta ce ta yadda kawai.

Raba kudin sukai gida biyu sannan ya fita sai murna yake.

Mu kuwa munsha habaici ranar da aka kawo kudin zance don dubu 100 aka kawo da goro, ranar umma yi tai kamar zatai hauka.

Mamanmu kuwa ko ajikin ta sai ma murna da ta ke taya ta sbd aurar da diyar ta zatai.

Nidai tunda aka sa ranar bikin nn Aunty take ban maganin sanyi ina sha sbd mamanmu kunya ta hana ta komai hakan yasa Aunty dagewa gun maganin sanyi.

Ai kuwa ina ganin amfani su don tunda na fara sha kullum ina hanyar bandaki ina fitsarar da shi.


Abuja

Ammi ce zaune a gaban Dada wacce take kan kujera tana taunar kashin kaza.

Daga bayan Ammi kuma saudat da salma ne zaune suna solving maths kasancewar an kusa fara waec.

Kallon Ammj dada tai tana taunar kashin ta tace “hala baki ji abinda nake ce miki bane Halimatu a’a.”

Kara sunkuyar da kai Ammi tai tace “dada baxan iya bane ko ba komai ke a matsayin uwa na dauke ki kuma gasu Salma in tafi in barsu gun wa.”

Tafa hannu dada tai tace “cemiki nai dana ki tafi Halimatu, guduwa fa nace kiyi kawai ki kwashe yaran kibi dare ki gudu baxan damu ba tunda ni nasan inda kike shi kuma madun don ubansa in kika gudu sai muga zai damu ko baxai damu ba.”

Hararar ta saudat tai sannan ta kalli salma wacce ita ma ita take kalla, a hankali tace “twinny anya kuma dada bata da tabun hankali?”

kafin salma tai magana sunga dada ta dunguro daga kan kujera, a zabure ta mike tana gyara daurin zanin ta da yake shirin faduwa.

Dora hannun tai aka ta saki wani kuka mai ihu kice da tashin hankali ta nuna Ammi tace “Halimatu kina duniya kina zaune yar ki ke cemin inada tabin hankali ni halimatu nii ta fada tana dukan kirjinta.”

Da sauri Ammi ta mike matso gun dada, cike da tashin hankali itama ta hau bawa dada hakuri wacce inaaa sai kuka take tana dafe kanta da hannayen ta.

Ganin taki shiru yasa Saudat data mike tana shirin fita sbd kallon da Ammi take mata cewa “nidai dada kiyi hakuri don Allah ba dake nake bafa littafin da muke dubawa ne teacher dinmu yace mu gama solving questions 50 kafin gobe shine nake cewa twinny anya yana da hankali kuwa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button