NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri Aunty ta mike tace “kinga nima fah dama na shirya jira nake kawai a xo kirana bara nasa mayafina.”

Daki ta shiga cikin minti biyu ta fito ta chanja kaya tasa mayafinta babba tunda kai ta lullube jikinta.

Fita sukai sumy ta bisu da Allah ya kiyaye.

Suna fita ta jiyo ta kalle ni tace “Masoyiya ji nake kamar na bisu wallahi nima na gano gidan da zaki zauna.”

Kallonta nai nace “habibty takya jin tausayina koh, kina gani aure baba ya dora min da wanda ban sani ba shima bai sani ba.”

Dafa ni tai tace “kiyi hakuri masoyiya insha Allah komai zai zo da sauki kuma wanda aka aura miki sai yama fi wannan banxan mahmud din komai komai kuma zakice na fada miki”(our Noor????♀️????♀️????♀️????♀️).

Murmushi nai kawai amma ba wai don na yarda da zancen ta ba nidai nasan baxan sake yadda na bude ma wani zuciya ta, ban taba soyayya ba kuma lokacin dana fara na sakankance na bude ma mahmud zuciya ta shikuma ya yaudare ni “hmmm”.

Su Hajjo kuwa sun lafe a mota sunyi shiru abinsu suna shan AC, don inna ma har ta fara gyangyadi.

Aunty ce ta katse shirun da cema Khalifa, “bawan Allah ya sunan kane.”

Dan juyowa Khalifa yai yace “sunana Yusuf amma Khalifa ake cemin.”

Hajjo ce ta cafe da “aah kace mai babban suna ne ashe mai gidana ne ma.”

Dariya yai yace “uwar gida kece a baya ban sani ba.”

Duka motar suka sa dariya, cikin dattako hajjo tace “ya sunan jikan nawa.”

Murmushi yai ya gane Noor take nufi hakan yasa sa cewa “sunansa Muhammad Noor”

“Masha Allah Allah ya basu zaman lafia ya kade fitina” inji Inna

“Ameen ya rabbi suka ansa.”

Gwaggwo Hafsa ce tace “kar ka gaji damu Khalifa kaga diyar mu aka basa dole mu tambayi halayyar sa da sana’ar sa in ba damuwa ka fada mana”.

Shiru Khalifa yai na yan sakanni kafin yace “Sunansa Muhammad Noor Muhammad yana da shekarar sa 33 yana da hankali da nutsuwa baya shaye shaye baya neman mata basa da wani mummunan hali kuma yana da ilimin addina dana zamani dai dai gwargwado, gidan sa nakan sane inda zasu zauna da ita Maryam din yana sana’ar gyaran mota a gareji.

Dan shiru yai sannan ya ciga “duk duniya bayan mahaifiyar sa nafi kowa sanin Noor kuma bawai na fadi dukkan wannan yabon akan sa don ya a dan uwa na bane a’a duk wanda ya zauna da Noor zai fuskanci wa’yannan kyawawan dabi’unsa.”

Murmushi Aunty tai don ita taji ya kwanta mata tace t”oh Alhamdulillah Allah ya kade fitina a zamanta kewar su”

“Ameen ya Hayyu ya Qayyum” suka fada gaba dayan su.

Haka sukai ta hira tsakanin su har suka iso unguwar sharada dake kano.

A kofar gidan yai parkin yace su fito ga gidan.

Duk fitowa sukai suna kallon yadda gidan yasha fenti abin sha’awa.

Bude gidan yai suka shiga nan ya nuna musu dakin Noor yace banda nn zasu shiga dakin mai gidan ne kuma yasa komai nasa a ciki.

Haka suka shiga palourn da yasha gyara abin sai san barka ko ina sun shiga sai sa albarka suke zuciyar su fess sbd su a ganin su wannan abin farin ciki ne daidai talaka gida yayi kyau.

Ko ina tsaf tsaf, bayan ya maida su gida zama sukai a dakin mamanmu suna shawarar abinda ya kamata su sake siya.

Kallonsu Aunty tai tace “kinga Mamanmu da kwai 70k a gurin ki da kika ban na ajiye fa kwai sadakinta 20k ga kudin dasu mahmud suka kawo tunda kawun yace a siya ma Maryon katifa shidai bazai karba ba kinga kudin ya kama 140k ga kuma kudin gudun mawar da aka hada 20k duk sun kama 160k knn gashi baban su(tana nufin baban su sumy) ya bada 20k shima duk ya kama 180k.”

Kallon Aunty inna tai tace “to ynxu mai dame za’a siya amma nidai ina ganin dakin nn kamar gado baxai shiga bako?”

“Eh inna nima naga kawai sai mu siya katifa da wardrobe mai hudu sai mudubi da kuma durowar gefen gado koh ya kuka ce.”

“Haka ne Gwaggwo Zainab nima tunanin da nake knn wallahi” Gwaggwo Hafsa ta fada tana cire tagumin da tai.

Aunty ce ta cigaba “sai a siyi kujera kinga da carpet sai mu siya tabarma guda 3 haka don bamu siya ba.
Naga mai gidan nata har Fridge ya siya mata kinga sai mu siya mata mu kuma kaya masu kyau da labulaye.”

Koda Aunty ta dawo nan ta zaunar damu tana koda mana gidan nidai ban wani damu na tsaya na ji ba sbd wannan baya gabana.

Washe gari kuwa da Aunty da Gwaggwo Zainab da Gwaggwo Hafsa ne suka shiga kasuwar gandu gurin yan gadaje.
Nan suka siyo min duk abinda ya dace kamar yadda suka tsara.

Kujera masu saukin kudi second hand suka samo dark brown tunda sunga kalar kayan fentin light brown ne 70k suka samo kujerun kujerun sunyi kyau set. Sai kuma kayan gadon suma dark brown sun siyo komai na set din gado shima 40k sbd masu kyau ne kamar sababo banda gadon amma sai katifa kuma 6 by 6 ita ma a 30k suka siya sbd second ce sai aka musu ledar katifa suka siyi pillow biyu 2k.

Duka kudin ya kama saura 38k.
Anan suka bada amin labulaye na window 4 sbd daki window daya ne falo ma window daya ne sai kuma za’a sa labulayen a kofar daki da kofar falo.

Sauran kudin suka siyo zannuwan gado yan 2k guda 4 sai kuma bargo na 15k. Duka kudin ya rage saura 7k da ragowar kudin suka yi shatar akori kura aka sa kayan suka nufi gidan maryo.

Dama sunyi magana da khalifa, suna zuwa ya fito ya same su suka shiga da masu gyara kayan.

Anan suka tarar da TV 32 inch ga satellite nn ana sawa, Aunty ce ta kasa hakuri ta tambayi Khalifa wannan tvn wa ya siyo.

Cikin lallashi da girmamawa yace ma Aunty shi ya siyo amma don Allah kar su bari Noor yasan shi ya siya in ya sani sai ya sashi cire wa.

Hakan ya kara ma su Aunty kara ganin kimar Noor da khalifan.

Yana gidan aka gama gyara komai aka kafa labulaye tuni gida ya dau kamshi sai kamshin kaya yake yayi kyau don sosai sunyi kokari.

Bayan an gama har zasu fita aka shigo da TV stand da carpet wannan ma aikin Khalifa ne.

Bayan sun gama ya kaisu gida yana ta musu godia akan karbar kayan daya basu da sukai.

Haka ya tafi yana adduar Allah ya sanya wa auren albarka sbd daga ganin yadda su Aunty suke yana saran itama Maryon ta kasance haka.

Lokacin da su Aunty suka fada wa su inna yadda abin ya faru nan suka hau farin ciki sannan sukai gobe zasu je dasu hajjon in yaso sai suma suga gida a kuma jera kayan kitchen.

Haka akaita shirye shiryen har ya kasance gobe za’a kaini gidan wanda ake cewa mijina ne…….

Comments nd share plz

Mrs A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
        Mrs AM 

Page 18

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Kallon Aunty nai dake tsaye akaina hannun ta dauke da comb da kifiya.

Marairaice wa nai nace “Aunty dan Allah kiyi hakuri kinga kitson fa bai wani tsufa ba kuma da yawa haka zan zauna na tsefe shi.”

Harara ta zanga min tace “cewa nai ki tsefe da kanki nida Sumayya zamu tsefe miki.”

Har na bude baki zan magana tace “zaki min shiru ko kuwa mutsu zaki tsaya kina min?.”

Girgiza kai na nai inam gyara zamana, ina ji ina gani Aunty da sumy suka hadu suna tsefe kannan, kamar nai kuka haka na zauna.

Bayan sun gama tsefe min kan taja ni gaban fanfon su ta wanke min kan tass duk da ba datti amma haka ta wanke da shampoo da conditioner din sumy.

Muna zaune tana goge min kaina akai sallama, dagowa nai ina amsawa naga mai lalle ce tazo da sauri na juya ina kallon Aunty.
Dauke kai tai ta maida kanta gun mai lallen tace “yauwa rabi’a yi maza ki mata mai kyau hannu da kafa tunda naga bakin ya fita sauran kadan ya rage shi kuma sai an lura ma sosai za’a gani koh?.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button