NOVELS

GARKUWA PART 3

Sai kuma ya kife kansa a jikin kujera yaci gaba da kuka yana mai cewa.
“Yana gaya min haka ƙanne shi ma suka matsoni sukace su sun san tasu ta ƙare a ciki amma zasu tsaretar dani.
A haka a gabana inaji ina gani aka fitar dasu woje, aka jera bindigogi da makamai da kuɗaɗen a gabansu, kana aka dasa musu camera bayan an gaya musu abinda zasuce.
Anan ake tambayarsu ku su wayene.
Cikin bushewar zuciya ganin sharrin da akeyi musu ido na ganin ido sukace.
“Mu ƴan kinnafin ne”.
Kana aka sake cewa.
“Ku wanne yarene?”.
Sukace.
“Mu fulanine”.
Wlh sai gashi wanda suke ciki kusa dani suna dariya suna cewa.
“Shegu fulanin dole sai mun koreku a kasar nan mun hanaku jin daɗi mun ɓata muku sunan ƙabilar shugaban ƙasar namu hegen bafullatani”.
Hankalina ya tashi dana gane wai ashe duk anayin hakane dan a ɓata sunan fulanin a dozarta ƙabilar shugaban ƙasar to amma. Alhamdulillah tun daga ranar aka dena dukansu da wahal dusu”.
Wani nannauyan numfashi suka sauƙe gaba ɗayansu suna masu zubda hawaye.
Cikin rauni Sulaiman yace.
“To tashin hankali na yaune za’a haska video da kayiwa yaran a nuna duniya cewa sune ɓarayin mutane”.

Tofa wannan al’amari yayi masifar tada hankalin Sheykh yayi kukan da shi kanshi bai san yaushe rabonsa da yinsa ba.

Ganin ƙarfe ɗaya ta wuce ne yasa ya sharce hawayensa, murya a disashe yace.
“Zan tafi Malam, amman in sha Allah zan meda hankali na kan batun yaran nan, in Allah ya yarda zan sasu cikin addu’o’i na.
Zan kuma roƙi duk limamen masallacin jumma’a su sasu a addu’a.”
Cikin tsananin jin daɗi Sulaiman da Malam sukace.
“Allah ya yarda ya bamu sa’a, ya tsaresu al’farmar Annabi da al’ƙur’ani ya fito dasu lfy”.
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya tafi.

Daga nan kai tsaye makarantar su Shatu ya wuce ya ɗaukota.

Ta lura yana cikin tashin hankali kuma duk jikinsa a mace.
To amma ganin lokacin salla yayi ne yasa batayi mishi mgn ba.

Suna dawowa ta shiga ɗakin ta, shi kuwa al’wala yayi ya fita.

Bayan an idar da salla kuma wurin Lamiɗo ya shiga ya mishi duk bayanin da Sulaiman yayi mishi.
Wannan ne yasa baiyi baccin tsakanin azahar da la’asar ba.

Kiran salla ne ya medasu masallaci.

Ita kuwa Shatu koda ta shiga wonka tayi kana tayi salla, akan sallayar ta miƙe, dan ta gaji.
Ummi kuwa jin motsinta ne yasa taje ta kai mata abinci.
To nanma da kyar taci kaɗan kana ta koma ta konta.
Itama Ummi ta koma ɗakinta.

Saida tayi sallan la’asar ne ta fito ta nufi kitchen ita da Sara.

Ita kuwa Shatu cikin ɗan jin sauƙin gajiyar ta miƙe doguwar riga ta zura kana ta fito, falonta.
Har kamar zata wuce babban falonsu kuma sai taji ƙafarta ta riƙe wanda yafi wata da fara mata hakan.
A hankali ta ja ƙafar ta isa gaban kayan kallon, hannu tasa ta kunna TV inda ta samu tashar BTV a kunne anayin zabi sonka.
A hankali ta koma baya ta zauna bisa kujera 3 str, tana fuskantar tv murmushi tayi tare da cewa.
“Oh ikon Allah ashe har yanzu anayin zaɓi sonka”.
Zama tayi tanajin ana gaishe-gaishe bayan minti biyar asa waƙa tayi minti biyar a cireta.
Ƙarfe biyar dai-dai aka gama shirin.

Shi kuwa Sheykh ana idar da sallan la’asar ya nufi gida,
tafiya yakeyi cikin yanayin tsantsar dauriya da danne tsananin halin da yake ciki.
Sabida wani irin masifeffen sarawa da ƙugunsa yake har sai yaji ƙahon zuciyarshi ya bada sautin ras-ras wata iriyar fitinenneyar zuface mai azabar zafi ce ta keto mishi tana tsastsafo mishi tako wani hudan gashin jikinsa.

Da sauri ya tura ƙofar falon ya shiga.
Ba kowa sai wulgawar Ummi daya hango ta shiga kitchen.
Yah Jafar kuwa gidanshi ya nufa.
Jalal kuwa yau kwana ukuma kenan baya gida.
Jamil kuwa tun safe daya tafi wurin aiki bai dawoba.

Wani irin azabebben karkarwa jikin shi ya farayi da tsuma sabida azabar ciwon da bai taɓa jin makamancinsa ba.
“La’ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama”.
Haka yake maimaita kalmar shahadar sabida jin tamkar ciwon zai ɗauke ransa.
So yake ya zaro wayarshi ya kira, Shatu ko Umaymah ko Abbanshi ko Lamiɗo ya gaza wani irin raunine ya rufeshi wanda yasa hawaye fara kwaranyo mishi, cikin zuciyarsa yake tunanin shike nan zai rasu ba tare da burinshi ya cikaba zai tafi matarsa bata haifuba zai bar ɗansa maraya.
Zai bar su Jalal cikin makirin masarauta.

Wani irin rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi tare da taune lip ɗinsa na ƙasa.
Kar-kar haka jikinsa ke karkarwar.
Babu abinda yake cewa sai maimaita kalmar shahada, wani irin jujjuya kai yayi ya tafi luuu ya…!

Ita kuwa Shatu, a hankali ta sunkuyar da kanta ta ɗaura hannunta bisa cikinta.
Tana jin yadda ɗan cikin ke jujjuyawa.
Da sauri ta ɗago kanta ta zubawa tv Ido, jin ɗan jaridar na cewa.
To masu kallo barkanmu da war haka yau dai gamu tare da SP Daniel tare da rahoton ƴan kinnafin ƴan bindiga daɗi, daga babbar het kotansu na babban birnin tarayya, zaku kalli video ƴan kinnafin ɗin kana muji ƙarin bayani daga SP Daniel
Ido ta zubawa allon tv lokacin da aka fara haske makaman dake jere gabansu Yah Giɗi Seyo Gaini da wasu matasan fulani waɗanda aka kamo kamar yadda aka kamosu.
Ana cikin nuna makaman, ana jefa musu tambaya.
“Wato wannan shine makaman da kuke amfani dasu a matsayin ku na masu GARKUWA da mutane?”.
Dai-dai lokacin kuma ake haska camerar kan fuskar Yah Gaini wanda duk sauyin da zai samu a duniya bazata gaza ganeshi ba.
Ana ƙarasa haska fuskarshi da fuskar Yah Seyo da Giɗi.
Tayi wani irin yunƙura da azaban ƙarfi zuciyarta kuwa tayi wani irin azabebben tsinkewa da masifan karfi.
Wani irin azabebben juyi ɗan cikinta, yayi gaba ɗaya jikinta karkarwa ya farayi kamar wacce aka jonawa wutar lantarki.
Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfi tare damke cikinta, ta buɗe bakinta da azabar firgita da karfi ta kurma wani irin azabebben kuka mai haɗe da ihu da kiran sunan.
“Yah Giɗi Seyo Gaini wlh ƙaryane. Sherri akeyi maku innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil wayyoooooooo Bappa wayyoooooooo Ummey na Yah Sheykhhhhhhhhhhhhh…!

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 zaku tura ta Account 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na Debit alert ɗin ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276 ƴan 300 ku in baki da damar biya ta Account ku sayi katin Mtn na ɗari uku kacal ku copy numbers ɗin ku turo min ta whatsApp 09097853276. Banbancin special Group da Normal group q yawan posting ne.
Special Group su yanzu muna gab da ƙare littafin da izinin ubangiji.

                      By
         *GARKUWAR FULANI*

4/6/21, 4:15 PM – &: Ina masoya na ????️????️????️????️????️ina masoyan littafin GARKUWA ?
To ku marmatso kusa don ina da babban albishir a gare ku. Hazikar marubuciyar nan Mai suna RUKAIYA IBRAHIM GAWATA marubuciyar littafin ” Cikar buri na ” ta zo muku da wani littafin mai suna “ZURI’A BIYU”.
Zuri’a biyu ya zo da sabon salo mai ban mamaki da daukan hankalin Mai karatu, littafi ne da yake kunshe da fadakarwa, tunatarwa ilmantarwa, tare da nishadantarwa. “ZURI’A BIYU” sunan littafin na GAWATAN GARKUWA
Kada Ku bari a baku labari….????????????????

“Yah Sheykhhhh”. Ta ƙira sunansa da ƙarfi da kuma karaji.

Wani irin juyowa Ummi dake kitchin tayi da sauri cike da tsaro ta nufi falon nasu cikin ruɗani da gudu.

Shi kuwa Sheykh jin muryarta da yadda ta zurma ihu da rakaji, yayi dai-dai da lokacin da yaji wani irin masifeffen azaban sarawa da ƙugunsa yayi, tare da harabar jijiyar bayanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button