NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Hade rai yai yace “har ynxu baki tafi gida ba”

Cikin inda inda tace “uhm yaya dama…

Kara hade rai yace “wuce ki tafi gida bana son yawan dare..”

Da sauri ta fita duk ranta a bace ba haka taso ba amma tasan baxa ta iya masa musu ba sbd baya daukan raini.

Fitowa nai jin muryar haruna, ganin sa nai yana shirin shiga dakin sa hakan yasa da sauri na durkusa nace “ina wuni an dawo lafia.”

Juyowa yai yace “lafia,” ganin zai shiga daki yasa nace masa “abincin da inna ta kawo in zubo ynxu ko sai anjima.”

Dan tsaya wa yai yana tunani yunwa yake ji tabbas kuwa gashi ya gaji yasan ba zai iya fita siyan abinci ba hakan yasa yadan kalleni yace “bara ayi isha’i,” daga haka ya juya ya shige dakinsa.

Mikewa nai na nufi kitchen robar dana ware don zubawa haruna abinci shi na dauko na zuba masa shinkafa da miyar, mika masa nai na dauko kofin roba mai dan girma shima na mika masa nace “gashi ka dibi ruwa kasha.”

Cikin rawar jiki ya karba yace “angode sosai Aunty Allah ya kara budi.”

Murmushi nai kawai na koma palourn, ganin da wuta yasa na kunna TV ai kuwa da ga mamakina sai na gan ta a hade nn da nakai Mbc 3 sbd inda Allah yai ni ina kaunar carton haka na zauna ina kalla har akayi isha’i.

Bayan na idar da sallah na shiga kitchen abincin na zubo masa plate na daura akan tray ma sa pure water guda biyu da spoon akai, rufe abincin nai sa wani plate din sai kuma na tsaya tunanin a’ina zan ajiye masa abincin tunda nidai baxan shiga dakinsa ba.

Palour nakai masa kawai sai na tsaya a waje ina jiran shigowar sa, banyi minti 5 ba ya shigo hakan yasa na kara nutsuwa ina sunkuyar da kai.

Sai da ya shigo da machine dinsa sannan ya rufe gidan ya dan tsaya yayi addua ya tofa a kofar gidan.

Ganin zai nufi dakin sa yasa nayi saurin cewa “ga abincin nn zaiyi sanyi.”

Bai ko kalleni ba yaje ya wanko hannun sa a pampo sannan ya nufo guna, ganin yana tahowa yasa na juya cikin gudu gudu na koma palour da sauri wai ni nn don kar mu yi gware.

Da sallama ya shigo ya zauna kan kujera yana kallon TV ganin abinda nake kalla yasa shi saurin kallona, dan tabe bakin sa yai a ransa yana fadin dama wannan ai jaririya ce.

Tsugunnawa nai na miko masa plate din bayan nasa spoon a ciki, karba yai ya janye spoon din yasa hannu yana ci da hannu, ni kuwa zamana nai akan carpet din ina wasa da hannuna duk na kasa sakewa.

Shi kuwa Noor abincin sa yake ci ba wani wasa don baya wasa da cikin sa, sai da ya cinye tsaf sannan ya dauki pure water guda daya ya shanye.

Mikewa yai ya fita daga dakin, dawowa nai ina kallon kofa ganin har yayi tsakar gida yasa na tabe bakina kawai ina fadin mai bakin hali kawai..

Daukan kayan nai na kai kitchen na wanke sannan nima na juyo ragowar abincin a plate, anan na zauna naci na koshi na sha ruwa sannan na wanke plate din na kife na fito.

Daki na shiga bayan na rufe kofar palourn shirin kwanciya nai na kwanta bayan nayi addua nan danan bacci y dauke nii.

Asuba ta gari amaryar Muhammad Noor????


Fitowa yai da jallabiyar sa da toilet a hannun sa ya shiga toilet, ya kai wajen 20 minutes kafin ya fito da dukkan alamu wanka yayi.

Daki ya nufa ya shafa mai da turare sannan ya kwanta da addua dauke a bakinsa..

Shiru yai yana tunanin rayuwar sa Allah ya sani shidai bashi da niyyar aure ynxu amma ba yadda ya iya dole yayi hakuri ya zauna da yarinyar nn.

Haka yai ta tunanin sa har bacci yafi karfin sa..


Kwance yake akan gado ya rufe idanun sa hawaye ne kawai ke zubo masa ba shi da aiki sai kuka tun da yaji labarin an aura wa wani Maryo kuma har ta tare jiya shikenan yai sallama da farin ciki.

Sallama akai a kofar dakin sannan aka bude wata matashiya ce da baxa ta wuce shekara 22 ba mai matsakaicin kyau ta shigo yana sanye da riga da wando na bacci sai hula akanta.

Ganin sa ayar da ta barsa yasa ta saurin tahowa gunsa, zama tai a gefen gadon ta riko hannun sa cikin nata.

Cikin kwantar da murya tace Yaya kayi hakuri komai mukaddari ne daga Allah kasa ma kanka dangana don Allah.

Cikin kuka yace taya kike so nasa ma kaina dangana Bilkisu ina son maryo ina kaunar ta ita kanta tana so na ni ta fara so a duniya gashi ynxu na yaudare ta duk irin alkwarin da muka ma juna ya tashi a banxa wani ya aure ta na shiga uku.

Runtse idanun ta tai tana jin zafin maganar sa Allah ya sani tana kaunar mahmud shiyasa take jure halin sa ma bashi da aiki sai zancen maryo kullum ko bacci yake sunan ta yake kira, rabonta da samun kansa tun da aka ce an daura mata aure..

Matsa hannun sa tai tace kayi hakuri Yaya ka daina maganar ta zunubi kake samu ynxu kaga matar wani ce, bata kara sa ba ya hankada ta ta fadi kasa..

Cikin fushi da wani kalar kishin da ya turnuke sa yace kar ki sake fadin ita matar wani ce matata ce ni kadai kuma dole sai na same ta kota halin yaya ne…….

Comments nd share plz

Mrs A.M????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23

Leave a Reply

Back to top button