NOVELS

GARKUWA PART 3

Da sauri ta juyo bayanta jin Junainah na cewa.
“Lah Oyoyo Dedde”.

Dai-dai lokacin kuma Ummey ta ƙarasa shigowa ciki wanda hakan yayi dai-dai da bugawar da kanta yayi wanda saida tayi sauri sa hannunta duka y ta damƙe kanta da masifan karfi tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Da ƙarfi wanda haka yasa Dedde juyowa ta fuskanceta sanadin juyawar da Dedde tayi kuma ya bawa Aunty Rahma da Junainah damar ganin fuskar Ummey da kyau.
Wani irin sauri Junainah tayi ta nufi inda suke ganin yadda gaba ɗaya jikin Ummeynta yake karkarwa da tsuma.

Aunty Rahma kuwa cikin wani irin tsananin firgita da kaɗuwa ta zazzaro idanunta waje har kamar zasu faɗo.
Wani irin taku mai cike da firgici tayi tana matsowa gaban Ummey dake jujjuyawa tana mai-mai-ta.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil”.
Wani irin matsowa kusa da ita Aunty Rahma tayi tare da buɗe baki da ƙarfi tace.
“La ha ila ha illahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama. Aunty Mamey!.”
Ta ƙarashe kiran da azaban ƙarfi da rakaɗi.
Ummey kuwa.
Kiranta da Aunty Rahma tayi yasata ƙara gigicewa.
Karkar haka jikinta ke rawa.
Cikin wani irin gigitaccen murya Aunty Rahma ta fara rabkawa ahlinta kira.
“Umaymah! Mamma Jazlaan ga Aunty Mamey ta dawo da izinin ubangiji Jazlaan, Jafar, Jalal, Jamil, Umaymah. Kuzo ga Aunty Mamey…”.
Wani irin azabebben zabura…!

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k ne kacal zaki turo ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Normal group Kuma 300 zaki turo ta asusuna ɗin sai kuyi screenshort na Debit Alert din ku turo min ta whatsApp 09097853276.

                     By
         *GARKUWAR FULANI*

4/6/21, 4:15 PM – &: “Aranar wata jumma da da wanna Zazzafar ƙaddara ta rufta damu shekaru goma sha uku baya.”
Sai kuma ya ɗan tsakaita
tare da jan
sassayan numfashi ya gyara
zamansa tare dasa tafin hannunshi ya share hawayensa.
Yayin da gaba
ɗayansu kacokam
suka mai da hankalin su kansa,
Duk sun ƙagu suji yadda a kayi a wannan ranar da basu manceba.
Shi kuwa Yah Jafar wani numfashin yakuma.
Saukewa kana yaci gaba da cewa.
“Ranar da dare bayan anyi sallan isha’i duk muna falon Mamey dani dasu Jalal Jamil Affan da Ummi da Imran yana ɗan sheksru takwas lokacin.
Anan mukaci abinci kana muka zauna muna hira.
Kasan cewar akwai shaƙuwa mai tarin yawa tsakanin Mamey da Affan da yake tana da son yara.
Amman son Affan da banne a wurinta har su Jamil kance wa Affan na hannun daman Mamey.
Takanyi Dariya tace.
“Eh ɗin ai ya fiku nitsuwa”.
Muna zaune sai hamma Mamey keyi tare da miƙa da lumshe idonta hakane yasa tace mana.
Duk ta sallamemu saida safe tanajin bacci.
Ummi tace.
To.
Still Kuma sai mukaci gaba da hira.
Da ido muka bita ganin ta miƙa cikin sanyi tace.
“Kai zanje inyi bacci wlh wani irin bacci mai nauyi nakeji yana fuzgata tamkar zan faɗi.
Ni na shiga saida safenku”.
Allah ya bamu al’khairi mukace dukanmu kana ta shiga.
Tana shiga kwanta ko second uku batayi da kwanciya ba tayi bacci.
Mu kuwa muna gama hira muka watse.
To su Jalal ne ƙarshen fita ashe basu tasheta ta rufe ƙofarta ba a famintata kenan fa?”.
Ya ƙare mgnar yana kallon su Jamil.
Da sauri Jamil yace.
Eh.
Cikin sanyi ya kalli su Lamiɗo kana yaci gaba da cewa.
“Ina komawa ɗaki na kira Juwairiyya muka fara hira a waya kamar kullum.
To bayan mun gama
waya da Juwairiyya
har na kwanta sai na mike na nufi
ɗakin Mamey dan
inaso nayi mata magana a kan Juwairiyya fa tasanar wa mahaifin su maganar auren mu da ita, tun da lokacin takammala
karatun ta dan haka itama ta gayawa Abba na ayi batun aurenmu dan nima tuni lokacin na gama karatuna har na fara aiki.
Kuma a kwanakin ne aka bani sarautar Galadima wanda da mijin Gimbiya Saudatu ce mai matsayin to daya rasune Lamiɗo ya maida mulkin kaina.
A zatonshi ta hakane zaisa yaranshi bazasuyi faɗa da junaba tunda bazasuce ya baiwa wane ya hana waneba.
Ni a lokacin dagani har Mamey da Jabeer da baya ƙasar ma ba son wannan mulkin mukayiba bisa dole aka bani ita.
Sai kuma ya jingina bayanshi da kujera kana yaci gaba da cewa.

Ina isa bakin kofar
Mamey natura kofar da sallama nashiga ɗakinta.

Da sauri naja natsaya nan bakin kofar.
Can na hangi Mamey na kwance.
Bisa gado tana bacci da alamun baccin mai nauyi ne.
Hajiya mama kuwa na tsaye a kanta da wata iriyar shiga da tafi kama data bokaye ko ince matsafa.
Da mamaki nake kallon
Hajia Mama dake tsaye bakin gadon sanye da wasu irin jajayen kaya tun daga samanta har ƙasa,
kanta babu ko ɗan kwali
hannunta rike da wani ƙwarya.
Tana yayyafawa Mamey
wani ruwa dake cikin ƙwaryar tare da yin wasu surutai da sukafi kama da surkullen matsafa.

“Innalillahi wa’inanna ilaihirraji’un, nafurta da karfi.
Da sauri nanufo in da Hajia Mama’n ke tsaye cikin ruɗani da kiɗima ina faɗin.
Meye hakan Hajia Mama? me kike mata? me kike zuba mata a jiki haka?.
Dasauri tajuyo kaina tasaka hannunta cikin ƙwaryar taɗibo ruwan tashiga watsamin tana ƙara matsoni,
kaucewa nashiga yi ina matsowa in da Mamey take kwance kamar gawa ko matsi batayi,
itako Hajia Mama masoni tarikayi tana watsamin ruwan,
Baki na buɗe da karfi sabida wani irin masifeffen suka da naji duk inda ruwan ya taɓa a jikina yanayi.
Ƙara watsomin tayi wanda yasa na ƙara kaucewa da sauri tare da buɗe baki da nufin yin ihun zafin da nakeji da kuma fargabar halin da Mamey na ke ciki.
Sai kawai naji harshena yafurta Innalillahi wa’inanna ilaihirraji’un,wannan kalmar narika nanawata da karfi madadin inyi ihu.”

Ita kuwa Hajia Mama da sauri tajuya cikin alamun tsoron tonuwar asirinta.
dan lokacin dare baiyi nisa sosai ba misalin ƙarfe goma ne,
da gudu tafita a ɗaki dan jin yadda na kara sautin salatin da nake.

Ita kuwa Hajia Mama tana fita part ɗinta ta nufa direct bathroom ɗinta ta shiga gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi number’n bokan ta takira yana ɗagawa cikin haki da fargabar a bin da zaije ya da wo tace.
“Boka yanzu nafito daga ɗakin matarnan na samu tayi bacci kamar yadda kace, kuma na watsa mata ruwan bata farka a sai daifa wani yaganni lokacin danake yayyafa mata ruwan maganin nan babban ɗanta Galadiman Masarautar Joɗa kenan ya ganni”.
Wani irin dariya irin nasu na hatsabibai bokan yayi kana yace.
“Toh daya ganki me yakeyi? me kuma yake cewa?”.
cikin rawar baki da soron da ya ziyarce ta gudun kada ai kin ya ɓaci tace.
“Sunan Allah yaketa ambata salati yaketayi babu ko kakkautawa da wasu addu’o’i”.
Cikin ɗan tsagaita dariyar mugayen bokan yace
“To aiki kam zaici amma dai akwai nakasu aciki, amma kada kidamu yanzu shi yaron zamu rufemasa baki zai dauwama kurma ba mgna a bakinsa bazai iya yin maganaba bazai iya furta komai ba haka zai dauwama ba mgn saidai yayi ta mai-mai-ta abinda yake cewa.
Sannan daga nan tagwayen kuma zamu haɗa ɗaya da bin mata ɗaya shaye-shaye shi kuma babban kinga zai zama kamar Mahaukaci, shi kuma wancan Jabeer ɗin na gaya miki tun yana ƙaramin akwai sihirin da wani yayi mishi kada ki damu dashi bazai taɓa yin aureba har gaban abadan ko an mishi bazai zauna da matarba, kinga kenan duk sun zama suna da matsalar da dole baza’a basu mulkiba sai dai a bawa ɗanki Affan tunda kinga shi Imran ɗan ɗaya kishiyar taki shine ƙarami kan Affan.”
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Yauwa boka na gode ni dama fatana ɗana yayi mulki dan bana son mulkin ya bar ɗakina tunda dai kace min tabbas cikin yaran Habibullah ne mijin wani zai gaji kakansa sarauta.
Dariya yayi tare da cewa.
“Kada ki damu mulki na gareki da ɗanki”.
Wa iyazubillah kaɗan kenan daga sharrin tsinannun shaiɗanu maƙiya Allah da Manzonsa bokaye taɓaɓɓu masu sa mai binsu ya taɓe ya gaza sauri a ranar da muminai ke sauri a bisa siraɗi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button