NOVELS

GARKUWA PART 3

Cike da alhini suma su Lamiɗo suke kallon yatsun kafar nata, hankali a tashe.
Cikin gigita Abba ya kamo hannunta tare da nunawa Lamiɗo murya a daburce yace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun Lamiɗo kalli yatsunta”.
wani matsanancin tashin hankalin ne yakuma dabaibayesu lokacin da suka ga yatsun hannunta yafara komawa irinna fiffiken tsuntsu.
Gaba ki ɗaya su haɗa baki sukayi wajan furta “innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un hasbullahu wani’imalwakin”. Sabida tsananin firgici da tashin hankali gaba ɗaya jikinsu rawa yakeyi.

Cikin matsanan cin tashin hankali Lamiɗo da cushewar tunani Lamiɗo ya juyo ya kalli Galadima murya a hargitse yace.
“Subahanallahi maza a kira Malam Musa yanzu nan”.
Cikin hanzari Galadima ya amsa da. “To”. Kana yajuya da sauri yafita.

Kan kace me labari yabaza masarautar Joɗo,
Batare da bata lokaci ba sakon kiran da Lamiɗo yayiwa Malam Musa ya isa gareshi.

Cikin ƴan daƙiƙu malam Musa ya iso cikin masarautar Joɗa Lamiɗo yabada umurnin a shigo dashi har cikin ɗakin Mamey.

Yana shiga kallonta malam Musa yayi cikin tashin hankali ya girgizata kai kana yakallesu Lamiɗo yace.
“Sihirine a kamata mai haɗe da tsafi kuma daga yanzu zuwa ko yaushe ko wanne lokacin zata iya juyewa daga mutun ta dawo tsunsuwa”.
Salati suka ɗauka baki ɗayansu nan kuma ɗakin yakacame da koke-koke su Jamil da Jalal Affan Ummi Jafar yayin da duk muryar Hajia Mama yafi amo wajen kuka da shiga tashin hankali ziraran miraran.
(uhum makircin mugu kenan.)
(Sai daifa akwai kishiyoyi na gari da matsalar kishiya kan sasu kukan gaske wlh.)

Ranar kuwa wannan masarautar taga tashin hankali mara misaltuwa,
Jiƙe-jiƙe da hayaƙi da shafe-shafen magungun gargajiya babu wanda malam Musa baiba, kiɗima yasa sun mance da suyi amfanin da ayatul shifa.
Ganin anyi duk abinda za’ayi na gargaji abin yaci tura ne yasa hankalin.
Dr Aliyu yakasa ƙwanciya gani yake ko wata cutarce ta da ban haka yasa ya fitadaga ɗakin yatafi part ɗin sa,
kiran wasu manyan likitoci a bokansa.
Yasanar musu koda wani shawarin da zasu basu bayan sun gama wayar kuwa.
Kayan ai kinsa ya ɗauko yakomo ɗakin Mamey’n yayi iya gwaje-gwajen sa babu abinda ya gane na wani cuta ko wani abu.
Cikin takaici Malam Musa yace.
“Kama bar gwada ta babu wani cuta face sihiri”.
Daga karshe dai dole ya hakura.
Ranar babu wanda ya rumtsa kusan a tsaye suka kwana nan cikin ɗakin Mamey’n ganin yadda gaba ɗaya kamannin halittarta ke juyewa, Gimbiya Aminatu tayi kuka iya kuka.
Lamiɗo ya kira Jadda ya sanar mishi halin da ake ciki tashin hankali iya tashin hankali Jadda da Sitti sun shigeshi nan suka fara shirin tahowa.

Can gabanin kiran sallar asuba lamari ya ƙara munana dan a lokacin suffar Mamey ta gama juyewa izuwa na tsunsuwar Boleru a gabana a gabansu Lamiɗo a gaban mafiya yawan al’ummar Masarautar Joɗa.
nan take kuwa Abba ya yanke jiki yafaɗi yasuma.
Cikin kiɗima Dr Aliyu yayi kansa yafara bashi taimakon gaggawa.
Mamey kuwa da yanzu takoma tsuntsuwa fara kaɗa fiffikenta tayi alamun son tashi take.

Ai kuwa tamkar al’mara sai gashi ta tashi firr ta fire tabi ta window dake a buɗe tayi tacikin Garden tashige cikin tawagarsa tsuntsayen dake wurin.

Innalillahi Jamil Jalal kuwa suma sumewa sukayi.
Cikin hanzari da kiɗima Lamiɗo da Galadima suka zo jikin window nan suka hango ta ta sauka cikin tsuntsayen kawai sai suka fashe da kukan tsoron al’amarin duniya.

Wani irin kuka Hajia Mama tasaka tana faɗin “wayyo Allah na waishin meke faruwa damune kam”.
sai kawai ta yanke jiki tafaɗi ta kakkafe idanunta kamar wacce ta suma.

Ranar Hajia Mama haka tawuni tana kuka ta rungume Jamil da Jalal dasuke keta kuka kamar ransu zai fita.

Jadda da Sitti da Umaymah da Aunty Juwairiyya da babanta duk a ranar sukazo.
An kamo tsuntsuwar Boleru suna killaceta, yayinda aketa tururuwan zuwa ganin tsuntsuwar.

Ido da ido da Gimbiya Saudatu tazo da yake sokuwace.
Sai cewa tayi.
“Allah sarki wato al’haƙi kuikuyo ko sharrinta ya dawo kanta, ohoho larabawa an zama tsuntsuwar Boleru”.
Toh fa daga nanne Magautan su Sheykh duk suka samu suka fake suka laɓe a bayanta.

Su kuwa haka sukaci gaba da kukan Hajia Mama ko uwartace ta mutu sai haka, duk wanda yaganta sai ta bashi tausayi akasin Lamiɗo da Galadima da suka sa zargi a kanta duk abin da take shirine da zallar iya tuggu munafurci da makirci.

Tun daga lokacin tsuntsuwar nan ko ince Mamey ko yaushe sai ana kamata ita kuwa tana firewa tana komawa cikin tsuntsaye ƴan uwanta.
Al’amarin ya magaga ya tada hankalin kowa.
Ana kamata zata zille ta fire ta koma cikin Garden ta zauna cikin tsuntsayen cikin masarautar Joɗa.

Duk wannan tashin hankali da ake ciki Sheykh Jabeer bashida labari dan lokacin yana karatu a jami’ar Madina sai dai kwata-kwata a lokacin hankalinsa yakasa ƙwanciya idan yakira wayar Mamey’n sai asa Aunty Rahma ta ɗauka tayi mishi mgn wanda ita kuma dama lokacin sun zo suna nan da Mamma.
Yadda Hajia Mama ke nuna tashin hankali tane yasa suka yarda da ita.

Wannan juyewar Mamey shine.
Sanadin da Jadda ya samu hawan jini kenan.

A ranar da dare Umaymah Mamma Aunty Rahma Aunty Juwairiyya Sitti duk sun gaza bacci, sun sa tsuntsuwar Boleru a gaba Magauta na musu dariya.

Sai da asubane sun kabbarta yin salla asuba, tsuntsuwar ta tashi ta fire, Bata tsaya cikin masararutar Joɗa bama ta fuskanci ƙasar Cameroon ta nausa tayi can yankin Yahunde.

Ɓacewar tsuntsuwar nan shi yafi tada musu hankali.
Anyi neman duniya har an gaji.
Ba ita ba dalilinta har dai aka ruggumi ƙaddara.

Sai dai Lamiɗo da Galadima da Jadda da Umaymah sunci gaba da bincikawa da neman mafita.

Lokacin da Sheykh ya kammala digirin sa na farko yazo.
Nigeria nan ne ake faɗa masa abin da ya faru a lokacin tashin hankalin da kiɗimar rayuwar daya faɗa ciki baya misaltuwa wani babban tashin hankalin kuwa shine daya iske ya Jafar baya magana sai addu’o’in da yin karatun al’ƙur’ani mai girma da kuka, dakuma ya buƙaci yaje yaga Mamey’n shi a yadda take ɗin a tsuntsuwar ta ɗin, nan ake faɗa masa ai tun lokacin da abun yafaru da kwana ɗaya rak ta fire tabar cikin masarautar Joɗa.

Ranar Sheykh kuka kamar karamin yaro ya rungume Jamil Jalal Yah Jafar da tun isowarsa Jafar ɗin ke ƙanƙame da hannun sa yana karatun yana kuka haka sukayi ta kuka Hajia Mama na tayasu.
Ranar tazamo musu tamkar sabuwa.

Tun daga wannan lokacin kuma sai yazamo kamar an cire hankalin Abba’n su a kansu madadin a lokacin ya janyosu jikinshi yazame musu Garkuwa dan suɗan sami sassaucin kunar dake cikin zuciyarsu sai yariƙa nisanta kanshi dasu.
Shi kansa bai san dalilin hakan ba,
duk wannan kuma acikin shirin Hajia Mama ce, kwana ɗayan da tsuntsuwar tayi tafire ma ita takoma gun bokanta tace tanaso tsuntsuwar tabar cikin masarautar gaba ɗaya dan taga sun dage da magungunan.
Dariya bokan nata yayi tare da cewa.
“Ke shar-shar banza da kika samu ma ba Addu’o’inku na musulmai sukeyiba ai da tuni sun karya sihirin”.
Cikin jin daɗi tace.
“Aini gaba ta kaini da hankalin su baije ga canba”.

Lamiɗo kuwa lokacin ya ƙara jan Sheykh a jiki sosai.
Sabida bayanin da Malam Musa yayi musu na cewar a sanadin aurensa da ba fulatanar daji mahaifiyarsu zata dawo.
Haka yasa part in da a ka bashi kusa da Garden inda tsuntsayen suke.
aka buɗe mishi wata kofa taciki in da daga cikin part ɗin direct zai sadashi da cikin Garden ɗin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button