NOVELS

GARKUWA PART 3

To sai marigayi Cuɓaɗo ya bamu tabbacin bulalin Shaɗin masarautar Joɗa ne kawai zai karya duk wani sihirin jikin Ba’ana to kasan cewar yana sonta so na gsky bai cutar da ita in hankalinmu ya tashi kan muna tsoron ya aureta takan ce mana.
“Abinda in na gama karatuna zamu koma Yahunde sabida ita bamu sanar mata mun gano asalin Ummey ƴar ina bane gudun ita yarinyace kada tai ta gayawa wasu.

To munata son yadda alaƙa zata haɗamu sai kuma ga ƙabilar ɓachama su tasomu gaba.
Ran da muka zo nan na forko da muka ga Jamil sosai muka ƙara ƙarfafa guiwar ita ahlin masarautar Joɗa ce dan akwai kamar jini tare dashi da ita.
To da akayi faɗa kukaje mana jaje da gayya Arɗo Bani ya gaggayawa mai martaba Lamiɗo mgn dan ya tunzurashi ayi Shaɗi mu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan.

Mun dawo da ita, mu kuma samu mgnin Ba’ana to kuma Alhamdulillah duk abin neman ya samu.

Sai kuma yayi ƙasa da kanshi murya na rawa yace.

“Sai dai sanadin faɗan ni na rasa kowa nawa”.
Bappa ya ƙarashe mgnar cikin rauni da zubda hawayen tuno matarsa da zaratan yaranshi.

Cikin raunin tuno ahlinshi kuka mai rauni ya rufeshi yayinda Shatuma kuka mai ƙarfi ya kubce mata hakama Ummey sabida ita dai gata ta dawo ahlinta shi kuma garin dawo da ita cikin ƴaƴanta ya rasa nashi yaran.

Cikin tsananin jin daɗi
Sheykh ya ɗan muskuta cikin tsananin farin ciki da jin daɗin da godewa Allah daya bashi damar kuɓutar dasu ƴaƴan Bappa su Gaini shima zaisa Bappa farin ciki kwatankwacin yadda ya sashi.
Cikin sauri da bada umarni ya kalli Jamil tare da cewa.
“Jamil tashi maza kaje kazo dasu”.
“To”. Jamil yace kana ya miƙe da sauri yafita batare da ɓata lokaciba sabida ya gano su waye Gaini.

Yana zuwa yace.
“Yah Gaini taso taso kuzo ga Bappanku da Shatu da Junainah”.
Ai kafinma ya rufe baki duk sun muƙe cikin tsananin zaƙuwa suka biyo bayanshi.

Shi kuwa Bappa da Arɗo Bani da Alhaji Haro da Alhaji Umaru rauninsu ya rigada ya dawo tuno irin kisan gillar da ƙabilar ɓachama sukayi musu.

Shi kuwa Sheykh dasu Lamiɗo shiru sukayi sabida son yi musu ba zata.

Da sauri Jamil yasa hannunshi ya tura ƙofar suka shigo tare da cewa.
“Assalamu alaikum Bappa share hawayenka gasu Yah Gaini Seyo da Giɗi”.

Duk sauran mutanen falon duk suka ɗago kansu.

Ido cikin ido Shatu tayi da Yah Giɗi’nta abokin tsamarta.
Wani irin yunƙura tayi ta miƙe tsaye tare da cewa.
“La’ilahaillaha Muhammadu rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam Alhamdulillah Bappa gasu Yah Gaini”.
Jin kalaman Shatu ne yasa Bappa dayake sunkuye ya ɗago kanshi yana kalli bakin ƙofar shigowa ya sauƙe kwayar idanunshi kan…..!

Kuyi haƙuri da typing errors ina cikin ciwon kai nayi typing ɗin a daddafe.

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300.
A yawan posting ne babban cinsu 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa in kin tura sai kiyi screenshort na Debit Alert ki turo min ta whatsApp 09097853276 ƴan 3oo in naki da halin biya ta Account zaki iya sayan katin mtn na ɗari uku ki copy numbers ɗin ku turo min ta whatsApp ɗin 09097853276.

                            By
              *GARKUWAR FULANI*

4/6/21, 4:15 PM – &: Ya sauƙe idanunshi kan Giɗi Seyo Gaini.
Cikin wani irin yanayin tarin farin ciki mai sanya rauni.
Wasu zafafan hawaye suka kwaranyo mishi.
Da sauri ya yunƙura ya juyo ya fuskanci al’ƙibila. Sujjadar godiyar Allah yayi kana ya ɗago yana mai zubda hawaye.
Ita kuwa Shatu da sauri ta ƙarasa garesu, kawai sai ta faɗa jikinsu baki ɗayansu, tare da sakin raunataccen kuka.
Cikin rauni da yanayin kula Seyo wa mai tausayi kamar uwa yace.
“Shatu dena kuka, mu godewa Allah”.
Sai kuma ta kalli Yah Giɗi cikin sanyi ta ruggume shi tare da cewa.
“Tunda na rasaka kusa dani na rasa abokin faɗa da tsama, shiyasa lokuta da dama ina jin daɗin inyi taƙaddama da Gimbiya Saudatu dan sai yana tunamin ta ƙaddamar mu, da Yah Giɗi na abokin faɗana”.
Cikin zubda hawaye shima Giɗi yayi murmushi tare da janyeta jikinshi kana yace.
“Nayi kuka a lokuta ma banbantan da bazan iya ƙididdiga ba sabida tunoki da rayuwarmu”.
Hannun tasa ta share hawayenta kana ta kalli Yah Gaini wa mai matsayin Uba cikin kulawa da yanayin rayuwarta yace.
“Shatu ina Ba’ana ko mun samu nasarar rabuwarki dashi”.
Da sauri tace.
“Yah Gaini Allah ya rabamu da Yah Ba’ana”.
Cikin tarin jin daɗi yace.
“Alhamdulillah”.
Dai-dai lokacin suka isa gaban Bappa daketa zubda hawaye.
Zama sukayi a gabanshi gaba dayansu huɗu.
A hankali Giɗi ya sunkuyo ya kwantar da kanshi bisa cinyar Bappa tare da sakin sassayan kuka a hankali yace.
“Bappa mun ganka kaida Shatu ina Innarmu ina Ummey ina Junainah ina Yah Lado?”.
Da sauri Ummey tasa hannunta ta rufe bakinta jin kuka zai kubce mata.
Sai dai tuni sautin kukan ya fito.
Da sauri Giɗi ya rarrafo gabanta murmushi yayi still Ido na zubda hawaye a hankali yace.
“Alhamdulillah Ummey Junainah ina Innarmu da Yah Lado”.
Cikin kuka Junainah ta faɗa jikinshi tare da cewa.
“Arnan Ɓacama sun kashe Innarmu sun kashe Yah Lado sun kashe mutane da yawa na rugarmu”.
Da sauri Giɗi ya juyo ya kalli Ummey cikin tashin hankali da kubcewar kuka.
Gaini da Seyo suma kuka mai rauni suka sake ganin Bappansu yana jinjina musu kai alamun zancen Junainah hakane”.

Shiru falon sukayi baki ɗayansu sai sutin kukan Giɗi, Shatu, Junainah, Ummey, Seyo, Gaini. Raunin da kukansu ya sauƙar a zuciyar Bappa ne yasa shima sakin kuka dan yau sai sukaji gaba ɗaya rasuwar Yah Lado da Inna ta dawo musu sabuwa.

Sosai Shatu keyin kuka tana durƙushe ta tanƙwashe sawunta, hakama Ummey.

Gaba ɗaya kab falon saida idon kawa ya ciko da ƙwalla.

Cikin Rauni Sheykh ya matso inda Shatu ke durƙushe gaban yayun nata, cikin sanyi ya kalli Bappa Ummey murya a raunace yace.
“Tabbas bansan irin ƙunar da kakaji a cikin ranka ba Bappa amman nasan kwatankwacin kamannin ƙunan rashin ɗa, a suman da Afreen tayi naji ciwo da ƙuna a zuciyata tamkar ban taɓa farin cikiba, nasan zafin rashin uwa, amman ban san zafin rashin mataba dan kamin gatan bani Mar’atussaliha ta zame min GARKUWA tana sani farin ciki a duk lokacin da nake cikin baƙin ciki.”
Shiru yayi sai kuma ga hawaye shar-shar a idanunsa cikin rauni yace.
“Na samu komai da nake nema a rayuwata daga gareka ka bani mata ta gari, Allah ya azurtamu da samun ƙaruwar arzin haihuwa sanadinka Ummey na ta dawo.
Inama! inama! ace Inna da Lado ɓata sukayi ba rasuwa ba, da tabbas zanyi iyakar iyawata in dawo maka dasu da izinin ubangiji.
To amman wannan hurumin ubangijin sammai da ƙassaine.
Kayi haƙuri Bappa Allah ne ya baka Inna matsayin mata ya ɗauketa ya sauyama da ƴar uwarta kuma Allah shi ya baka Lado ya ɗauke shi kuma ya killace maka Seyo Gaini Giɗi, wanda wata ƙil da suna Rugar ba’a sacesu ba da an kashesu.
Gashi yanzu Allah ya dawo maka dasu.
Bappa kace Alhamdulillah ka godewa Allah da ni’imar da yayi maka sai ya ƙara maka wata a kai.
Kayi haƙuri ka bar kuka kaga kukanka na ƙara ingiza nasu”.
Ya ƙare mgnar yana sa hannunshi cikin tafin hannun Shatu yana murza a hankali.
Cikin gamsuwa da jin sanyi a ransa Bappa yace.
“Alhamdulillah”.
Da sauri Su Giɗi suma sukace.
“Alhamdulillah”. Hakama su Lamiɗo kab falon sai suka fara mai-mai-ta hamdala.
Ai kuwa cikin ikon Allah duk ƙuna da ƙuncin da zuƙatansu keyi a take Allah ya sauƙaƙa musu shi.
Cikin gyaran murya Lamiɗo yace.
“Alhamdulillah komai yayi forko zaiyi ƙarshe duk abinda yayi tsananin tabbas zaiyi sauƙi Allah mun gode maka daka ara mana rai da lfy”.
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Sheykh dake kallon agogon hannunshi sabida jin anyi kiran sallan azahar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button