NOVELS

GARKUWA PART 3

A part ɗinsu Jalal kuwa.
Yah Giɗi Seyo Gaini ne zaune bayan duk sunyi wonka, sun saka sabbin kayan da Jamil ya zaro musu cikin durowarsa.

Cikin wani irin yanayin jin daɗin duniya da kuma bege da kewar iyaye da ƴan uwa wanda da sun cire tsammani.
A hankali Yah Giɗi ya kalli Jamil dake miƙo mishi turare yana cewa.
“Kai masha Allah sai kunga yadda kukayi kyau, farinku ya ƙara fitowa”.
Cikin rauni Giɗi yace.
“Dan Allah bawan Allah, nan ina muke ne? Kuma ina wanda muka dawo dashi? Sannan ina za’a kaimu? Wayasa aka fito damu?”.
Da sauri Jamil ya zauna gabanshi kamo hannun shi yayi a hankali yace.
“Nan kuna cikin Ɓadamaya ne, cikin masarautar Joɗa, wanda kuka dawo dashi kuma Yayana ne Affan ya tafi ƙofar matarshi.
Wanda ya taimake ku yasa aka fitar daku kuma babban Yayanane Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa.
Yana nan matarsa ta haihu yau akeyin suna. Sai in ya nitsu zaizo wurinku shi zai gaya muku ina za’a kaiku”.
Wasu irin hawaye ne suka tsunkowa Gaini murya na rawa yace.
“Alhamdulillah kowa yace yaya zaiyi ya manta da Allahu wahidun ƙahharar sarki buwayi gagara misali mai badawa mai hanawa mai raya mai kashewa mai kawo sauƙi cikin tsanani mai yaye tsananin duhu ya wanzar da haske”.
Ido Jamil ya zuba musu cike da so da ƙaunar su, sai kuma ya kalli Seyo da yake zubda hawaye cikin sanyi yace.
“Ko wanne hali ahlinmu ke ciki”.
Da sauri Jamil yace.
“Yanzu muje falo kuci abinci kunji dan Allah ku bar kukan”.
Kasan cewar ya haɗa su da Allah yasa ba musu suka tashi.
Amman badon hakaba farin cikin da suke ciki ya kori yunwa bare ƙishi.

A tsakiyar falon suka zauna.
Jamil da kanshi ya zuba musu abincin da Aunty Rahma ta kawo musu.
Sukaci suka sha.

Dai-dai lokacin kuma aka kira sallan magriba.
Nan sukayi al’wala kana Jamil ya jasu sukayi jam’i.

Shatu kuwa bata bar ɗakin Sheykh ba saida ya tafi masallaci.
Ta fito cike da farin ciki.
Aunty Amina da Khadijah da Umaymah da Hibba ta samu a falonta Umaymah ta miƙa wa key ɗin tare da cewa.
“Umaymah Yah Sheykh ya saya min mota”.
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
“Masha Allah. Allah ya sanya al’khairi”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Kana duk sukayi al’wala haramar salla.

Ƙarfe goma da rabi.
Duk baƙi sun watse.
Sai su Umaymah da su Aunty Amina.
A falon Shatu suke suna hirarsu cikin salama Ummi na ruggumi da Afreen.
Umaymah kuwa na haɗawa Shatu tea da fifitashi da kyau.
Aunty Rahma kuwa kitso Khadija keyi mata.
Junainah da Ishma kuwa suna can babban falon da Hibba da Jalal.

Sara da Larai da indo hadimar Aunty Juwairiyya kuwa tattare kitchin sukeyi da kimtsa ko ina na gidan.

Sheykh kuwa a hankali ya jawo wayarshi daya tattare wacce yake waya da Hajia Mama da ita.
Kiranta yayi.
Tana amsawa yace.
“Ƴar ta mutu ko?”.
Wani irin gigitaccen tsaki taja tare da cewa.
“Inafa ta mutu na dai ji ta suma amman wannan Shegen yaron duk abinda nayi a kanshi ko matarsa yanzu dama yar tashi abun baya tasiri.
Sannan babban tashin hankali na, shima Sarkin al’adun suna bai dawoba.
Kuma wayarshi na shiga baya ɗagawa, tsorona kada dai sun ganeshi”.
Cikin sauya muryarsa ih zuwa muryar Jahan yace.
“A a ba dai kamashi ba kam, sai dai ko in yana jin tsoron amsa kiran nakine sabida kada kiyi mishi faɗa tunda ƴar bata rasuba kada kice bai iya aikinsa bane a ganina fa shine yasa baya amsa kiran naki”.
Cikin tashin hankali tace.
“Ni babbar matsala ma yau tunda gari ya waye hankalina yake a tashi zuciyata na tsinkewa gaba ɗaya tsoro ya rufeni ji nakeyi wani mugun abu yana tunkaro rayuwata, naje gidan boka kuma ya koroni shima sai tsalle yakeyi yana kaɗe jikinsa
Wai komai na gab da dawo mana”.
Murmushi mai cike da jin daɗi yayi a ransa yake zaton ko shiryace zata zo mata, haka yasa yace.
“Sai gobe zanzo muyi mgn in kaiki gidan wani sabon boka”.
Da sauri tace.
“To”.

Daga nan ya katse kiran.
Kana ya miƙe ya fito falo, a hankali ya kalli Jalal da Hibba tare da cewa.
“Jamil fa”.
“Yana Part ɗin mu”.
Jalal ya bashi amsa”.
To yace kana ya juyo ya kalli Yah Jafar da yanzu ya shigo kenan.
A hankali ya tsaya gaban Sheykh.
A hankali suka lumshe idonsu a tare, da sauri Sheykh da Jalal da Hibba suka matso kusa dashi sosai jin yana cewa.
“Jabeer zuciyata na tsinkewa tun jiya sai inji kamar wani abu zai faru”.
Cike da mamaki Jalal yace.
“Wlh nima tun jiya zuciyata ke tsinke kirjina yaita bugawa”.
Wani irin rumtse ido Sheykh yayi tare da cewa.
“Nima abinda naketa fama dashi kenan tun jiya, to da Aisha ta suma sai nai zaton ko abinne ke samin tsinkewar zuciya.
To kuwa still abin bai bariba saima ƙaruwar da yakeyi yana tsananta”.
Cikin sanyi Hibba tace.
“To kuyi ta addu’a hakama Umaymah da Mamma da Aunty Rahma sukace suna ji”.
Kai suka gyaɗa gaba ɗaya.
Hannun Yah Jafar ɗin Sheykh yaja suka nufi Part ɗin su Jamil.

Su kuwa su Jalal zama sukayi suna kallon Ishma da Junainah daketa sabgoginsu.

A hankali Sheykh ya zauna tare da kallon Jamil dake zaune tsakiyarsu Giɗi a hankali yace.
“Ka barsu su huta mana”.
Cikin sanyi Jamil yace.
“Allah ko Hamma Jabeer ina so in tafi wurin Khadijah ma sai inji zuciyata na tsinkewa kamar dai zan samu wani abu”.
Cikin kula Sheykh yace.
“Uhmm duk haka mukeyi kaita mai-maita innalillahi wa innailaihi rajiun”.
To yace.
Shi kuwa Sheykh nitse ya kalli Gaini da zai kai sa’an Affan.
Cikin kula yace.
“Sannunku da hanya”.
A tare sukace sannu.

Jamil ne ya ɗan kallesu tare da cewa.
“Shine babban yayanmu Sheykh da yasa aka fito daku”.
Da sauri suka ɗan gyara zama suka matsoshi tare da cewa.
“Allah sarki bawan Allah mun gode Matuƙa Allah ya saka da al’khairi ya kula da ahlinka fiye da yadda ka kula damu”.
Cikin jin daɗi yace.
“Amin ya rabbil izzati, amman kuma duk haka ya farune sanadin Sulaiman da aka rufeshi tare daku”.
Cikin gamsuwa sakace.
“Ayyah”.
Sai kuma Giɗi ya ɗan share hawayen da suka zubo mishi tare da cewa.
“Ayyah bawan Allah yaushe zamu koma Rugar Bani muga Bappa da Inna da Ummey da Shatu da Junnu”.
Cikin gamsuwa da tausayinsu Sheykh yace.
“In sha Allah nan kusa amman nafi son sai naga kunyi aski kun ƙara hutawa, gobe zuwa jibi da kaina zan medaku”.
Cikin wani irin masifeffen jin daɗi sukace.
“Allah ya kaimu”.
“Amin Amin”. Yace kana ya musu sai da safe.

Daga nan wurin Abbanshi da Lamiɗo da Galadima yaje suka ɗan yi wata mgnar kana ya dawo.

Ranar dai haka suka kwana gaba dayansu babu wanda yayi isasshen bacci sabida masifar bugawa da ƙirazansu keyi.

A can Rugar Bani kuwa.
Ko abincin dare Ummey bata iya ciba.
Haka nan sai taji zuciyarta na tsinkewa yana bugawa.
Tun abun bai damunta har ta gayawa Bappa, so ya bata ƙarfin guiwa da yin addu’a.

                 *Ba'ana*

Zaune yake gaban yaransa cikin rauni da yanayin damuwa yace.
“Nanda wata uku masu zuwa zan koma ƙasar Nigeria zanyi yaƙin neman Shatu koda zan rasa rainane, zan koma gareta.
Zan gaya mata ko mutuwa nayi sonta ne ajali na”.
Cikin bashi ƙarfin guiwa ɗaya daga cikinsu yace.
“Zama kayi nasara”.
A hankali yace.
“Babu tabbas, domin tunda na rasa Shatu nakega nayi rashin babbar nasara”.
Sai kuma ya miƙe ya shiga cikin ƴar ƙaramar bukkarsa.

Murmushi Baron yayi tare da katse kiran da yayi Sheykh yana jin duk bayanan Ba’ana.
Dan shi Baroon yanzu ya zama ɗan aikin Sheykh dan tun zuwansa lokacin ciwon hannun Shatu.
Da fari har yasa a kirasa daga baya yasa aka dawo dashi.
Ya biyashi kuɗi masu tarin yawa, yayi mishi duk bayanin ɗaya nema, kana yasashi ya koma wurin Ba’ana kuma ya naɗo mishi rahoto da duk wani motsin Ba’ana yana turo mishi.
Alhamdulillah kuma yanzu duk shirin kama Ba’ana yakeyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button