NOVELS

GARKUWA PART 3

Sai kuma ya ɗan ƙara jawota jikinshi tare da cewa.
“Samuwar ɗan, ana nufin kamar yadda ya shafi uwar kai tsaye, to haka kuma ya shafi uban.
Don haka, irin yanayin da ta ji saboda zuwan yaron, shi ma yakan iya jin hakan.
Sai dai kawai nasa bazai kai yawan na uwar ba, saboda ta fi shi kusance da ɗan, kasancewar yana jikinta kin gane ko?.”
Cikin gamsuwa ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Na gane na gamsu.
To kuma batun naƙuda fa da kace kayi min.
Shin dama na miji kan ji ciwon naƙudan matarsa kamar yadda wasu mazan ke jin ciwon laulayi ciki ne?
Ko dai kwatakwata babu wannan!?”.

Kanshi ya ɗan cusa tsakanin wuyanta da kafaɗarta tare da shaƙar ƙamshin jikinta cikin fahimtarwa yace.
“A dai iyakar abinda muka sani zuwa yanzu, wanda kuma bincike da gwaje-gwace likitocin duniya suka tabbatar shi ne, namiji ba ya iya jin ciwon naƙuda.
Sai dai yakan jin tsananin damuwa da ciwon rai ne, maimakon ciwon jiki da raɗaɗi da mai naƙudar take ji.
Sai dai bincike ya tabbbatar da cewa yana da tasiri sosai wurin sauƙaƙa wa matar ciwon naƙudar, idan zai kasance tare da ita har ta haihu”.
Da sauri tace.
“Kamar yaya to dan yana kusa da ita zataji ciwon ya sauƙaƙa?”.
Kai ya ɗan ɗago ya kalleta tare da cewa.
“Domin idan ya zauna a gunta, musamman in zai riƙe mata hannunta ko ya riƙa ɗan shafa goshinta yana yi mata sannu kamar dai yadda nai miki ta miki lokacin kina naƙudar gab da haihuwar.
To tabbas zataji sauƙi da sassaucin naƙudar da samun haihuwa a sauƙaƙe da izinin ubangiji.
Saboda yayin da suka kasance a haka, jikin matar yana samar da wani sinadari da ake cewa oxytocin , wanda yake sanadin tsattsafowar wannan ruwa mai tsantsi to zai sauƙaƙa fitar yaron daga jikinta.
Da iznin Allah”.
Cikin gamsuwa ta sauƙe numfashi tare da cewa.
“To kai kuma kace harda ciwon baya kaji ranar da zan haihu a lokacin ma meya kawo hakan?”.
Cikin sanyi ya jujjuya kanshi tare da cewa.
“Allahu ahlamu, kawai abinda nasa a raina wannan wani ikone da ƙudurar ubangiji daya gwada a kanmu wanda tabbas na taɓa riskar makamancin lbrin miji yayiwa matarsa naƙuda, to amman dai a likitance bamu ganoba tukun, dan haka wannan fagene na ubangijin sammai bakwai da ƙassai bakwai, shiyasa nasan zafi da ciwon da mata kanji yayin haihuwa”.
Cikin gamsuwa tace.
“Ayyah sannu Yah Sheykh”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ke kam ba cewa kikayi in dan zanci gaba dayi miki laulayin ciki da naƙuda ba, ko duk shekarama ki haihu ba matsala ko”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Eh mana”.
Murmushi yayi tare da jawota jikinshi yana mai sa hannunshi ɗaya zai zare boxes ɗinsa.
Fahimtar inda ya dosane yasa ta miƙe da sauri tare da cewa.
“Bari inje wurin Ummey na naji alamun Afreen ta farka”.
Fuskarshi ya kwaɓe tare da cewa.
“Kai Aish ni dai banjiba”.
Cikin son zille mishi tace.
“Kaji can muryarta tana kuka”.
Komawa yayi ya kwanta
Cikin jinjina ƙudurar ubangiji yace.
“Toh ɗaukota kuzo”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Toh”. Kana ta fita.

Tana fita ya maida kanshi bisa pillow’nshi yana tasbihi da girman zatin Allah daya samar da cikekkiyar dangantaka tsakanin uwa da ɗanta ta yadda ko bata tare dashi in zaiyi kuka ko ya tashi bacci.
Mamanta zai sanar mata.

Ita kuwa Shatu tana zuwa ta wuce bedroom ɗin Ummi.
Umaymah da Ummin kawai ta samu sunata hira da dariyar Abba daya shigo da kansa ya kira Mamey wai tazo su gaisa da abokanshi, daga nan yayi Part ɗin shi da ita wanda yake kusa da nata.
Umaymah na kwance Afreen na gabanta Ummi kuwa zaune.
A hankali ta zauna gefensu tare da cewa.
“Umaymah Ina su Ummey”.
Kai Umaymah ta juya tana danne dariyarta tace.
“Sun tafi Side ɗin ta”.
Da sauri tace.
“Harda Mamma”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
“Bakiga tun da yamma Mamma da Rahma sukaje suka gyara komai na Part ɗinta ɗinba.
Sabida Abban yasa an kawo mata sabbin kayan ɗaki sannan anyi duk abinda ya kamata”.
Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Ayyah”.
Sai kuma tace.
“Bari inje in kwanta”.
Sai da safe tayi musu.
Ta fita ta tafi.

Ishma da Hibba ta samu kwance bisa gadonta tuni sunyi bacci da alamun Hibba wayama takeyi tayi baccin.
Gefenta ta kwanta.

Su kuwa su Umaymah sukaci gaba da hira.
Sai kusan ƙarfe biyu ne da Afreen ta tashi Umaymah ta kaita ta bata mama tasha kana ta dawo da ita wai karta hana uwarta bacci.

Alhamdulillah fa komai na tafiya yadda ya kamata rayuwa ta miƙa.
Gsky tayi halinta.
Jadda da Sitti da Babansu Aunty Juwairiyya sun koma.
Haroon ma da Jannart sun da Hibba sun koma.

Saura Umaymah da Mamma Aunty Rahma.

Tuni Mamey ta koma Part ɗin ta.

Hajia Mama kuwa ta tabbata mai suffa hudu kafar ladin kogi, hannun fiffigen tsuntsuwar Boleru idanu na Duji, sauran jiki na mutun.

Ta zama abar kallo Abba kuwa ya danƙara mata saki.
Affan kuwa yana nan lfy da ƴan uwanshi.

Yanzu Shatu ta kusa wata ɗaya.

Wanda ya kama satin su Umaymah uku da zuwa kenan.

Abboi kuwa dasu Bappa sunje ga iyayen Rafi’a sun nemi aureta ga Al’ameen an basu kuma.
Kana su Bappa kuwa sun nemawa Salmanu auren Hasfi an kuma basu.

Zaune suke Umaymah Mamey Lamiɗo Galadima Abba
A hankali Lamiɗo ya gyara zamanshi tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah komai ya wuce ya zama tarihi.
Manufar taruwarmu anan a kan Masarautar Joɗa ne.
Na gama zama da duk manyan fada mun gama tsaida zance duk kowa ya gamsu da batun Jabeer ya mulkin Masarautar Joɗa.
Toh amman inda gizo ke saƙan kun san ɗan naku, na kira sarki Jalaluddin akan batun to shi mgn ɗaya yayi cewa yasan Jabeer mai biyayya ne ga Khadijah da take ƙanwar mahaifiyarshi ma bare ke Aisha da Habibullah da kuke iyayensa yace ya sani tabbas in kuka cewa Sheykh ya mulki masarautar Joɗa ku bashi umarnine ba shawaraba tabbas zai yarda”.
Cikin gamsuwa Galadima yace.
“Haƙƙun wannan haka yake tabbas zai yarda bisa dole bisa umarnin iyayenshi”.
Cikin sanyi Mamey tace.
“In kuna son in bashi umarni zan bashi kuma nasan zai min biyayya to amman meyasa baza’a bawa wani cikin ƙannen mahaifinshi ba sai shi”.
Shiru sukayi baki ɗayansu jin Lamiɗo na cewa.
“Sabida ina son masararutar Joɗa ta tsarkaka ta rabu da duk wata al’ada daba addiniba.
Na sani babu mai iya sarrafa Masarautar Joɗa ya juyata daga bahahuwa zuwa ba damiya ya kauda al’adar bidi’a ya wanzar da sunna sai shi.
Zai gyara masararutar ta yadda za’a dena zalama da son cutar da juna bisa kujerar zai sauyata ta yadda sai mai cikekken ilimin addini ne zai iya mulkarta.”
Cikin gamsuwa Mamey tace.
“In sha Allah zaku sameni mai biyayya bisa umarnin ku na in bashi umarni kuma na sani zai min biyayya”.
Cikin jin daɗi sukace to.
“Allah ya shige mana gaba”.
Amin Amin sukace.

Sai kuma suka nitsu jin Lamiɗo na cewa.
“Alhamdulillah yanzu Ita matarshi ta kusa gama wonka tana gamawa zukjne Rugar Bani suyi kwana ɗaya daga nan su dawo su shirya suje Ƙasar Cameroon wurin iyayen Shatu kuma zasuje da Aliyu (Dr Aliyu) kenan da Basiru da Galadima domin su nemawa Jamilu auren Khadijah ƙanwar Shatu”.
Cikin jin daɗi Mamey tace.
“Alhamdulillah to Allah ya kaimu”.
Amin Amin sukace.
Sai kuma Abba yace.
“Jalal kuwa mun gama mgna da Abban Haroon kan batun Jalal da Hibba”.
Cikin tsananin jin daɗi sukace.
“Alhamdulillah daga nan suka watse taron.

Washe gari su Umaymah suka koma.

Alhamdulillah yau Shatu ta gama arba’in.

Sosai Afreen tayi kuɓul-kuɓul da ita gwanin burgewa ta cika tayi kyau in ka ganta kamar yar wata biyu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button