CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Mik’ewa tayi tana kuka ta shiga d’akin Momy,jakarta da mayafinta ta d’auka tayi waje a fusace,Momy na tambayarta”Lafiya?,amma ko juyowa batayi ba balle ta bata amsa,a matuk’ar fusace ta wuce ta6e baki Ameen yayi tare da d’aga jafad’a alamar ke yadama,jin ana kiran salla ya fita zuwa masallaci,
****************
Wani katafaran gida naga Fareeda tayi hune da k’arfi,da sauri me gadi ya bud’e mata sauran kad’an ta taka masa k’afa saboda yadda ta shugo da gudu,tana parking ta fito da gudu tayi cikin gidan,
Da k’arfi take kiran Mamee”Mamee”Mamee,wata farar matace na gani ta sakko matattakalar bene da sauri tana”Fareeda lafiya meke damunki,k’an nanta ma suka fito da sauri,haka Babansu,
Jikin mahaifinsu ta fad’a tana kuka sosai kamar wata k’aramar yarinya duk yabi ya rud’e sai tambayarta”lafiya yake,cikin kuka tace”Didi wallahi Ameen ne na fad’a maka yarda nake k’aunarsa takanas nayije don tarbarsa amma bayan bak’ak’en maganganun da yaimin harda mari,”Mari,Didi ya fad’a da k’arfi,gyad’a kai tayi cikin zubar hawaye,Mamee tsaki taja mtsuwww tace”wallahi nasha wani abunne ya faru ko kuma rasuwa akayi kike irin wannan kukan ai ni yayimin daidai Fareeda dama chasaki yayi tunda kedai baki da zuciya irin ta mata,tayi gaba tana k’orafi don halin nan na Fareeda yana damunta,Sayyed yace”babu mace mafi k’ask’anta a gurina sai wacce ta furtamin tana sona,fahat yace”wallahi kuwa ke Anty da za’azo ace ana sonki a matsayinki na mace saike kike tusa kai wallahi Allah ya k’ara dama bugunki yayi,
Nan tayi kansu da bala’i,aiko suka ruga suna mata gwalo daman sun saba,nan suka dunga kewaye k’aton farlournsu,kuka take haik’an irin na shagwa6a66u,su kuma suna mata dariya daga baya suka barta suka fice,Didi ya rik’eta yana bata hakuri”rabu dasu Fareeda k’annanki ne kuma ai ba haramun bane don kince kina son Ameen ra’ayinsu ne hakan,da haka yashawo kanta ta hakura,
Bayan wucewarta ya share hawayen dasu gangaro masa,Mamee da ke kallonsa ta k’araso ya zauna kusa dashi cike itama da damuwa tace”haba Alh kadena tuno abinda ya faru kasan kana da hawan jini ga ciwon zuciya don Allah kacire da muwa a ranka Allah zai nuna mana ita……
TOFA wakenan suke nema su kuma wad’an nan bayin Allah,ni yadda naga irin gidan da abubuwan dake ciki banyi zaton akwai wani abu da zai dami rayuwarsu,muje zuwa????
Fateenku ce????
Ummu Affan✍????
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
Bismillahir rahmanir rahim
????3⃣5⃣-3⃣6⃣
????”Allah zai nuna mana ita,taci gaba da sharemai hawaye itamma ji take kamar ta zubda hawayen,cikin raunin murya yace”sai yaushe?Rabi’atu ki fad’a min sai yaushe?kullum maganarku kenan za’a ganta me yasa haryau ba agantan ba,ni nasan ‘yata ta rasu na fawwalawa Allah shekaru goma sha biyar da za’a gantan da tuni anganta,
Mamee ta kallesa kamar zata fashe da kuka tace”ina ji ajikina ‘yata tana raye saidai ina yawan mafarkai marasa dad’i akanta ni kullum addu’a nake mata a duk inda tasami kanta Allah ya duba mata al amuranta,Didi yace”to amin,
Nan dai sukayi zaune suna k’ara jajanta abin,harsu Sayyeed suka shugo ganin iyayen nasu a irin wannan halin sunsan abinda ke damunsu,don haka zama suma sukayi cikin damuwa,Fareeda harda kuka don tana matuk’ar k’aunar ‘yar uwarta,nan suka yi addu’o’i suka shafa,ko abincin kyirki suka kasaci haka suka kwana ranar cikin damuwa da bak’in ciki,daman duk ranar da suka tuno ‘yar uwar tasu haka suke kasancewa,
“””””””””””””
Duk’e na hango Naanah tana wanki,tayi wani iri kamanninta duk sun sauya saboda wuya,Umma sai mgn take ya6o mata,ganin Ummar ta shiga ciki yasa ta jawo hijabinta da sauri ta fice,daman Anty Rahma bata,gidan,
Kai tsaye gidansu Zainab ta shiga bayan ta gaida me gadi ta wuce ciki da sauri,kici6is sukayi da Zainab zata fito,ai ganin Naanah yasa Zainab sakin kuka tare da rungumeta,sosai take kallonta”Naanah baki lafiya ne ramarnan taki tayi yawa wannan wanne irin ciwo ne kike,Naanah ta k’amk’ame Zainab cikin kuka tace”Zainab naga k’angin rayuwa,rayuwa tazomin da wani sabon yanayi ina cikin tasku da uk’uba,Zainab ji nake inama ba a duniyar nan nakeba ina ma zan mutu na huta da wannan rayuwar mara dad’i,wallahi na gaji da wannan duniyar inama zan mut….
Zainab ta rufewa Naanah baki cikin kuka tana girgiza kai”Naanah kar wata wuya ko tsananin da kike ciki yasa kiyi sa6o,Naanah ke musulmace ki yarda da ko wacce k’addara da Allah ya yimiki duk da bansan abinda ke damunki ba amma nasan ba k’aramin abu ne zaisa ki dinga furta irin wad’an nan kalaman ba,Meke faruwa Naanah ki sanar dani,
Wani irin kuka na saki nace”Zainab ciki ne da ni,a tsananin furgice ta kalleni tare da dafe girji,sai kuma ta fara girgiza kai tana cewa”k’arya ne duk wanda ya fad’i hakan k’arya yake miki Naanah tare muka taso dake tun muna yara nasan halinki kinsan nawa duk inda zamu tare muke zuwa boko islamiyya duk d’aya muke zuwa gidan nan kina shugowa indai bamu da makaranta kema naku ina zuwa saida Umma ta hanani shiga na dena zuwa idan harke kina da ciki to nima ina dashi,
Gaba d’aya kuka muke dagani har ita mun k’amk’ame juna,nace”Zainab da gaske nake,nan na kwashe komai na sanar mata har izayar da su Umma kemin,sosai take kuka kamar itace akace da cikin,
Nace”wallahi Zainab kinji na rantse banta6a sanin wani namiji ba bansan yadda akayi hakan ta faru daniba bansan CIKIN WAYE?ba Zainab koda kasheni za’ayi bansan CIKIN WAYE?ba ni kaina tambayar kaina CIKIN WAYE?nake,don Allah karki tambayeni basan nawaye zan ce miki ba,
Kuka muke sosai Zainab ta gyad’a kai”nayarda dake Naanah nasan bazaki ai kata hakanba duk wanda yayi miki haka Allah ya tona asirinsa,da amin na amsa,
Hajiya ta k’araso wacce duk hirar damuke tajimu,ta rungumeni cike da tausayi tace”Naanah na tausaya miki Allah ya saka miki,ni kaina na yarda dake,anyi amfani da wani abu ne aka gosar da tunaninki aka yi miki wannan aika-aikar amma karkiji komai da sannu gaskiya zatayi halinta ai k’arya fure take bata ‘ya’ya,
Tuno abinda nake wato wankin da Umma tasani yasa cikin sanyin murya nace musu”zan tafi Umma batasan na fito ba kuma wanki tasani,Zaunar dani Hajiya tayi kitchin ta shiga ta had’omin tea mai kauri aiko jiki na rawa na amsa na fara sha,ta zubomin shinkafa da jar miya da nama zuk’u-zuk’u,sai ruwa a gefe,naci abincin sosai daman yunwar nakeji,sai kallona suke cike da tausayi,bayan nayi dam ni kaina sai naji jikina cikin dad’i rabon danaci abinci irin haka tun kafin wanna cikin daman san CIKIN WAYE?ba ya sameni,
Zainab ta rakani har k’ofar gida barabon mu had’u da Marwan yana Asibiti kunsan abunku ga likita bokan turai,
Naci sa’a har lokacin Umma bata fito ba,na duk’a naci gaba da’aikina,
Yah Ameen ne cikin moto yana tafe yanajin sautin wak’ar M-Shareef,cikin nishad’i yake harbin wak’ar yake”Soyayya idan har bakece ba,babu macen da zanso mi zaunawa tabbasssss,yayi murmushi har kumatunsa suka lotsa yace”Tabbasss Naanah babu macen da zanso muyi zaunawa idan ba kiba,ya dafe saitin zuciyarsa ya d’anyi d’an murmushi da ya tuno wani abu,zuwa cen kuma yayi shuru jikinsa kamar yayi sanyi,sai kuma yace”Ina k’aunarki Naanahta,k’ara sauri yayi don ya k’osa ya isa gidan yaga Naanahrsa,