NOVELS

GARKUWA PART 3

Suna shiga falonshi ya juyo ya ruggumeta gam-gam a jikinshi cikin sanyi yace.
“I’m so sorry afwan Mar’atussaliha. Wani aikin gaggawa ya sameni a Valli Hospital, wasune sukayi hatsari.
To biyu daga cikinsu sunada ciki, sun jikkata sosai dole sai anyi musu CS.
Dole yanzu zan tafi can.
Nasan ke kuma kin matsu mu tafi Rugar Bani, shiyasa na kira Baba Ado zai kaiki.
In Kuma zakiyi hakuri sai gobe muje tare to?”.
Cikin sanyi da tausayawa matan tace.
“A a Hamma Jabeer babu komai Baba Ado ya kaini, kaje ka taimakesu.
Sabida sun fini buƙatar ka a yanzu, tunda su ransu da lfyarsu zaka taimaka da abinda ke cikinsu.”
Ta ƙarashe mgnar da bashi ƙarfin guiwar yin aikinshi cikin nitsuwa”.
Lip ɗin ta na ƙasa ya sumbata tare da cewa.
“Masha Allah Mar’atussaliha, ngd Matuƙa da kekyawar fahimta. Allah ya miki al’barka in sha Allah nima zanzo”.
Ya ƙarashe mgnar yana zaro wasu sabbin kudin rafa-rafa ɗaurin dubu hamtsin-hamtsin guda biyu ya bata.
Kana a hankali ya sunkuyo ya durƙusa ya kife guiwowinsa a ƙasa.
Hannu yasa ya ture rigar jikinta sama.
Dai-dai kan hudar cibijiyarta ya mannawa kiss kana ya fara kissing ɗin cikin tako ina.
Ita kuwa Shatu ido kawai ta lumshe tare dasa tafin hannunta bisa kanshi.
Ya daɗe yana kissing cikin da sauri-sauri, kana ya manna kunnenshi bisa cikin tare dasa hannun ya zagaye ƙugunta.
A hankali ya fara karanto Ayatulkursi’u yana tofawa yana idarwa ya sake saida yakaranceta ƙafa bakwai kana yayi falaƙi 3 nasi 3 ƙulhuwa 3 ya ƙara da azubikalmatillahi har ƙarshe.
Ya tofe a cikin sannan ya taso. Ya ruggumeta tare da cewa.
“Allah ya kaiku lfy yasa ku samesu lfy ki gaida min Ummey da Bappa da kyau.
Akwai tsarabar Junainah tana cikin motar kice ina gaisheta”.
Cikin sanyi tace.
“Zasuji Ngd matuƙa Allah ya ƙara buɗi ya rufe asiri”.
Fuskarta ya shafa tare da cewa.
“Amin My dear bey’.
Yana faɗin haka ya juya ya fita.
Itama ta binshi a baya.

Da sauri Ummi ta miƙa jin yana ce mata.
“Toh Ummi mu tafi”.
Da sauri Ummi tace.
“Toh Shatu sai mun dawo”.
A hankali tace.
“Ummi nina yanzu zan tafi Baba Ado zai kaini”.
Dai-dai lokacin Baba Ado da Jamil suka shigo da sallama.
Ita kuwa Ummi cikin ƙarfin hali dason zuwa gidansu Shatu ta ƙiddigi zarginsu tace.
“A a Sheykh ba tare zamu jeba”.
Kanshi ya ɗan juyo kana a hankali yace.
“No Ummi kada ki damu zamuje ɗaukota yanzu dai Baba Ado zai kaita”.
Sai kuma ya juyo ya kalli Baba Ado a hankali yace.
“Baba Ado na yarda da tuƙinka amman a ƙara kulawa kuje a hankali, tafiyar kuma ta zama ta siiri kada kowa yasan da ita kuka fita kaji ko”.
Cikin mutunta juna Baba Ado yace.
“In sha Allah ba matsala”.
Daga nan yace.
“Jamil fito mata da kayanta, mu mun tafi”.
Nan suka fita shida Ummi.
Ita kuwa Jamil ya kai mata kayanta cikin motar da Baba Ado ya kawo har bakin Part ɗin su.

Tana fita Jalal na binta a baya, ya rage Sarace kadai ke musu aikin abincin dare.

Tana shiga motar Baba Ado yaja a bakin Part ɗin Lamiɗo suka tsaya nan ta shiga tai musu sallama kana suka fito suka tafi.

Ƙarfe uku dai-dai suka isa Rugar Bani.
Motar nayin parking tayi sauri ta fito.
Junaidu dake fitowa gidan ne, yayi maza ya nufi inda take fuska cike da murmushi yace.
“Oyoyo Adda Shatu masha”.
Cikin tsananin jin daɗi tace.
“Oyoyo Junaidu.
Yauwa isa ka shigo min da kayana”.
Da sauri yace to, kana ya nufi.
Wurin motar inda Baba Ado ya fito mata da jakarta da kuma ɗaya jakar wacce Sheykh yayiwa Junainah tsaraba.
Amsar jakukkunan yayi ya ajiye a bakin zauren kana ya dawo kusa da Baba Ado ya bashi hannun suka gaisa tare da cewa.
“Ka iso mana Baba”.
Cikin nitsuwa Baba Ado yace.
“A a ba komai yaro sauri nake zan juya so nake kafin a kira la’asar na isa gida.”
“Bazaka tsaya ku gaisa da Bappanmu Baba”.
Junaidu ya Kuma faɗa.
A a ba matsala sai in munzo ɗaukarta.
Dole Junaidu ya barshi yaja mota ya tafi.

Shatu kuwa cikin wani irin masifeffen jin daɗi da begensu ta kutsa kanta cikin gidan tare da cewa.
“Assalamu alaikum Ummey ina kike Junanaih Ina Inna Amarya”.
Wani irin zabura Ummey dake cikin ɗaukita tayi tare da miƙewa ta nufi waje da sauri.
Junainah kuwa da fitowarta daga ban ɗaki kenan.
Wani irin ihu mai cike da tsalle da jin daɗi tayi ta cilla butar hannunta can gefe.
Tare da nufo Shatu a guje tana cewa.
“Wayyoooooooo Allah na Adda Shatu na Ummey ga Adda Shatu na Oyoyo”.
Ta ƙare zancen cikin tsananin jin daɗi tare da nufo Shatu haiƙan ƙadaran.
Zaro ido Ummey tayi tare da cewa.
“A a fa a a Junainah kada ki faɗa jikinta zakiji mata ciwo”.
Sai kuma tayi shiru tare da zuba musu ido ganin itama Shatu gudun takeyi cikin ƴar sassarfa kamar ba mai cikiba.
ta nufo Junainah.
Wani irin ruggume juna sukayi da ƙarfi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ta ɗago Junainah data makaleta tafara jujjuyawa da ita.
Da sauri Ummey ta nufosu tana cewa.
“Na shiga uku Shatu ki sauƙeta zakiji ciwofa.
Inna Amarya ma da sauri ta nufosu tana.
“La hailahalillah Shatu zaku faɗifa”.
Junaidun da shima yanzu ya shigo da jakukkunan sai kallonsu yake yana murmushi.

Ita kuwa Shatu Ummey na isosu ta sauƙe Junainah kana ta faɗa jikin Ummey ta ruggume ta gam-gam tana maida numfashi da haki take cewa.
“Oyoyo Ummey na yau kam daɗi zai kasheni”.
Itama Ummey wani irin ruggume ta tayi cikin tsantsar jin daɗi da tsananin so.
Tace.
“Oyoyo Shatuna Boɗɗona mangana yar al’barka.”
Sai kuma tayi saurin janye jikinta jin yadda ɗan cikin yake wutsul-wutsul da sauri ta kamo hannun ta.
Ita kuwa Shatu hawayen farin ciki take zubdawa.
Inna Amarya kuwa taburma ta shimfiɗa musu a tsakiyar gidan.
A ƙarƙashin inuwar bishiyar mango da bishiyoyin ayaba suka zagayeshi hakan ya bada daddaɗan inuwa mai sanyi.
Da sauri Ummey ta ajiyeta.
Ruwan sanyin da Inna Amarya ke miƙa mata ta amsa ta bata.
Ba musu ta amsa ta kafa kai dan hakin da takeyi yasata jin ƙishi.
Gefenta Junainah ta zauna.
Ummey kuwa gabanta ta zauna Inna Amarya kuma gefenta.
Junaidu kuma shigar da kayanta ɗakin Ummey yayi kana ya fito ya gaisheta sannan ya tafi.

Ita kuwa Shatu a hankali ta zame ta kwanta ta ɗaura kanta bisa cinyar Ummeynta cikin sanyi tace.
“Alhamdulillah yau gani ga Ummey na”.
Murmushi Ummey tayi kana ta shafa cikinta tare da cewa.
“Shatu ki dena wasa da jikinkifa, kada kije ki tadawa kanki naƙuda lokacin ta baiba”.
Cikin jin ɗan kunya tace.
“Toh Ummey itama ai yau tana farin cikin ganinki”.
Sai kuma tayi maza ta miƙa zaune.
Jin muryar Bappa na cewa.
“A a a masha ALLAH yau gani ga Shatu na”.
Cikin sauri ya iso inda suke gefenta ya zauna ita kuwa hijabinta ta gyara tana ɗan rufe cikinta alamun kunya tace.
“Oyoyo Bappa na”.
Cike da jin daɗi yace.
“Sannu Shatu na.

Nanfa suka fara gaggaisawa da hirar yaushe gamo, ɗaya Bayan ɗaya haka take tambayar ahlinta wato ahlin Abboi.
Su iro ma suna dawowa aka zauna ana hira.
Inna Amarya kuwa da Ummey gidin murhu suka koma sunata haɗa miyar jumma’a.
Junainah kuwa na liƙe da ita.

Sai salla ne kawai yake ɗagasu a wurin.

Sai bayan sallan isha’i kuma duk suka zauna bisa taburma suna hira suna cin abinci.

Cikin nitsuwa Shatu ta juyo ta kalli Bappa dake gefe dashi dasu Iro yayinda farin wata ya haskasu ras, numfashin ta ɗan fesar tare da cewa.
“Bappa na ya lbrin su Yah Giɗi na”.
Tayi mgnar hawaye na ciko mata ido”.
Cikin sanyi yace.
“Wlh Shatu jikina na gaya min su Giɗi suna gab da baiyana.
Dan wayewar asuban yau nayi mafarkinsu wai Mijinki ya dawo min dasu da hannunshi.
In sha Allah kuwa suna kan hanya da izinin ubangiji tabbas suna hanya, muci gaba da Addu’o’in da muka sabayi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button