NOVELS

GARKUWA PART 3

Hajia Mama kuwa gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi da masifar takaici da tsanar Shatu da abinda ta haifa dama wanda ya bada cikin dan sune gagararrunta.

Cikin takaici ta miƙe ta fita. Hadiman ta na biye da ita a baya.

Wani irin murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Ɗan Adam kenan mugun icce kai dai kaga mutun baka san me accikin zuciya nai ba”.
Cikin mamaki Aunty Amina tace.
“Ikon Allah kai wannan gida naku yana cike da sarƙaƙiya”.
Da sauri Ummi tace.
“Sosai ma kuwa”.

Har bedroom ta wuce.
Zaune ta sameshi bisa bakin gado.
Da sauri ya buɗa mata hannunshi, ba musu ta raɓa jikinshi.
Ruggume ta yayi tare da sauƙe numfashi a hankali yace.
“I miss you so much”.
Ƙamshin jikinshi ta shaƙa tare da cewa.
“I miss U to”.
Gyara rungumar da yayi mata yayi, tare da amsar Baby cikin manna mata kiss a goshi yace.
“Baki tambayi sunan ta ba”.
A hankali tace.
“Kayi mata huɗuba ne?”.
Da sauri yace.
“Tuntini ma tun randa nace miki ko kinada sunan da kike son saka mats, kikace insa sunan Mamey duk da ban gaya miki wacece itaba”.
A hankali ta manna kanta da ƙirjinshi tare da cewa.
“Toh ai nasan itace mafi ƙololuwar soyuwa da daraja a wurinmu, tunda koda ban santaba baka gaya min komai a kanta ba.
Na fahimci tafi ko wacce mace daraja a garemu, tunda in kaji wuya ita kake kira kana raki in kaji daɗi ma ita kake fara tunowa.
Nasan tanada matsayi na musamman a rayuwarmu”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Aish sarkin falsafa, to nasa mata sunan Mamey kamar yadda kikace”.
A hankali tace.
“Me sunan?”.
Murmushi mai sanyi yayi tare da yin ƙasa da murya yace.
“Aisha shine sunan Mamey na, kuma sunan matata sunan ƴata ta fari kuma”.
Cikin murmushi tace.
“Masha Allah sunan Ummey nama Aisha ne”.
Ruggume ta yayi tare da cewa.
“Iye zuriyar Aysha’s kenan”.
Da sauri ya zaro ƙaramar wayarshi.
Murmushi yayi ganin
3bala’i.
Da sauri ya ɗan janye jikinshi gareta.
Amsa kiran yayi tare da karawa a kunne tare da cewa.
“Uhumm ya akayi ne”.
Cikin huci Hajia Mama tace.
“Jahan wlh zan kashe mutanen nan baki ɗaya in huta”.
Da sauri ya miƙa ya nufi cikin Bathroom yana juyowa yana kallon Shatu cikin yin ƙasa da murya yace.
“Dame zaki kashesu?”.

A hankali Shatu ta bishi da ido, fahimtar kamar yana buƙatar sirrine baison tasan abunda zai tattauna a wayar ne yasa ta miƙe a hankali ta nufi side ɗin ta.
Bayan ta gyarawa jaririyar kwanciya bisa gadonshi.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya sauƙe ajiyan zuciya jin Hajia Mama na cewa.
“Wallahi nayiwa kaina al’ƙawarin tabbas ranar suna zan kashe ƴarinyar nan cikin buzun al’ada da za’a naɗeta, tabbas da ita zan fara kafin inbi ta kan uwar da uban su ƙannen dama a tafin hannuna suke, yayan kuwa majanunine”.
Cikin danne tashin hankalinsa yace.
“To wai meya hatsalaki hakane?.”
A fusace tace.
“Yanzu na baro ƙofar Sheykh wlh naje da garin batur a hannuna zan turawa ƴar shi a baki, wannan fitsarerriyar ƙauyen matar tasa ido cikin ido tace.
Kar a bani ƴarta ita bata so.
A gabana ta amshi ƴar ta fita inaga ɗakin shegen ustazun ta tafi”.
Cikin danne dariyarsa yace.
“To bari yanzu ina cikin uzuri anjima zanzo muyi mgnar dake”.
To tace kana ta katse kiran”.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya fito.
Ganin bata ɗakin ne ya sashi sauƙe ajiyan zuciya.
Yana murmushin wautar Hajia Mama
Ya fito falo.

Dai-dai lokacin kuma Junainah data shigo da tray’n breakfast ɗinshi ta ajiye bisa Dinning table.
Shiru tayi tana jin kukan tsuntsayen dake cikin Garden ɗin, a hankali ta juyo ta sauƙa kan steps ɗin.
Ganin tsaye ne yana kallonta yasa ta ɗan matsoshi.
A hankali tace.
“Hamma Jabeer wannan kukan tsuntsayen fa a ina suke?”.
“Cikin Garden suke nan baya”.
Da sauri tace.
“Ayyah dan Allah ta ina hanyar zuwa wurin yake”.
Cikin tsareta da ido yace.
“Zaki jene?”.
Kai ta gyaɗa alamar eh.
“Toh me zakiyi a can?”.
Ya kuma tambayarta
“Zanje inga tsuntsayen ne ina son kukansu daɗin ji”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Gacan hanyar muje in rakaki”.
Yayi mgnar yana yin gaba tana biye dashi a baya.
Dai-dai lokacin kuma Lamiɗo da Galadima da Abbanshi suna ciki can bakin ruwan waya sukeyi da Jadda.

A hankali ya tura ƙofar forko kana ya turo ta biyun.
Cikin sauri ta biyo bayanshi tare da cewa.
“Wow masha Allah”.
Sai kuma ta lumshe idonta tare da buɗa hannayenta, tana binshi a baya.
Juyowa yayi ya kalleta bisa alamu duk tana jin daɗin iskar dake kaɗawan.
A hankali ta fara juyi tana gaba.
Da sauri yace.
“Ke Junainah tsaya a nan”.
Ya faɗa lokacin data nufi inda ɗawisun su yake, da sauri ya nufota, sanin muddin bawai ya gabatar da ita gareshi bane zaiyi ta yagusheta sai in jinin masararutar Joɗa ce ita to nan babu abinda zasuyi mata.

Ita kuwa Junainah hango ɗawisun a gefenta ne, yasa tayi sauri ta nufi inda yake.
Shima ɗawisun kanta ya nufo gadan-gadan.
Da sauri Lamiɗo da Abba da Galadima suka zuba mata ido.
Shi kuwa Sheykh da sassarfa ya biyota yana cewa.
“Junainah! Junainah!! Dawo nan zai ji miki ciwo”.
Da ƙarfi ya rumtse idonshi lokacin daya hango ɗawisun ya iso gab da ita ya buɗe fikafikansa a zatonshi ya guneta zai farayi.

Ita kuwa Junainah wani irin murmushi tayi tare dasa hannun kan ƙunɗun ɗawisun ta fara shafawa, shi kuma fiffigensa ya fara kaɗawa yana jujjuyashi.
Da sauri Sheykh ya buɗe idonshi jin shiru sai dariyar ta da yake juyowa.
Lamiɗo kuwa da Galadima da Abbanshi da sauri suka miƙe tsaye suka nufosu cike da al’ajabin ganin ɗawisun ya fara zagayata kamar yadda yakeyiwa dukkan jinin masararutar Joɗa.

Zagayeta sukayi gaba ɗayansu suna kallon tsananin kamarta da Mameyn Sheykh.
Shi kuwa Sheykh cike da mamaki ya zuba mata.
Ita kuwa idonta a lumshe tana jin yadda Ɗawisun ke goga mata fikafikansa a fuskarta.
Cikin gamsuwa Lamiɗo yace.
“Tsuntsuwa tana shunshunar jinina”.
Da sauri ta buɗe idonta jin muryar mutun.
Shi kuwa Sheykh Jabeer hannunshi yasa ya kamo nata, da sauri ta matsoshi tare da cewa.
“Sannunku ina kwana”.
A hankali Abba ya ɗan matsota hannunshi yasa ya dafa tsakiyar kanta.
da sauri tasa hannunta kan nashi ta dafe hannun nashi a kanta.
Murmushi mai faɗi Abba yayi tare da cewa.
“Allah yayi miki al’barka”.
Cikin jin daɗi tace.
“Amin Amin Baba ngd”.
Shi kuwa Sheykh murmushi yayi fahimtar tarbiyyar su Shatu da Junainah ɗaya ne suna masifar jin daɗi in akayi musu addu’a da sanya musu al’baka”.
Da sauri
Galadima yace.
“Me sunanki?”.
Buɗe idonta tayi tare da cewa.
“Sunana Junainah Aliyu Garkuwa”.
Da sauri Lamiɗo yace.
“Shekarun ki nawa ne?”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kaka shekaruna fa da yawa”.
Murmushi Abba da har yanzu hannunshi ke bisa kanta yayi tare da cewa.
“Gaya mana mana”.
Cikin nitsuwa tace.
“13”.
Wani irin dogon numfashi mai nauyi Abba ya sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ta janye hannunshi daga kanta cikin sanyi yace.
“Uhumm yanzu abu biyu ya rage, muga ko tanada tambarin jinin masarautar Joɗa a tsakiyar kanta kana muga mahaifiyarta”.
Da sauri tace.
“Ummey na tana gida, bata zoba”.
Cikin son fahimtar manufar Abba Sheykh yace.
“Kuma kuna irin zaton da nakeyi ne?”.
Da sauri Lamiɗo yace.
“Aimu namu ma yafi naka ƙarfi”.
A hankali yace.
“Toko dole mubi komai a hankali”.

Kai suka jinjina kana Sheykh ya nuna mata hanya tare da cewa.
“Koma ciki ina zuwa”.
To tace kana ta juya ta tafi.
Su kuwa zama sukayi.
A nan Sheykh yake basu lbrin batun ƙarar da ya shigar kan case ɗinsu Gaini.
Tuni Affan kuwa ya tattara dukkan hujjoji da shaida a matsayinsa na lawyer mai cikar ƙwarewa.
So yama tafi shida Sulaiman da Malam Abubakar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button