NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaune take a falon tana karkade kafaunta, babbar macece wacce a shekaru baxa ta wuce shekara 40 ba tana da kiba sosai kuma gajera ce fuksar nn tata da wuyan ta sun hade sbd kiba
Jikinta zuwa fuskar ta tsabar farin su har yellow yellow take kana kallon ta kasan allura ake mata.

Falon ya gaji da haduwa kujera set uku ne a palourn sai kamshi ke tashi na tutaren wutan yan maiduguri.

Wayar ta ta dauka wacce aka kira ta, cikin yanga take magana kamar bata girma ba
Ohk darling gani nn zuwa hadda coffee ma bara na taho ma dashi

Daga dayan bangaren ne dai banji mai aka ceba amma naga ta mike tana kallon katon agogon dake manne a palourn, karfe 11 saura da sauri ta mike tana zura wasu lafiyayyun flat shoe a kafanta dasuka sha ado da nail paint.

Rigace a jikinta iya gwiwa wacce ta matse ta daga sama sai ta dan bude kadan daga kasa gun kwankwason ta

Wata kofa ta shiga inda nake kyautaya zaton kitchen ne batai minti goma ba ta fito tana tura keken zuba abinci har ta nufi wata kofa ta shige ta maida kofar ta rufe.

Wai kai Noor meyasa baza ka daina abinda kake bane, don girman Allah ynxu menene a ciki don na baka kyautar kudi sai ka dinga kin karba kana kallon halin da kake ciki fah.
Ynxu ko kaya na siyo ma na baka ba karba kake ba.

Hade rai a ahankali ya bude bakinsa kamar baya so yace……..

Comments nd share plz

Mrs A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

   Written by 
       Mrs A.M 

Page 6

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

  Meyasa ka kasa ganewa ne wai Khalifa, hmm nace ma ina so na gina kaina da kaina bana son ganin na dogara da wani.

Shiru kawai wanda aka kira da khalifa yai yana kallon abokin nasa, ya rasa wata iriyar zuciya ce da shi kudi gashi nn shi yana da su amma yaki yadda ya taimake sa.

Kallon tsakar gidan khalifa yai yana girgiza kansa, sannan ya jiyo inda NOOR ke zaune ya hade girar sama data kasa don ma kar khalifa ya kawo masa raini????

Shiru dukkan su sukai kafin khalifa ya mike yai masa sallama ya tafi don yana son kafi ya koma yadan taimakawa aminin nasa tayanda shi baxai san ya taimake sa ba.

Bayan tafiyar khalifa dakin sa ya bude ya shiga, zama yai gefen katifar sa ya tsura wa durowar sa kayansa ido ya shiga tunanin rayuwa…


Da asuba bayan mun idar da sallah na shiga wanka, a gurguje na fito na shiga shirya wa don shidda har tayi gashi makarantar mu da dan nisa kuma a kafa muke zuwa.
Bayan na shirya na janyo murfin durowar kayan mu na ajiye a agefe, a hankali na sa hannu na kasan kayanmu na janyo wata tsohuwar pos nita na bude.
Zama nai gefen gadon mu ina irga kudin dubu hude ne da dari bakwai, murmushi nai cikin jin dadi na dauki dubu 3 da dari bakwai din nasa a cikin socks dina sannan na maida ragowar kudin cikin pos din na ajiye inda na dauko.

Fitowa nai palourn jin muryar Sumy, murmushi nai don nasan biyo min tai.
Ina fitowa kuwa na ganta tsaye itama cikin uniform dinta irin nawa doguwar riga ce dark grean sai wandon da hijab din light grean da dan kwali dark grean.

Zama nai ina ajiye jakata da hijab dina a gefena nace sannu da zuwa habibty
Murmushi tai tana zama gefena tace yi sauri dai wallahi kinga mun kusa makara gashi yau Thursday za’a yi wannan assembly(kasan cewar mu Mondays nd Thursdays muke assembly)

Da sauri nake shan kunu na wanda yaji sugar kadan nasan sugar dinma mamanmu ce ta sa mna don umma bata bamu kunu da sugar acewar ta ai ina sana’a don haka na fitar da kudi na siya mana .
Mikewa mukai na riko hannun muhd ina kallon mamanmu dake tamana addua.
Mamanmu in mun tashi zan biya kasuwa na siyo madara sa sigari kinga sun kusa karewa

Kallona tai kawai sannan tace sai kun dawo amma ku tabbatar kun dawo da wuri kar ku kai 4

Da sauri nace Insha Allah mamanmu ai nida Sumy ma zamuje kuma baxa mu dade ba.
Allah ya kiyaye ya bada sa’a ku yi adduar fita daga gida kar ku manta kunji.

Atare muka hada baki gun cewa insha Allah.

Muna fitowa daga dakinmu muka ga Umma ita da iyalanta suna zaune akan tabarma suna shan kunu da kosai, nidai cikiciki na gaishe ta inda ta dauke kai kuwa kamar bada ita nake ba.

Ko kara kallonta ban ba naja hannun muhd muka fita.
A soro mukayi cikibus da Faisal zai shiga shima cikin shirinsa na makaranta da bakar leda a hannun sa.
Gaisawa mukai cikin sakin fuska sannan ya kalleni yace har zaku tafi.
Kallonsa nai na gyalla masa harara nace zama zamuyi ba tafiya ba.

Dariya yai yace gaskia kanwata kin rainani da yawa wallahi

Wace kanwar taka kadai neme ta amma bani ba kaima ka sani yaro.
Sumy ce ta kashe mana rigigar mu gun cewa kunga don Allah kuyi hakuri in mun dawo daga makaranta zai ku cigaba don tunda kuka fara zaku iya kaiwa dare baku gama ba

Dariya faisal yai yana miko min hannu yace ban gullisuwa ta don jiya har mafarkin ta nai.

Dariya nai ina bude jaka ta ta miko masa ledar dana zuwa masa gullisuwar da alawar madara, sallama mukai masa muka tafi.

Da dan sauri muke tafiya bayan mun shiga gidan su Sumy na fada ma Aunty ina son ta rakani kasuwa na siyo kayan alawar madara ta.

Bayan mun isa makaranta an gama assembly muka tafi class dinmu ss 2 B.

Kafin a tashi tuni an siye alawar madarar da gullisuwar har ma ana neman karin gullisuwar, cinikin 1000 nai don dama gullisuwar 500 ce alawar madarar 500.

Cikin farin ciki muka fito bayan an tashi Sumy na rike da hannun muhd ina gefen ta.
Cikin jin dadi tace masoyiya kinga gullisuwar nn tayi farin jini gaskia ya kamata gobe kiyi ta dubu daya in yaso ita alawar madarar kiyi ta dari bakwai ko dari takwas, kinga fah har aka tashi ana ta zuwa siya amma ta kare.

Cikin murya ta mai cike da nutsuwa nace eh insha Allah kuma kinga fah in mun koma yan unguwa zasu dinga zuwa siya.

Eh mn kuyi sauri dai kunga mamanmu tace kar mu dade cewar Sumy.

Kallon sumy nai nace masoyiya kin san me, girgiza min kai tai tace a’a

Murmushi nai nace alkawarin Allah ya tabbata yau zan siya wa mamanmu waya.

Da sauri muhd ya fincike hannun sa ana sumy ya rike nawa yace yaya da gaske kike muma zaki siyawa mamanmu waya ta dinga kiran su hajjo(kakarmu wacce ta haifi mamanmu)

Murmushi nai masa nace eh mn.
Sumy ma cikin farin ciki ta riko hannu na tace nayi murna sosai wallahi masoyiya nasan mamanmu zata ji dadi amma kin fada mata ne

Girgiza mata nai nace ban fada mata ba bata ma son zan siya mata ba kawai ina son nai mata surprise ne.

Haka muke tafiya muna tattau nawa yawancin maganar akan karatun mune sbd muna tare da muhd baxai yi mu yi wasu zantukan ba????

Gefe daya kuma na zuciyata tunanin irin murnar da mamanmu zatai nake don rabon ta da waya anfi shekara daya tunda ta siyar da wayar waccen sallar tayi amfani da kudin kafin na fara sana’a

Shiyasa in har tana son tayi waya da mutanen gidan su sai dai ta wayar Aunty.

Kasuwar dake gaba da makarantar mu muka je wacce anan nake siyan komai dazanyi amfani dashi.
Madarar dubu daya na siya sai kuma na siyo sugar na dari biyar, kudina ya rage saura dubu uku da dari biyu.

Adaidaita muka hau bayan munyi ciki zai kamu farm centre.

Muna sauka a farm centre na kara take fuska ta sbd ganin duk maza ne a kasuwar daidai kune mata.

Cikin kasuwar muka nufa shagon farko dake kallon mu nuka shiga da sallama a bakinmu

Mai shagon amsa mana sallamar yai yana cewa bismillah
Shigowa mukai sosai muka tsaya a dan nesa da shi sannan na fada masa abinda muke so
Wayoyin ya dauko mana yana fada mana kudaden su, wata itel na gani blue black tayi min kyau duk da second hand ce amma daga gani bata ji jiki ba don a haka ma kamar sabuwa take.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button