NOVELS

GARKUWA PART 3

A hankali murya na rawa ido na zubda hawaye yace.
“Mata ina sha, ko kada insha zaki gaya musu, ki gaya musu mana”.
Da sauri Jalal yace.
“Adda Shatu menene wani tsafin zaiyi ne?”.

Da sauri ta kalli Jalal kana ta juyo ta kalli Ba’ana ta kuma juyowa ta kalli Sheykh.
Cikin sanyi murya na rawa tace.
“Ka.”
Dai-dai lokacin kuma Baroon yasa hannunshi ya bugi ruwan tare da cewa.
“Idan yasha zai ɓace ne fa”. Yayi mgnar sabida baisan Ba’ana ya ƙauracewa tsafi da asirce-asircen ba.
A hankali ya juyo ya kalli Shatu tare da cewa.
“Ƙarasa mgnarki domin itace kamar zaɓin rayuwata da mutuwa ta.”

A hankali tasa hannunta ta ɗauki Afreen dake kallon fuskarshi tana wasa.
Cikin rauni tace.
“Kada ka sha Yah Ba’ana ka bari hukuma tayi maka hukuncin daya dace da kai”.

Yana zubda hawaye yace.
“Uhummm to shike nan Mata. Amman nasa baki san me nake aikatawa ba shiyasa kike tunanin hukuncin hukuma zai rageni da rai”.
Da sauri ta nufi cikin ɗaki tana kuka.

Kana su Jalal kuma suka kamashi sukasa a motarsu sukayi gaba dashi.

Su kuwa Bukar da Bugulu da kuka suka tafi.
Yayinda duk mutane ke zubda hawaye.

Bayan anyi sallan la’asar ne.
Sheykh yace su fito su tafi cikin disashewar murya Shatu tace.
“Jamil aini zan kwana biyu”.
Kai Jamil ya ɗan juya yace.
“A a Yah Sheykh yace ki fito mu tafi, wai ya fasa baza ki kwana ba”.
Jin haka yasa Inna Amarya dasu Giɗi da Gaini da Seyo da yanzu suka dawo sukace.
Tabi umarnin mijinta.
Dole haka ta fito suka tafi, harda Junainah.

Gaba ɗaya Rugar Bani tayi shiru tayi sanyi tamkar waɗanda akayiwa mutuwa.

A can masaraur Joɗa kuwa.
Cikin wani irin ƙunan rai Sheykh ya kalli A….!

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 a yawan posting ne babbancinsu yake. Idan kinaso turo kuɗin ta Account 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai kiyi screenshort na Debit Alert ki turo ta WhatsApp 09097853276. Sai in saki a group, ku ƴan 300 in baki da damar biya ta Account to ki sayi katin Mtn na ɗari uku kacal ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276. Banbancin special Group da Normal group a yawan posting ne kada kizo kice in miki ƙarin bayani ɗan Allah.

                               By
             *GARKUWAR FULANI*

4/6/21, 4:15 PM – &: Agogon hannunsa, ƙarfe 11:30 pm na dare har yanzu Shatu bata shigo inda yakeba.
Idanunsa ya rumtse da ɗan ƙarfi,
tare da gyara kwanciyarsa, ya mai jin wani irin zazzafan kishi na taso mai.

Allah Ya sani yana jin ciwo da zafi acikin zuciyarshi, har yanzu idan ya tuno yanayin tashin hankali da kuma tausayi da rauni’n da ya gani a fuskar Shatu, lokacin dasu Jalal ke dukan wannan taƙadirin tsohon saurayin nata.

Mchewww yaja wani dogon tsaki a fili yace.
“Sabida shine zata barni ni ɗaya a ɗaki kamar wani marar galihu?”

Muskutawa yayi tare da fesar da zazzafar iska ta bakinsa, sosai yakejin kuna acikin zuciyarsa, wanda kuma duk akan Kishin Shatou’n da yakeji ne.
A haka dai bacci b’arawo yayi awon gaba dashi bayan yayi ta juye-juye.

Ita kuwa Shatu tunda suka dawo ta gaza tsaida hawayenta.
Allah Ya sani bata taɓa jin son Yah Ba’ana aranta ba, bata kuma jinsa a matsayin saurayin da take buri da fatan aure, sai dai tasan tabbas tana mishi so irin na ɗan uwan taka.
Tana jinshi tamkar su Yah Al’ameen dasu Yah Giɗi.
Tana mishi so irin na ƴan uwa musulmai da son ya gyara rayuwarsa ko ya samu rabauta ranar gobe kiyama.

Kuka sosai takeyi, rungume da Afreen damunta da yarinyar tayi ne kuma yasa ta fito da ita.

A falo ta samu Ummi zaune ita da Jalal.
Cikin disashewar murya tace.
“Ayyah Ummi ga Afreen kaina ciwo ina so inyi bacci ta hanani”.

Da sauri Ummi ta miƙo hannu ta amsheta tare da cewa.
“Tasha mamanta ai ko?”.
Kai ta gyaɗa mata alaman “Eh.”

Jalal ne ya ɗan kalleta sosai fuskarta, ta kumbura tayi jazir idanunta kuwa sunyi tib tib.

A hankali ya maida kanshi ga Ummi yana mai ci gaba da cewa.

“Ai daga can Rugar tasu cibiyar bincike na jiha muka kaishi.
Alhamdulillah kuma shida bakinshi ya amsa dukkan laifukansa tare da yin bayanin komai, ya tabbata cikekken mai laifi da ake nema ido rufe, yanzu
kai tsaye ba ɓata lokaci za’a kaishi kotu ta yanke mishi hukunci ranar Monday da izinin ubangiji.”

Cikin sanyi Ummi tace.
“Allah sarki, Allah yasa ya samu da sauƙi”.

Miƙewa Jalal yayi tare da cewa.
“Wani da sauƙi kuma Ummi ai yadda yayi ta kashe mutane, da sace dabbobin su shima kasheshi za’ayi a rage mugun iri a duniya”.

Jin hakanne kuma yasa cikin sauri Shatu ta koma ɗakinta.
Bisa kan gadonta ta kwanta tare da kifa kanta kan pillow, wani irin sassanyan kuka ne ya kwace mata.

Lokaci daya Komai ya fara dawo mata sabo, tun randa ta fara ganin Yah Ba’ana da kuma yau da tayi mishi kallon da take tsoron kada ya zama na ƙarshe ne.
Saboda ita dai bata taɓa sanin cewa yana sata da kashe mutane ba.

Haka ta dinga sak’e sak’e acikin zuciyarta, a ranar dai haka suka kwana kowa da abinda ke damunsa.

Washe gari kuwa, ranar Lahadi, Sheykh yana gida wuni zur amman Allah bai sa yaga idon Shatu ta fito ba.
Wannan abun ya ƙara ingiza mishi zafin kishinsa, ji yakeyi tamkar yayi ta ihu dan takaici.

Bayan sallan azahar ne.
Ya dawo a falon ya samu Ummi da Aunty Juwairiyya da Mamey.
Wacce kuma ta shigo ne dan ta duba Shatu, da yawan kuka ya sakar mata zazzafan zazzaɓi da ciwon kai.
To ta fito daga d’akin Shatou d’in kenan, suna zaune afalo ya dawo.

A hankali ya ɗan sunkuyo ya shafa kan Afreen dake cinyar Mamey.
Tare da cewa.
“Mamey ɗazu naje kina bacci”.
Tana kallon yadda yake shafa kan Afreen yana cewa.
“Allah ya miki al’barka”.

Murmushi tayi tare da cewa.
“To masu ƴaƴa kaima Allah yayi maka al’barka”.
Cikin jin daɗi yace.
“Amin Amin Mamey na”.

Murmushi tayi kana tace.
“Muna son mgn da kai”.
Da sauri cike da biyayya yace.
“Toh Mamey gani”.

Miƙewa tayi ta nufi waje, shikuwa gyara al’kyabbar dake jikinshi yayi tare da bin bayanta.

Kai tsaye Part ɗin Abbanshi ta nufa yana biye da ita a baya.
Da sallama suka shiga.

Murmushi Abba yayi tare da miƙa hannunshi ya amshi Afreen daketa raba ido.
Ita kuwa Mamey gefenshi ta zauna.

Da sauri ya zauna gabansu a ƙasa bisa Austrian carpet, ya tanƙoshe sawunshi ya fuskancesu da kyau.

Gyaran murya Abba yayi tare da zuba mishi ido, wanda haka yasa shi yin ƙasa da kansa.

Shiru-shiru basuyi mgna ba, hakane yasa ya sake ɗago kanshi da sauri yayi ƙasa da idonshi sabida ganin daga Abban har Mameyn ido suka zuba mishi.
A hankali ya fara motsa lips ɗin shi yana cewa.
“Astaghfirullah!!”.
Ya fara tubawar ubangijin mu.
Kafin ya tubarwa iyayen nasa dan hakan da sukayi ya rauna tashi sabida bai san laifinsa ba.

Su kuwa sun mishi hakane dan su sa mishi rauni da kuma halarto da biyayyarsa.

Karo na uku ya kuma ɗagowa ya kallesu.
Kawai sai ya tankwashe kansa bisa kafad’arsa murya cike da rauni yace.

“Dan Allah Abba Mamey kuyi haƙuri ku gafarceni idan wani laifi nayi muku, ku sanarmin dan in kiyaye gaba kada in maimaitashi”.
Sai kuma ga idanunshi sunyi rau-rau sun fara wani sheƙi alamun hawaye na tsastsafowa daga cikinsu.

Cikin tsare murya da fuska da kauda wargi Abba yace.

“Muhammad!”

Da sauri murya na rawa yace.
“Na’am Abbana”.
Sai kuma ya kalli Mamey da itama ta kirashi.
Amsawa yayi tare da zuba musu ido.

Kai titsiyewar iyaye akwai sa rawan jiki da fargaba a zuciyar ɗan adam.
Cikin tsananin kausasa murya Abba yace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button