NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

   Written by
     Mrs AM

Page 1

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 Ke Maryo baza kiyi maza ki gama ba don wulakanci wanke wanke ne tun dazu kina zaune amma kin kasa bada himma kiyi maza ki gama sbd iskanci, hmmm ko da yake ba laifin ki bane na wannan uwar taki ce. A fusace na juyo ina kallon umman, na tsani naji ana zagar min uwa shiyasa naji raina ya baci kara hade girar sama da ta kasa nai nace wai ke umma meyasa kike haka ne tsakani da Allah sai kiyi ta zagar min uwa, to wallahi wanke wanken ma baxan yiba. 

Mai nake ji haka, ke uwata meyasa baki da kunya ne wai don ubanki ba babarki bace kike gaya mata magana haka. Ko kallon inda yake ban ba nace amma baba kana ji fah tana zagin mamanmu kuma fa wanke wanken yawa ne dashi tun na jiya da daddare su Zainabu basu yi ba sai da na dawo daga makaranta sannan ta sani fah, gashi time din islamiyya ya kusa.
Toh don ubanki sai kinyi mata cewar baba, Umma ce tace yauwa malam dama nasan ai ba sa hannun ka a lalacewar wannan yarinyar uwarta ce take kara bata ta kuma tana nuna mata rashin girman ka, harararta nai sannan na figi hijab dina dake kan igiyar shanya na fita da sauri don ma kar baba yace na dawo nai ma umma wanke wanken don na rantse tun da ta zagar min uwa baxan yi ba.

Binta sukai da kallo malam ya daga murya yace kee hadiza, mama da sauri ta fito tace gani malam, kallonta yai cike da tsana yace wai meyasa kika rainani ne don banda kima da mutumci a idon ki kinaji wannan yarinyar tana ma Ummansu rashin kunya amma ko fito ki mata fada koh? Sunkuyar dakai Mama kawai tai tace malam kayi hakuri sallah nake ne, tsaki yaje sannan ya kalli Umma yace kiyi hakuri kinji kinsan halin Uwata bata ji wallahi sai hakuri kawai.
Kallonsa Umma tai tana jin wani bakin ciki a ranta ta tsani yadda malam baya iya ma Maryo fada sosai kamar wanda yake jin tsoron ta. Tsaki tai kawai ta juya ta tafi madafa tana maganganu kasa kasa, juyawa mama tai ta koma daki tana ma Maryo addua aranta.

Tunda na fiti na kara hade raina sam bana son raini sbd unguwar tamu samari masu zaman banxa suna da yawa wanda basa aikin komai sai sa’ido. Gidan dake kallon gidan mu nashiga shima gidan su kawata ne don duk duniya ita kadai ce kawata ita kadai ke jure halina, gidan nasu sunfi gidanmu sbd du baban su malami a secondary school don haka sunfi mu ruin asiri, kuma su babarsu ce kawai bata da kishiya gasu basu da yawa.
Tura kofar gidan nai ina sallama wacce na tabbata ba wanda ya jiyo ni sbd zauren su yana da dan tsayi, wucewa nai cikin tafiya ta wacce mutane suke cewa yanga nake yi nayi cikin gidan. Da Sumayya na fara cin karo tana gyara wake, dagowa tai da sauri jin murya ta tace masoyiya kece da rana tsaka, harararta nai nace in bakiji dadi ba in koma mana, yi hakuri kinji masoyiya zo zauna. Zama nai ina sa hannu cikin gyaran waken ina tayata, kallona tai tace uhm yan miskilancin ne knn, ko kallonta banba na dauke farantin hannun ta ina gyara waken don Allah yamin zafin nama nan danan na gama gyarawa na ajiye mata farantin a gabanta. Kallontai tace masoyiya me ya bata miki rai ne wai naga kina ta wani hade rai? batare da na kalle ta ba nace in kin gama tashi mutafi islamiyya kinsan Malam Nasiru zai karbi hadda yau ko baki iya bne? Murmushi tai tace na iya man ina tare da malama kanar ki, girgiza kai kawai nai ina murmushi. Maman suce ta fito daga dakinta tace Maryo ashe kin shigo, eh Aunty na ban dade da shigowa ba islamiyya na biyo mata mu tafi, to masha Allah ya jikin maman dazu naso na leka na mata sannu amma sai ban sanu damar zuwa ba, ahankali nace da sauki ai Aunty yanayin fuskata na chanjawa tunawa da nai yadda mamanmu take fama da zazzabi mai zafi amma babanmu ko biyar bai ba yarba don a kaita chemist sai a kudin alawar madarar da nake ta shiyarwa na kaita chemist da dadddare, Hmmm kawai nace.

Fito wa mukai daga gidan su muma tafe Sumayya na ban labarin saurayinta Umar wanda muke sa ran shi zata aura , kamar daga sama naji an bangajeni an wuce da karfi har saida na kusa faduwa, a fusace na jiyi don ganin wani mai gangancin ne wannan …….

Wannan shine book dina na biyu ina fatan zai samu karbuwa

Comments nd share plz

Mrs AM

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

  Written by
    Mrs Am

Page 2

Muhd na gani wanda shima da sauri ya juyo aikuwa ganin nice yasa kawai ya fashe da kuka ya daga hannu sama yana cewa Yaya don girman Allah kiyi hakuri wallahi nuhu ne ya biyoni akan.

Kallonsa nai kawai don wallahi da ba muhd bane sai na kartama kowaye rashin m, hade rai nai nace mai kaima nuhun ya biyoka.

Kafin ya ban amsa munji magamar Nuhu daga bayanmu yana cewa baban kune mana ya aiko sa wai na basa bashin shinkafa rabin kwano zai biyani daga baya, shine nace yaje yace masa baxan bayar ba.
Ina binsa yafi dubu biyar to dan iska ne ni da zan… kasa karasawa yai ganin na zuba masa idona masu kama dana mage don colour din kwayar idona light blue ce ga idon kuma tubarkallah a lumshe suke.

Kallona ya tsaya yi sannu a hankali yace gaskia nidai Maryo ki daina kallo na haba mutum sai yana son ya fadi abu sai ki tsare shi da wadannan idanuwan naki kamar na mage.

Tubarkallah Masha Allah Muhd ya fada, kallon Nuhu nai nace ima jinka.

Cewa nai ace masa baxan sake basa bashi ba har sai ya biyani duk bashin da nake masa, shine wannan yaron fa ya fara min rashin kunya ni kuma na biyo sa na saita masa hankali kin gane ai.

Hararar sa nai kawai na juya kan muhd na hade rai nace kai tarbiyyar da mamanmu tai mana kenan ta yima manya rashin kunya.
Kwabe fuska yai yace kiyi hakuri Yaya baxan sake ba wallahi wannan ma tsautsayi ne kinji yayata ta kaina.
Juyar da fuska ta nai nace basa hakuri, da sauri yace Yy Nuhu kayi hakuri baxan sake ba kaji.

Murmushi Nuhu yai yace gaskia Maryo kina birge… wani kallo nai masa dayasa sa rufe bakinsa a ransa yana cewa wannan yarinyar anyi masifaffiya ni bantaba ganin miskila masifaffe kamar taba.

Jan hannun Sumayya nai da take ta dariya kasa kasa mu ka tafi ina cema Muhd in ya sake naga bai je islamiyya ba nida shi ne.
Hira muka cigana dayi wanda duk rabin hirar sumy ce ke yinta nidai nawa ji, a haka muka isa islamiyyar muka tarar har an fara karbar hardar muma muka zauna kowa yana tilawar haddar sa a ransa don kar azo karba kayi kuskure.

Karfe 6:05 muka fito daga makarntar nida Sumy tare da ragowar dalibai don an tashi.
Har munyi gaba na kalli Sumy nace zo ki rakani don Allah na taho dasu Zainab, tohm tace min muka koma makarantar don taho da kannena duk da ba daki daya muke dasu ba amma bana bari na barsu sbd yawo suke tafiya.

A cikin kawayen su na gano su suna ta wasa suna dariya aikuwa suna ganina suka taho da gudu sbd sun san halina????

Rike hannun Zainab nai ita kuma Sumy ta riko Minal da Hafsa muka taho tana cigaba da ban labarin project din da aka bamu a school.

A kofar gidan mu muka tsaya kallonta ta nai ina jin tana cewa ku gaida min Mamanmu don Allah masoyiya zan shigo bayan isha’i insha Allah.

Tohm kawai nace muka shige gida dasu minal.
Muna shiga na shige dakin mu da sauri don naga labilen falon mu an daga shi ni kuma bana son naga ana dagawa sbd sauro.

Da sauri na shiga da sallama a bakina, amsawa sukai mamanmuce da Muhd a zaune akan ledar falon mu suna cin abinci a kwano daya, wanda dana mun saba cin abinci a plate daya ko dan sbd abincin ya ishe mu.

Zama nai kusa da mamanmu ina cewa washh, mamanmu na gaji sosai wallahi bakiji bayana ba kamar zaj balle gashi yunwa nake ji.

Ko kallona batai ba tace ynxu Maryo kin fiso kiyi ta jamin fada agun baban ku koh, ynxu don Umma ta saki abu sai ki kiyi sbd bakya jin magana?

Hade rai nai kawai nace mamanmu kiyi hakuri baxan sake ba.
Hmm ke kuma Maryo sau nawa kima cewa haka amma kina sake wa?.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button