NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Kiyi hakuri mamanmu yunwa nakeji ynxu tun safe dana sha koko ban sake sama cikina komai bafa.

Je ki wanko hannun ki kizo muci, da sauri na fita naje kusa da madafa inda muke zuba ruwa a randa na diba na wanke hannuna na koma dakin.

Mamanmu muhd ne ya daga labilen nan koh? Da sauri ya girgiza min kai yace yaya mamanmuce tasani wallahi.

Murmushi kawai nai nasa hannun a cikin kwanon ina cin tuwon a hankali, tuwon masara ne miyar kuka amma tuwon kamar yaro ne yai duk bai tuku sosai ba ita kuma miyar daga ji gishiri aka sa kawai a matsayin magi da Onga.

Girgiza kai nai ina kai laumar tuwon bakina dama duk ranar girkin Umma muna gasuwa kamar ne.
A hankali muke cin abincin mamanmu na mana nasiha akan mu dinga hakuri akan komai na rayuwa.
Nasan dani take shiyasa kawai nai murmushi don Allah ya sani ba komai ake min nake kyalewa ba ina da zafi lokuta da dama amma ai duk yanayin gidanmu ne ya mai dani haka…

Comments nd share plz

More comments more typing

Mrs AM

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by
        Mrs A.M

Page 3

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Bayan isha’i Aunty da Sumy suka shigo duba jikin Mamanmu, janyo hannun Sumy nai muka tafi dakin mu wanda dama mu daki da falo ne damu sabanin umma wacce babanmu yai mata dakuna biyu da falo, da wayona ma ya gina mata dayan dakin.

Ba komai a dakin namu sai katifa wacce duk ta yamushe amma an shinfida mata zanin gado, duk da zanin gadon ya tsufa sosai amma katifar tayi kyau.
Sai ledar daki a kasan dakin, gefe kuma wata durowa ce mai murfi biyu, murfayen duk sun balle a haka muke makalasu.
Gefen dama kuma kayan kitchen dinmu ne don bama barin ko farantin mu na cin abinci a waje sbd umma da mugunta take lalata mana su.

Zama mukai a kasan dakin na kalli Sumy nace masoyiya dama jira nake kizo ki tayani hada alawar madara ta kinga yau har gullisuwa nake so na fara don ba siyo madarar da dan dama.

Kallo na sumy tai tace kinyi dabara wallahi kinji dadin ki kina ta sana’ar ki ni kuwa kinga yar farar ma dana fara duk cinye wa nake.

Dariya nai mata kawai sannan nace don kinga komai babanmu ya dauke muku ne shiyasa kike yadda kika ga dama, ni danasan yawancin abubuwa ni nake mana ai kinga ko an bani ance naci baxan ciba.

Dariya tai tace kuma hakane fah, muna hirar school har muka gama yin alawar madarar da gullisuwar.

Daukar gullisuwar mukai nace zo muje mu soyo mu dawo, fitowa mukai muka iske su mamanmu da Aunty suna hira a falo.

Sannunki Maryo ai kinyi dabara wallahi kina ta sana’ar ki amma kinga wannan kawar taki ba abinda ta iya in ba a dafa mata taciba.

Zumburo baki Sumy tai tai waje da sauri, nabiyo ta ina mata dariya don yadda ta zumburo bakin yaban dariya sosai.

Umma ce zaune a tsakar gidan ta shinfida tabarma tana zaune ita da yaranta dukkan su.

Walida ce babbar yarta mai shekary 18 ta ban shekara biyu, sai faisal shine sa’ana yana da she karu 16 sai Zainab mai shekaru 10 ita kuma sa’ar Muhd ce sai minal mai shekaru 8 sai aura hafsa mai shekara biyar, yayan umma su biyar ne sabanin mu da mamanmu mu biyu kawai ta haifa ni da Muhd kuma tun daga kan muhd haihuwar ta tsaya mata.

Duk yayan umma mun fi shiri da faisal tun umma na dukan sa akan yadda yake shiga dakin mu har ta hakura don shima kusan halin mu daya ta kafiya.

Bama shiri da Walida ko kadan ita tacika girman kai da son dole sai na kaskantar da kaina tunda ta girmeni, abinda ni kuma bata isa nai mata ba shiyasa ko magana bamu cika yiba.

Tsakanina da su Zainab kuwa sai girnamawa don bana daukar raini shiyasa suma suke kiyayewa.

Da sauri faisal ya taho yana cewa a’a maryo me kuma zaki soya ne haka.

Kallonsa nai ina nuna masa gullisuwar nace kaga abinda nace bara na gwada ko Allah sai sa itama a fara siya.

Eh gaskia kinyi dabara mai kyau, ungo nima inaso naira dari ce ya miko min yace in kin gama kisamin gullisuwar ta hamsin alawar madara ta hamsin.

Murmushi nai nace toh dan yawanci duk ranar danai abin siyar wa sai ya siya.

Da sauri umma ta taso har tana tuntube da farantin da suka gama cin abinci tace don ubanka faisal ba tun dazu nake cema kaban kudi ba zan siyo tsire amma kace baka da, sai ynxu ka bama wannan shegiyar har naira dari wai zaka siya abinda yake siyarwa.

Da sauri ta fita daga gidan gaba daya don yasan tsaf Umman zata iya sasa ya karbo kudin y bata.

Kallona tai tace don ubanki bani kudinnan wallahi baxai siya ba
Ko kallonta ban ba na janyo kasko na da already na gama hada mai na dora kan murhu naja kujera yar tsugunne na zauna.

Ba dake nake magana ba don uwarki, badai uwata ba nafada da dab daga murya yadda zata jine.

Zaro ido Sumy tai tana kallo na ita tana mamakin yadda ko kadan bana jin tsoron fadim wasu abubuwan ga Umman sbd kaf gidan mu tsoron ta suke ji har Malam wanda dama shi tuni ta mallake sa.

Ni kike zagi Maryo ni kike zagi kawai ta fashe da kuka ta dora hannu aka ta shige dakinta yaranta ma duk suka tafi gunta banda walida data tawo guna a fusace.

Ina kallonta ta gefen ido ta karaso hannu ta daga da niyyar ta kifa min mari na rike hannun nata da sauri ina mikewa.

Kar ki kuskura don wannan shine mafi munin kuskuren daza kiyi kice zaki daga hannu ki buge ni wallahi, yarfar da hannun nai na juya ina juya gullisuwa ta.

Dagani Sumy tai tace don Allah masoyiya ki rage zafin nan mana ynxu meye zaki mayar ma da umma magana.

Bakiji zagar mum uwatai ba tunda ita Mamanmu baxata dinga ramawa ba tana ji ana zalintarta ai sai in dinga rama mata koh?

Hmm kin dai bi a hankali kinsan halin umma bata da imani

Tsaki nai nace duk rashin imanin ta bata isa taimin abinda Allah bai min ba.

 Zaune yake akasan bishiya yana cin gyada, gefen sa kuma wani saurayi ne shima gyadar yake ci magana suke kasa kasa duk yadda naso naji mai suke cewa na kasa. 

Mikewa dayan saurayin yai yace NOOR na tafi toh sai na sake lekowa kuma

Uhm kawai yace masa wanda yasa na juyo ina tasbihi ga Ubangijin dayai wannan halittar fari ne wanda farine mai jaja yana da manyan idanu tubarkallah masu dauke da zara zaran gashin ido, yana da dagon hanci wanda shi ba siriri ba can kuma bai bude sosai ma sai bakinsa wanda suke yan mitsili kamar tea spoon baxai shiga ba yana da sage mai kyau.

Sanye yake da yadin ishurunka kalar ruwan kasa maraya dukda kayan ma yadan kode amma fes suke ba alamar datti sai hulla akansa itama dao taji jiki amma hakan bai hana kwantaccen gashin sa fitowa ba.

Mikewa yai ya zura silifas dinsa yana tafiya a hankali ya goya hannunsa a baya har ya isa ga wani gida wanda yana daya daga cikin gidaje mara sa kyau a layin, a hankali ya tura kofar gidan ya shiga ya maida kofar y rufe.

Muma gama soya gullisuwar muka shiga daki, Mamanmuce ta kamani da fada tana cewa ban hanaki wai yima ummanku rashin kunya ba ko ba dazun nan kika gama cewa kin dena mata fitsara ba.

Kinga mamansu kiyi hakuri kinga itama umman bata kama girman ta wallahi kina ji fah yaron nan ya bada kudinsa abasa alawar madara amma tazo tace dole sai an bata kudin.

Amma Aunty ai da sai tabata basai ta maida mata magana ba, ynxu in malam ya shigo zakiga yadda sai dinga bala’i wallahi don nasan ba iyaka abinda ya faru zata fada masa ba.

Kiyi hakuri dai ai ba lefin ta bane.

Kallom sumy Aunty tai tace muje ko don babanku nasan ya kusa dawowa ynxu.

Bayan tafiyar su Sumy har munyi shirin bacci wanda nida Mamanmu akan katifa muke kwana sai Muhd a kasa yake shinfida bargo ya kwanta don mamanmu bata yadda yana kwana a falo shi kadai ba.

Mikewa nai ina bude mana window din dakin don mu dinga jin iska sbd ba wuta, naji ana buga mana kofa da karfi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button