NOVELS

GARKUWA PART 3

Bedroom ɗinsa ya wuce.
Yana shiga ya kira Shatu a waya, ta kawo mishi ɗan.
Yayi mishi huɗu ba.
Ido ta ɗan zuba mishi tare da cewa.
“Me sunanshi?.”
Murmushi yayi tare da kashe mata ido a hankali yace.
“Sai ranar suna zakiji”.
“Abinma sirrine kenan”.
Ta faɗi tana murmushi.
“Ina da wani sirrine bayan ke, Y.M.D.G na”.
Ido ta zuba mishi tana mai nazartar baƙaƙen da yake yawan faɗi wasu lokutan.
Kiranshi da akayi a wayane yasa ta bar zancen.

Ranar jumma’a, da safe bayan an fito sallan asabu, aka raɗa sunan yaron kana suka nufi cikin gida kowa na mamakin sunan da Sheykh ya sawa ɗansa.
A tare suka shiga falon shida ƙannensa.

Da sauri Mamma tace.
“Affan me sunan ɗan naku?”.
Murmushi Affan yayi tare da nuna Sheykh dake wucewa Side ɗinsa Haroon da Ibrahim na biye dashi a baya.
Da sauri Umaymah tace.
“Affan me sunan ana tambayarka kayi shiru”.
Cikin dariya yace.
“Uhumm Yah Sheykh da abun mmki sunanshi fa ya sawa ɗan, duk zuriyar mun nan ya rasa wanda zaiwa takwara sai yayiwa kanshi”.

Cike da mamaki su Ummi sukayi salati, shi kuwa Sheykh murmushi yayi tare da juyowa jin yadda suke salati yana dariya yace.
“Yoh duk zuriyar mu, nuni wanda sunanshi ya kai nawa daɗi Muhammad Jabeer, kuma kafin in burge wani gwara in burge kaina da kaina. Kuna ina son yaron yaji daɗin da nakeji a duk sanda naji an kirani da sunan sabida iyayena sunmin kekkyawan zaɓi”.

Murmushi Mameyn tayi tare da cewa.
“Allah ya raya Muhammad Jabeer ƙarami yasa ya gaji halayyar mahaifinshi”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.

Ita kam Shatu murmushi takeyi tana shafa kan jaririn.
Tare da kallon Afreen dake zaune gefenta.
Oh Allah mai iko wai itace dai Shatu da yara har biyu.

Nan dai sukaci abinci.
Kana duk mazan suka fara shirin fita ɗan sha biyu dai-dai za’a naɗa Sheykh.

Ƙarfe ɗaya saura.
Duk illahirin manyan Masarautar Joɗa, da baƙin sarakuna.
Da duk maza ahlin masarautar Joɗa, hatta Jabeer da yau aka fita sunansa.
Jalal yazo dashi.
Gaba ɗaya ɗakin rantsawar ya cika maƙil da bani Adam.
Babu abunda ke tashi sai sarewa da tambura da al’gaita da kakafi.

A hankali Lamiɗo ya tashi bisa kujerar, kana ya matsa.
Sarkin naɗi, ya kamo hannun Sheykh dake cikin shiga ta al’farma shigar limancin.
Ya matso dashi gaban kujerar, kana a hankali yasa hannunshin ya zare hiramin kansa.
Sannan ya sunkuyo ya amshi.
Rawanin da Lamiɗo ke miƙa mishi.
Yana daga tsayen ya naɗa mishi.
Kana ya juyo bayanshi da niyar zare al’kyabbar jikinshi.
Da sauri Lamiɗo yace.

“A’a barshi da shirgarsa ta limancin, shigar sarauta bazata kori ta limancin ba.”.
A hankali Sheykh ya lumshe idonshi yana mai jin wani irin masifeffen nauyi dake ratsa kanshi nauyin rawanin mulkin Masarautar Joɗa.

Shi kuwa Sarkin naɗi kai ya gyaɗa kana ya zaunar da Sheykh bisa asalin kujerar masarautar Joɗa da sunan Allah a bakinsa.

Kana aka miƙa mishi sandan ya amsa ya riƙe, sarkin fada ya matso kusa dashi.
Hakama ɗan zagi.
Sauran fadawa kuwa duk sai suka matsa suka janye labulen da sukayi musu da manyan garunan su.

Lokacin ɗaya gaba ɗaya mutanen cikin hall ɗin duk suka zauna
Tare da jinjina kai, dan ko kai sarkine in kazo Masarautar wani sarkin to shine a sama.

Sabida kalmar nan ta bahaushe.
(Kare ma a gidansa zaki ne)
Bare kuma sarki.
Nanfa makaɗa da mabusa duk suka ɗauki amo.

Cikin wani irin rauni Sheykh ya lumshe idanunshi tare da ci gaba da tasbihin da yake abokin rayuwarsa.
Sabida wani irin tashi da tsikar jikinshi keyi.
Sarautar tana ratsashi.

Bayan an gama naɗa shi ne, aka naɗa Baba Basiru a matsayin Galadima.
Wanda dama anfi son Galadima yafi sarki shekaru.
Nan kuma aka naɗa Affan Chiroma.
Kana Jalal Wambai, Jamil Durbi.

Yah Jafar kuwa Majidaɗin Masarautar Joɗa.

Masha Allah komai dai ya tafi yadda ya kamata.
Nan aka naɗa duk sauran hakimai.
Kiran sallan Jumma’a ne ya tadasu a taron.
Nan kuma aka raka’a.

Inda Sarki Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa ya kasance limamin kamar kullum.
Bayan ya tsaya ya dai-dai-ta tsayuwarsa bisa mimbari.
Ya fuskanci taron al’ummar Annabi dake cike maƙil a masallacin da harabar.
Gyaran murya yayi cike da rauni dan fara hudbar jumma’a kamar kullum.

Cikin taushin murya da lafazi.
Murya na rawa yace.
“Mulki, da sarauta”.
Sai kuma muryarsa ya fara rawa, sabida nauyin abinda yake jin tsoro daya ratsa kanshi.
Hawaye na zuba yace.

“Da ace ɗan Adam yasan nauyin dake cikin kalmar mulki ko sarauta da bai ɗauke ta ƙaramar kalmaba.
Da daga cikinmu mun dena sha’awarta sabida nauyi da haƙƙin wanda kake matsayin shugaban su, da zai rataya akanka”.
Sai kuma ya sunkuyar da kansa.
Cikin rauni da zubda hawaye ya fara zazzafan hudba kan sarakuna da kuma shugabannin.
Wanda gaba ɗaya aka nitsu akayi cib.

Mafi akasarin mutane rauni da tsoro ya sasu zubda hawaye.

Bayan ya idane, akayi salla aka idar.
Sannan dubban al’ummar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam suka shaida ɗaurin auren. Jalaluddin da Muhibbar, (Jalal and Hibba) Khadijah da Jamil. Rafi’a da Al’ameen.
Al’amarin yayi armashi matuƙa gaya.

Nan aka fito, mafi akasarin manyan sarakuna da shugabanni da baƙi a take Airport suka fara wucewa, sabida komawa.
Jirage kuma a ranar tamkar a jidda Airport a lokacin aikin Hajji.
Haka jirage ke tashi. A Ɓadamaya International Airport.

Tuni mutanen Cameroon sun tafi da amryarsu.
Da duk mutane su.
Hakama su Aunty Rahma sun kai Hibba part ɗin ta.
Mutanen Cameroon kafin su tafi sun kai.
Khadijah Part ɗinta.

Sosai mutanen gidan suka ɗan rarragu.

Sheykh kuwa hada-dadar jama’a ta hanashi shiga gida.
Sabida zaman fada.
Sai bayan sallan isha’i ya samu shiga gida.

Kai tsaye Part ɗin Mameynshi ya wuce.

A can kuwa ya samu su Umaymah gaba dayansu.

Sai Shatu da Junainah dake Part ɗinsu suna gyarawa sabida mutanen sun tafi.

Cikin jin daɗi Mamey da yan uwanta sukayi ta sanya mishi albarka da mishi addu’o’in Allah ya bashi ikon mulki kan gsky.
Ga mamakinsu yana kuka.
“Amin Amin”.
Daga nan ya fito ya nufi Part ɗinsa.

Ita kuwa Shatu tuni sun gama kimtsa komai.
Har tayi wonka, ta kimtsa cikin wata tattausar doguwar riga mai ɗan karen kyau.
Afreen da Jabeer kuwa dama Ummi tayi musu wonka kafin ta tafi.

Tana ruggume da Jabeer Afreen na biye da ita a baya ta nufi Side ɗinsa.
Jin Junainah na ce mata.
Adda Shatu Hamma Jabeer na kira.

A hankali ta tura ƙofar tare da sallama a bakinta.
Cikin sauri ya juyo dan dama bai ƙarasa shiga tsakiyar ɗakin ba.

Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai sauƙi Shatu ta sauƙe.
Sabida ganinsa cikin shigar sarakuna yayi masifar ratsata kwarjininsa ya ninku ɗari bisa ɗari.
Afreen kuwa da gudu ta nufoshi.
Ta isa ya sunkuyo ya ɗagata sama, ya ruggume ta tsam a jikinshi da hannu ɗaya.
Kana ya buɗewa Shatu hannun ɗaya.
Da sauri ta iso ta faɗa jikinshi.
Ruggume ta yayi tsam a jikinshi.
Cikin sanyi murya na rawa yace.
“Aish bayan nauyinku. Ke Afreen Jabeer da kai tsaye in ance iyalaina ku ake nufi.
Kana Abbana Mamey dasu Jalal da in ance ahlina su ake nufi.
An sake ƙara min nauyin da duk Ɓadamaya nine shugaba a garesu kuma abin dubawarsu”.

Tasan mijinta tasan rauni sa.
Tabbas tasan baison mulkin nan, tamkar dolene.
A hankali ta kuma ruggume shi gam jin yana cewa.
“Mulkin nan yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da Lamiɗo ke tirsasani inyi a rayuwata.
Sai dai na yarda da batun mulkin ne bisa Kekkyawar niyar yin gyara da kauda al’adun da ba tsarin shariya ba, da kuma kauda wasu abun da suke kamanceceniya da asiri”.
Cikin jin daɗi tace.
“Allah ya baka ikon gyara ya kuma kare mana kai da kariyarsa.
Ya baka rai da lfy da damar gyara al’farmar Annabi da al’ƙur’ani”.
Amin Amin yace cikin rauni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button