NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Jin abinda dady yace yasa jikin sa sanyi girgiza kansa yai yace “nagode sosai Daddy Allah ya saka da alkhairi ya kara budi.”

Cikin farin ciki ya amsa da “Ameen son” sannan suka fita shida khalifa.

Zama yai a dakinsa yana zabga tagumi ko kadan bai taba kawowa babansa zai masa abu irin haka ba amma kuma tunda ya iya……… ai wannan ba wani abu bane ma da zai damu don yai masa shiba.

Karar wayar sa ce ya dawo dashi daga tunanin da ya tafi.

Xaro ta yai ganin sunan Ummi akan screen din yasa sa daukar wayar ya kara akunne.

“Assalamu alaikum Ummina”

“Waalaikumussalam boy, y kk ya komai da komai.”

“Alhamdulillah ummi ina wuni”

“Lafia qalau boy.”
Jin yayi shiru yasa ta cigaba wa “kayi hakuri boy komai mai wuce wa ne kalar taka kaddarar kenan insha Allah kuma zaka cinye ta cigaba tai da masa nasiha har saida taji yana sauke ajiyar zuciya sannan ta ce kuma ka rike min amanar sirikata don ina ji ajikina ita din haske ce a rayuwar mu Allah yai ma rayuwar auren ku albarka.”

Shidai bai amsa mata ba sai ita ce tace “Ameen.”

A ranar aka fara gyara gidan don Daddy kudi ya sakar ma masu gyaran yace so yake a kwana biyu a gama shiyasa nan da nan suka fara aikinsu.

Da kansa daddy ya shiga gidan inna yai mata bayanin an daura wa Noor aure kuma insha Allah ranar asabar amaryar zata tare.

Itadai inna taiyi addua amma yana fita ta fara yan fade faden ta.


Ni kuwa ina can ina aikin kuka sai da aka kira magriba sannan Aunty tazo tasa ni nayi sallah zama tai aguna har akai isha nai sannan ta ban magani nasha na kwanta.

Acikin gidan mu kuwa Umma masu kidan kwarya ta kawo aka shiga shagali da habaice habaice sai murna take.

Ji take ba na biyunta a farin ciki yau.

Bama da aka zo daukar taga motoci har biyar tuni ta hau rawa da guda.

Haka aka kai walida gidan ta dake unguwar rijiyar zaki gidane mai kyau don sama da kasa ne dakuna hudu palour biyu.

A daya daga cikin dakin dake sama aka ajiye ta sannan aka tafi aka barta.

Lokacin da yan kai amarya suka koma suka bama umma labarin dukiyar da aka zuba a gidan walida ji tai kamar ta koma gida itama amma tunda dai zata dinga zuwa ai ba komai.


Bangaren walida kuwa bayan kowa ya tafi mikewa tai ta bude yar jakar ta da aka hado mata kayan ta aciki, wani kullin magani da kwalli ta dauko.

Bude maganin tai ta shiga bandaki ta barbada a kasan ta sannan ta fito ta zizira kwallin.

Tana ajiye wa taji an bude kofar dakin, ganin wanda ya shigo yasa ta sunkuyar da kai cike da shauki don ba karamin kayan mata su umma su bata ba.

Zama yi gefen ta yace “amarya bakya lefi ko kin kashe dan masu gida.”

Farr tai da idonta tana janye gyalen ta tace “hakkun haka maganar ka take,” yar dariya yai ya janyo ledar daya shigo da ita ya bude nama ne mai romo romo yasha hadi da kayan su tumatir.

Miko mata ledar yai gaban ta yace “bismillah amarya fara da wannan kafin kaza ta biyo baya kinga bashi da wani yawa..”

Ci ta fara da sauri ba bismillah ba komai, sai da ta gama ci tsaf sannan taji kanta na sara mata anan ta zube cikin fitar hayyaci………..


Washe gari da kyar na iya tashi sbd yadda kaina yake min ciwo gashi bana wani jin karfi a jikina duk jikina ciwo yake.

Sallah nai sannan na koma dakin sumy na kwanta ka gado.

Waya ta ta miko min tace “gashi masoyiya”

Kallon hannun ta nai nace “bana so ki rike kawai.”

Daga bakin kofar naji muryar Aunty tana cewa “baxa ayi hakaba ke Sumayya anjima kije farm centre ki bada wannan wayar a chanja mata wata in kika ki karba da wacce zamu dinga waya in aka kaiki gidan mijin?”

“Shikenan kuwa Aunty kinga in an siyar da wannan din ai bata ganta ba balle ranta ya baci koh masoyiya?”

Nidai ban kulata ba na juya nace “in kinje ki siyo min ko wacce amma banda Samsung”(me kuma company waya ta yai miki????????)

Haka kuwa akayi da yamma sumy taje kasuwa ta siyar da waccen tawa ta siyo iPhone 6+ a gun wanda ta siyar da wayar ta siya iPhone din hakan yasa ta tsaya ta basa iPhone din ya min transfer din komai nawa ita kuma ta min copying numbers din waya ta ban da ta mahmud ta karya sim din.

Sabon sim ta siya min da cases guda biyu masu kyau na yan mata.

Lokacin data kawo min wayar sai naji ina sonta sbd tayi kyau kalar golden.

Agidan su sumy nake zamana har bayan kwana biyu da daurin auren don banyi kuskuren ko lekawa gidan mu ba…


Cikin kwana biyun nn tuni an gama gyara gidan yayi kyau an chanja kofa an ma gidan fentin dark brown dakunan kuma aka musu light brown.

An chanja kofofin gidan gaba daya ansa ta zamani.

Gidane mai kyau dan daidai cikin rufin asiri, kitchen din gidan yana kallon kofar dakin Noor shima ansa cabinet masu kyau kuma kitchen ne mai dan girma har fridge mai hade da freezer dady yasa a kitchen din.

Daga hannun daman gefen kitchen din kuwa kofar toilet ne, shima ban dakin an chanja komai na ciki ansa toilet sit da sink ga shower an sa kasan shi yasa tiles.

Cikin daki da palourn maryo ma an gyara sunsha tiles da fankoki irin kananun fankokin nn na sama masu gudu ga bulbs abin dai sai san barka ko ina yayi kyau.

Tsakar gida ma yasha tiles gashi Daddy yasa solar agidan.

Duk kuncin Noor sai da aka gyara masa shima dakinsa aka masa fenti aka chanja masa bulb da fanka.

Yau Khalifa yai zai je ya dauko yan uwan Maryo suzo zuga gida sbd susan abinda ya kamata suyi hakan yasa tun da asuba Noor ya kulle kofar dakin sa da mukulli ya fita…..

Comments nd share plz

Mrs A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
        Mrs A.M

Page 17

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Karfe biyu na rana tai ma Khalifa a kofar gidan su Maryo, yana zuwa ya dannawa baba waya dama kuma sunyi dashi zai zo yau ya dauke su suje suga gida.

Fitowa baba yai ya mika ma Khalifa hannu dake gaida sa.

Cikin farin ciki baba yace “bara na shiga ciki na fada musu suzo su tafi.”
Bai tsaya jin amsar Khalifa ba ya shiga gidan, dakin mamanmu ya nufa yana zuwa ya sane su a zaune hajjo, inna, Gwaggwo Zainab sai kuma kanwar inna Gwaggwo hafsa dama duk suna nan basu tafi sunce sai sunkai maryo da kansu sunga mazaunin ta.

Gaishe su yai wanda aciki ciki suka ansa hajjo ce kawai ta ansa masa ba yabo ba fallasa, hakan da ya gani ne yasa sa ce musu kanin mijin maryon ne yazo kaisu gidan nata su gani.

Ba wanda yai masa magana sai mike sukai dukkansu banda mamanmu suka fito dama a shirye suke kowa yasha Hijabin sa.

Suna fitowa Gwaggwo hafsa ta nufi gidan Aunty don ta kirawo ta.

Muna zaune a tsakar gidan ni da Aunty da sumy muna hira wanda yawancin hirar duk su sukeyi nidai nawa ji nai, sbd wannan abinda ya faru ba karamin girgiza min zuciya yai ba duk yadda nake so na rage zafin abin hakan ya gagara.

Duk na kara komawa wata masifaffiya abu kadan sumy zata min na hau ta da masifa hakan da Aunty ta fahimta ne yasa ta jawa sumy kunne akan ta daina damuna.

Da sallama Gwaggwo hafsa ta shigo, amsa mata mukai tana karasowa muka hada baki nida sumy wajen cemata “ina wuni”

“Lafia qalau aminan juna ya kuke”

“Alhamdulillah Gwaggwo”

“Kallona tai tace ya jikin naki maryo ba inda ke miki ciwo ynxu koh?”

Dan murmushi nai nace “Alhamdulillah ba inda ke min ciwo Gwaggwo.”

“To Masha Allah, Allah ya dafa miki a dukkan lamarin ki.”
“Ameen” na fada ina jin kwalla na tarar min a idona.

Kallon Aunty tai tace “kanin mai gidan maryo yazo zai kaimu muga gidan yana jira a waje su Hajjo ma duk sun fito.”

Jinai gabana ya fadi da karfi sbd yadda tace kanin mijina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button