COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“To ni bana daukar nonsense any moment and bana careless akan watsewar tarbiyyan ƙanne na, ba ma iyakar su ka ɗai ba ,dukkan mace, yarinya, babba , budurwa, ni haka tsarina yake ni Ubaidullah!”
Ya karasa maganar cike da izza da jin ƙai.
Sai da ya shiga mota sannan ya ce.
“Sa’arku daya tak baku gwadamin iskancin samarin bakaro ba, dan wallahi da kun min taurin kai kun kawo min raini da ko wani ƙaramin dan iska ya kwashi kashinsa a tafin hannunsa, idan ku na da ra’ayi ku shiga mota mu tafi ko wallahi nayi tafiyata.”
Ai tun bai karasa ba suka miƙe har su na rige-rige, da sun ga alama idan har zasu yi faɗa da Ubaidullah babu abin da zasu ɗauka a jikinsa.
~~~~~~~~~
Ta bangaren su Zaidu kuwa sun isa asibiti sun samu jikinsu Na’ila da sauki, har ma likita yana maganar sallamarsu.
Zaidu ya ce.
“Bari Ubaidullah ya zo”
Hafiza da gudu ta rungumi yar uwarta, suka saka kuka a tare.
Zaidu ya ce.
“Wai meya faru ne kam?”
Mama ta ce.
“kai dai bari kawai Zaidu kanwarka bata jin magana, idan munje gida sai ta fada maka da bakinta”
Zaidu yayi murmushi ba tare da yayi magana ba
Suka zauna jiran Ubaidullah yau ne gobe ne shuru.
Mama ta ce.
“Zaidu kawai kayi abun da ya kamata mu tafi gida wannan
Abokin naka sai kai .”
Zaidu yana dariya yaje sa hannu aka basu sallama sai gida .
~~~~~~~~~
COMMENTS
&
SHARE
BY MOMYN AHLAN✍????????????♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶••••~~
TYPING… WA’YA KASHE ZAHRA’U? #200(My No ga masu bukatar siya 08165550116)
my wattpab@Fateemah0
QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????
Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________
page°°°°15&16
Basu zarce ko ina ba sai gidan Anty Ummu, sallama suka yi, Anty Ummu ta fito da sauri daga kitchen sakamakon jin murya ɗan uwa gudan jiki.
Tana ganinsa kuwa annurin fuskarta ta ƙaru, shi ma Ubaidullah dariya yake yi wanda har ya bayyana hakwaransa.
Hannu Anty Ummu ta miƙa masa cike da murna, tana cewa.
“Ɗan uwa kai ne ko kuma dai idona ne yake min gizo?”
Cike da zolaya Zaidu ya ce.
“Anty Ummu abu daya zai sa ki tantance ko shi ne, ko ba shi ba ne, bari na miƙo miki wancan tabaryar, ki shemesa da ita daga nan za ki gane gaskiyar tambayarki.”
Anty Ummu ta kwashe da dariya, ta ce.
“Daga haka ma na tabbatar ƙanne na ne a gabana ku shigo daga ciki.”
Su na shiga Anty Ummu ta cike musu gabansu da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,sai nan nan take yi dasu.
Sai da ta tabbatar basu buƙatar wani abu tukunna tazo ta zauna kusa da kaninta suka gaisheta ta amsa,su na hira su na dariya.
Anty Ummu ta ce.
“Amma dai ina fatan bana zaku kwana biyu kafin ku koma ko?”
Zaidu ya ce.
“Ina kuwa jimawa Anty babba, wallahi 5days General Of Army ya bamu dan kwanan nan zamu tafi bakin bordern nijar domin kamo wasu y’an ta’adda.”
“Oh Allah ni Ummu kenan yanzu shikenan ku haka rayuwarku zata ƙara a fagen da ga?”
Sai yanzu Ubaidullah ya bude baki yayi magana.
“To big sister ya zamu yi ai ya zama dole tun da munyi alƙawari tare da rantsuwar gare kasarmu ta gado wato nigeria, gashi mune jami’ai wanda aka fi ji dasu bana gaya miki a waya an yi mana ƙarin girma ba, to ai yanzu kam bamu ga wani hutu ko zama waje daya ba, kawai ku dinga tayamu da addua.”
Anty Ummu ta numfasa ta shaƙi iska, sai ga hawaye yana zuba daga idonta wanda yayi sanadiyyar hankalin Ubaidullah tashi nan ya shiga jero mata tambayoyi ba ƙaƙƙautawa.
Girgiza kai Anty Ummu tayi ta ce.
“Ba komai dan uwa ka kwantar da hankalinka,Allah ya taimake ku Allah yasa ku gama da duniya lafiya,Allah ya ƙare ku da ga sharrin masu sharri.”
Sosai Anty Ummu take ta zuba musu adduoi su na amsawa da amin.
Daga baya kuma suka hau hiran yaushe gamo har yaran Anty Ummu su biyu suka dawo suka samu kawun su, suka hau murna su na cewa.
“Oyoyo kawu”
Ubaidullah ya na dariya sai kace ba shi bane mai cin magani a barracks, amma in dai a cikin familynsa ne yana dariya har haƙorinsa ya bayyana , sai dai idan y’an halin ne suka tashi,dan a kwaisa da miskilancin magana wasu lokutan, ga zafin rai, wa in da basu san shi ba kuma suke cewa yana da girman kai.
Kallon yaran Anty Ummu yayi yana dariya ,Haidar da Sakina, ya ce.
“Yarana ya kuke? fatan lafiya kalau kuke ko?”
Suka amsa da eh, nan ya dan taba wasa da yaran kafin Anty Ummu ta korasu gidan kakarsu ta wajen uba.
Bayan sun fita Anty Ummu ta ce.
“Wai ni yaushe ne kam za a kawo min surka? gaskiya ina so naga matan ƙannena.”
Zaidu ya kwashe da dariya ya ce.
“To Ubaidullah gareka fa ,big Anty tana son ganin in’law “
Hararan wasa Anty Ummu ta yiwa Zaidu kafin ta ce.
“Ai ba da shi kadai nake yi ba har da kai, ko sai na ba da sadakar ku ne?”
Zaidu ya zare ido ya ce.
“Big Anty ai wallahi my man yafi karfin sadaka dan baki ga yanda ladies a barracks suke haukan sonsa bane abun har tsoro yake bani wallahi.”
Anty Ummu tana dariya tana kallon ƙaninta lokaci guda ya haɗe rai da fuska sai ka ce ba shi bane mai dariya yanzu-yanzun nan.
Zaidu ya ce.
“Ka ga Malam Ubaidu duk wannan haɗe ran naka bai taso ba, kai soja ne nima kuma soja ne, kawai fina kayi da zafin rai miye to ma na hade rai din danna faɗawa Big Anty gaskiya?”
“Mtswwww Zaid ka fa kiyayeni, kasan fa halina, Allah na tuba in ban da tsautsayi mai zanyi da y’an matan barracks? duk babu wacce take gabana, kai ne dai kake sha’awar aure yanzu, amma ni Captain Ubaidullah ba yanzu ba, dan har kwanan gobe ban ga yarinyar da tamin ba wanda zan buɗe bakina na ce ina sonta ba”
Riƙe baki Anty Ummu tayi tana kallon ƙanin nata cike da mamaki da al’ajabi, shi fa haka yake, idan ya rikiɗe sai ka kasa gane kansa, dan wani lokacin ma yafi hawainiya.
“To yanzu kai Dan Uwa idan baka yi aure yanzu ba sai yaushe zaka yi? karka manta fa kai Jarumin Soja ne, kuma Sojoji sai da mata a kusa”cewar Anty Ummu.
Zaidu ya ce.
“Kyalesa kawai big Anty, shi ma fa yana so kawai basarwa yake yi yana nunawa kamar baya so, kuma wallahi ranar da muka je gidan General naga y’arsa tana satan kallonsa duk yanda aka yi itama ta ƙyasa ne” ya ƙarasa managar yana dariya.
Iyakar ƙuluwa Ubaidullah ya gama tunzura, sai huci yake fitarwa yana hararan Zaidu.
Dariya Zaidu ya kwashe da shi kafin ya ce.
“Ai dama nikam sai dai na ƙare a harara amma babu abin da za a min aha”
Anty Ummu abun dariya ya bata ta ce.
“To shikenan naji ƙanina baya son aure yanzu, amma kai Zaid naji ya ce kana so dan haka wacece surkar tawa, tun da yallabai ya ce ba yanzu ba ina jira faɗamin ita yanzu?”
Sun kuyar da kai ƙasa Zaidu yayi yana sosa ƙeya ba tare da yayi magana ba.