NOVELS

GARKUWA PART 3

Murmushi mai yelwa Gimbiya Aminatu tayi ganin yadda Sheykh ke ruggume da matarsa da yartsu a tsakiyarsu wace taketa wawure-wawuren hannunta.
Kusa dasu ta zauna daɓas, kana tasa hannun ta amshi yarinyar tana cewa Shatu.
“Sannu Gimbiya Aysha surkar Gimbiya Aisha mai sunan Maman Lamiɗo, uwa kuma ga AYSHA masha Allah.”
Shi dai Sheykh sai murmushi yakeyi
Ita kuwa Gimbiya Aminatu amsar yarinyar tayi,
Kana ta ɗan kamo zariyar cibiyar, ta saita da ƴar ƙaramar yatsarta ƴar ƙuri, wanda hakan yayi dai-dai da kan mahaɗan da alamun kamar ƙari a wurin wanda dai-dai kan ƙarin ta ƙasa tasa zaren ɗinki ta zagaye ta ɗaure cibiyar kana tasa reza ta yanke.
Miƙa Ummi yar tayi tare da cewa.
“Kin amshi haihuwar Babanta tsawon shekaru talatin da lokacin tun kina ƙaramar ki, yau kuma kin amshi haihuwarta, kiyiwa babanta jakadanci itama kiyi mata”.
Da sauri Sheykh yace.
“A a kam shiyasa ban bari ƴar ta faɗo a hannuntaba, dan Ummi na ayntacciyace nima bazata min jakadanciba bare ɗiyata, jika ta samu wannan shine tukuicin forko da zanwa Ummi a masarautar Joɗa daga yau wannan sunan Jakadiya ya bar kanta”.
Ruggume ƴar Ummi tayi tare da sakin wani irin murmushi mai haɗe da hawaye tana sa yar cikin mayafin nan tana cewa.
“Masha Allah, zuwanki ya iso mana da al’khairai”.
Shi kuwa Sheykh cikin sanyi yace.
“Ummi ni wannan al’adarfa ba sonta nakeba, kada asa min ƴa a kwarya”.
Da sauri Gimbiya Aminatu tace.
“Jakadiya fita harkar shi ɗauki ƴar ki kaiwa Lamiɗo gashi tafi da mabiyiyar kije ki benneta inda ake binne na ƴaƴan ɗakinsu”.
Da sauri tace. To.
Shi kuwa Sheykh a hankali yace.
“Ummi a bari in mata wonka”.
Bata kulashi ba ta fita.
Ganin haka ya miƙe ya kamo hannun Shatu.
Bedroom ɗinta Suka shiga, kai tsaye Bathroom Suka wuce, suna shiga ya ajiyeta kan toilet,
ai kuwa sai ga jinin yana zubowa.

Ita kuwa Gimbiya Aminatu tattare wurin tayi kana da sauri tabi bayansu.
Tana zuwa bakin ƙofar tace.
“Kai buɗe ƙofar ka fito”.
Cikin nitsuwa yace.
“Wonka zatayi.”
Tura ƙofar tayi ta shiga tare da cewa.
“Bani wuri”.
Shiru yayi ya koma gefe,
ita kuwa Gimbiya Aminatu a nitse ta juyo ta kalli Shatu dake zaune.
“Yanzu taso kizo kiyi wonka”.
Cikin sanyi tace.
“Toh a haɗa min ruwan zafi”.
Da sauri Gimbiya Aminatu ta girgiza mata kai tare da cewa.
“A a ai mu al’adar masarautar Joɗa mace in ta haihu bata wonka da ruwan zafi bazataci abinci mai zafiba bazatasha abin sha mai zafiba.
Komai da abu mai sanyi zatayi amfani.
Jaririnma muddin na mijine to da ruwan sanyi za’ayi mishi wonka in macece muke ɗan tarfa na ɗumi kaɗan sabida bamu sai ita ina rabo zai kaitaba”.
“Ikon Allah sai kallo waito wasu tsarabe-tsaraben sai yaushe za’a barsune a saki al’ada a kama gsky”. Ya hafaɗa yana taimakawa Shatu ta shiga wurin wonkan.
Kana yayi gefe.

Ita kuwa Shatu kasan cewar ta gaji yasa bata ce komaiba.
Wonka tayi kana ta fito.
Suna fitowa Gimbiya Aminatu ta koma falo, shi kuwa a hankali ya jawo hannunta, bakin gado ya akiyeta, kana a hankali yace.
“Ɗan gyara inga ko baby ta ƙaraki”.
A hankali ta ɗan kwaɓe fuska, kanshi ya jujjuya alamun kiyi haƙuri.
A hankali ta ɗan zame ta konta, towel ɗin ya ɗan ja, kana ya sunkuyo, da sauri yace.
“Akwai ƙarin amman ɗan ƙanƙanine ɗan kaɗan yanzu kici abinci mu tafi Valli muyi ɗinki”.
Ya ƙare mgnar yana gyara mata towel ɗin.
Da sauri Ummi dake bakin ƙofar tace.
“A a ba’a buƙatar ɗinki zai haɗe da kanshi”.
Shiru yayi yana kallon Ummi sai kuma ya miƙo hannunsa ya amshi Babyn.
Wacce anyi mata wonka an naɗeta cikin rawanin Lamiɗo.
Murmushi yayi, tare da matsowa gefe ya zauna a bakin gadon.

Ita kuwa Ummi taya Shatu kimtsawa tayi.
Kana tace.
“To zauna bari in kawo miki abinci”.
Da sauri ta kwanta tare da lumshe ido kana tace.
“A a Ummi barshi wlh bacci nakeji sai nayi in na tashi zanci”.
Jin haka yasa tace.
“Toh.”

Har zata fita sai kuma ta tsaye jin yana cewa.
“Uhummm Ayyah Ummi a bani zam-zam da dabino mana”.
Da sauri tace. “Toh”.
Ba kowa a falon haka yasa taje ta ɗauko danino da zam-zam ta kawo mishi kana ta juya ta fita.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya ɗan malle marfin zam-zam ɗin yasa a bakinshi yasha da kyau.
Kana ya buɗe kwalin dabinon.
“Bismillah”. Yace kana yasa dabinon a baki, ya tattaunashi da kyau.
Ya haɗe da damshin zam-zam da yawunshi ya tsastsafo da ruwan zaƙi da ɗan-ɗanon da binon.
A hankali ya sunkuyo ya kawo bakinshi kusa dana yarinyar,
ita kuwa Shatu ido kawai ta zuba musu.
Da sauri ta kalleshi jin an fara kiran sallan magriba.
Shi kuwa bakinshi ya manna kan na yarinyar ya rinƙa tura mata ruwan dabinon, ai kuwa sai gashi tana laluma tana haɗiyewa, murmushi yayi tare da juyowa ya kalli Shatu a hankali yace.
“Uhumm Bubbuga Rumbun Abboi ta haifo bubbuga Rumbun Sheykh dan ke ta gado da ciye-ciye”.
Murmushi mai cike da jin daɗi tayi tare da cewa.
“Allah Junainah ce uwar kwaɗayi da kuma Jamil to ta gaji ƙanin ka da ƙanwata”.
Murmushi ya kumayi yanaji a ransa yanzu dai sun gama zama abu ɗaya.
Haka yayi ta taunar dabino yana bata ruwan saida ya tauni tabino bakwai.

Amfanin fara bawo yaro dabino a matsayin abinci na forko da zai fara ci a duniya yana da yawa.
Ɗaya daga cikin wanda manyan likitocin duniya sunyi ittifaƙi a kai kuma sun gamsu dashi shine.
Sun gano duk wani abinci da na sha a duniya kab in ɗan adam yaci, sai sun fara zama a ciki uwar hanji ta bambance ta fidda mai kyau da mara kyau kana ya sarrafu ya zama jini kafin nan zuciya kuma ta harba ta rabashi ko wani sashi da saƙo na jikin ɗan adam.
Sai dabino ne abinci ɗaya da likitocin suka tabbatar da cewa.
Shi muddin ka cishi kai tsaye ƙoƙolwar ɗan adam yake wuce, ya wonketa ya in ƙantata.
So bada ruwan dabino ga jariri yana sa yaro ya tashi mai kaifin basira da ilimi da kwarin ƙoƙolwa.
Yayinda mutane kuwa ke cewa.
Yaro zaiji mgnar wanda ya shayar dashi ruwan dabinon da yawunsa fiye data kowa.
Wannan shine bayanin da Sheykh yakewa Shatu yana mai kontar mata da jaririyar kusa da ita.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Masha Allah”.
A hankali ya ɗan shafa kanta kana yace.
“Bari in tafi masallaci”.
Ya ƙare mgnar yana fita.

Ita kuwa ido ta zuwaba ƴar tasu.
Shi kuwa tv ya kashe kana ya nufi falonshi.

Ummi kuwa tana kitchen zabbi take gasawa waya na saƙale a kunneta Umaymah taketa kira tun ɗazu amman bata ɗagawa.

Katse kiran tayi ta kira Juwairiyya tana ɗagawa tace.
“Juwairiyya Shatu fa ta haihu”.
Cikin tsananin jin daɗi Juwairiyya dake bisa sallaya tace.
“Kai Ummi Alhamdulillah masha Allah me muka samu?”.

“Ɗiya mace”.

“Masha Allah bari inyi salla inzo”.

Galadima kuwa yana komawa Side ɗinsa ya gayawa matarsa.

Ita kuwa Ummi Umaymah ta kuma kira, bugu ɗaya ta ɗaza da sauri tace.
“Assalamu alaikum al’bishirinki Umaymah”.
Cikin dariya mai cike da zallar jin daɗi da farin ciki tace.
“Goro Ummin Jabeer amman Lamiɗo ya rigaki, yanzu yake gayawa Jaddanmu kinsan su Mamma da Aunty Rahma sun zo shekaran jiya, nima tun jiya ina Katsina.
To yanzufa Jadda ya shigo yake gaya mana kai Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!.”
Cikin dariyar jin daɗi Ummi tace.
“Eh lallai Lamiɗo yamin shigar saurin”.
Sitti ce ta amshi wayar tare da cewa.
“A a kada ki damu goron Al’bishir ɗinki na musamman ne”.
Aunty Rahma dake gefene tace.
“Ummi yar da waye take kama”.
Da sauri Ummi tace.
“Wlh da Ishma take kama”.
Mamma ce ta amshi zancen da cewa.
“Allah sarki yadda take son Ishma haka Allah ya bata mai kama da ita”.
Dariyar jin daɗi sukayi dukansu da yake wayar a amsakuwa take”.
Daga nan Ummi ta ƙatse kiran ta nufi falon.
Ɗakin Shatu ta fara shiga murmushi tayi ganin Shatun na konce tanata kallon yarinyar tana mata tofi.
Fita tayi ganin bata gantaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button