NOVELS

GARKUWA PART 3

Wasu lallausan sleeping shoe ta zura a ƙafarta, tare kuma da tubke long hair ɗin kanta, da bluesy ribbon.
Tana gama kimtsa kanta kuwa, ahankali ta fito daga ɗakin, tare da jawo ƙofar ta rufe.
kaitsaye ta nufi Side ɗinsa.

Cikin sanyi ta tura ƙofar Bedroom ɗin nasa tare da yin sallama can ƙasan maƙoshinta.

Ganinsa atsaye da tayi ne kuma yasa, ahankali ta jingina da jikin ƙofar tana kallon yadda yake zirya a tsakiyar ɗakin, shi kadai sai ya kai mari ya kau gouro.
Ga wani irin numfashi mai ɗumi da yake fitarwa.
Idanunshi kuwa sun kaɗa sunyi jazir.

A hankali ta nufo tsakiyar ɗakin.
Cikin sanyi da kuma rauni ta nufi inda yake.
Dai-dai lokacin shi kuma ya juyo.
Yana juyowa kuwa ta faɗa jikinshi ta rungumeshi tsam a jikinta.
Ashagwaɓe ta saki wani irin raunataccen kuka mai kashe jiki da zuciya.
Murya na rawa cike da rauni tace.

“Kayi haƙuri Yah Sheykh ka gafarceni, na tuba please, kukana bawai inayi dan na ɓata ranka bane, banason fushinka, Dan Allah kada ka kwana kana fushi dani, I’m very scared dan bazan iya jurewa ba…”

Kasa ƙarasa maganan nata tayi, lokaci ɗaya kuma ta ci gaba da sakin Shessheƙan kuka, tare dasa hannayenta akan chest ɗinsa.

Shi kuwa Sheykh har yanzu fushi yakeji, saboda haka ma gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi dan tsananin takaici kukan da takeyi.
Hannunshi yasa ya soma ƙoƙarin ɓanbareta daga jikinsa, murya adaƙile yace.
“Ni Sakeni! ki barni!! kuma ki fita harkana!!! Kije can ki gama kukan naki a can ɗakinki, badai kinfi sonshi ba? maza fice min a ɗaki ni ɗakina ba wurin zubda hawayen soyayyar wani ƙato bane.”

Jin hakanne yasa, cikin sauri tasa hannayenta ta saƙalo wuyanshi, tare da cusa kanta a ƙirji shi, murya a raunace tace.
“Ni banason shi, da gaske Yah Sheykh ka yarda dani bana sonshi, aduniya waye zanso sama da kai? kaine fa Mijina, mahaifin ƴata, sannan kuma Garkuwa ta, tayaya zan so wani bayan kai?”

Da sauri yace.
“Eh mahaifin ƴarki ko? Bama mahaifin ƴaƴan kiba, wato irin daga ita shike nan ko?”.

Baby face d’inta ta shag’wabe, cikin kasala da kuma son sauk’ar masa da fushinsa tace.
“I’m very sorry Zawj mahaifin yaƴana.”

Idanunsa yaɗan lumshe, cikin kuma yanayin fara jin sanyi arashin ya tureta ya koma bakin gado ya zauna tare da cewa.
“In dai bazaki bar kukan nanba fice min a ɗaki sanida kukanki yana ƙona min rai”.

Da sauri tasa tafin hannunta ta share hawayenta.
Kana ta matsoshi Ahankali ta kwanta a jikinshi tayi lib, laɓɓan bakinta taɗan tattauna kana a raunace tace.

“Please Yah Sheykh nabar kukan, amma ka yafe min, bazan sakeba dan Allah kayi haƙuri”.

Ajiyar zuciya mai sanyi, ya sauƙe dan ta haɗashi da Allah ta gama zance.

Juyowa yayi asanyaye ya fuskanceta, tare dasa hannunsa ya ɗan tallafo kanta, shiru yayi batare daya ce komae ba, sai tsurawa fuskarta ido da yayi.

Ganin hakanne kuma yasa ahankali ta sake matsowa jikinsa, wani sassanyan hugging tayi masa, tare da fara sauƙe tagwayen ajiyan zuciya cikin sanyi da taushin murya a hankali tace.
“Nifa Bana sonshi, so irin wanda nakeyi maka, nadai soshi matsayin wana jinina, sannan kuma nayi kukane saboda rauni na.
Musamman ganin yadda ake dukanshi, da kuma yadda iyayenshi ke kuka.
Yah Sheykh Yah Ba’ana shine wanda yayiwa Ummey magani tsawon shekaru biyu ba dare ba rana kafun ta fara magana ta dawo haiyacinta.
Naje gidansu dare da rana cikin ruwa da iska na amsowa Ummey na magani,
Bai taɓa cutar da niba, Ya soni tamkar ransa, Nikuma na soshi matsayin ɗan uwa musulmi, Shekaran jiya tausayin dukan da akayi mishine ya sani kuka.
Jiya kuma tunda Jalal yace min za’a yanke masa hukuncin kisa raunina yasa na kasa tsaida hawayena.
Amman bawai dan ina sonsa so na aureba, kawai dai akullum Ina tuna al’khairinsa garemu ne, domin koba komae shid’in yayi taimako agaremu”.

Wani sassayan numfashi ya sauƙe tare da, sa hannunshi ya ruggumeta gam-gam a jikinshi.
Haka nan yaji duk jikinsa yayi sanyi.

Jin yanda yayi hugging d’inta ne kuma yasa ahankali tace.
“Nida Allah ya azurtani da miji kamarka, miji na gari! Mumini! Salihi! Mai tausayina! Mai riƙo da ibada! Mai cikakkiyar nagarta! Ta yaya idona zai iya ganin wani ɗa namiji da wata suffar, har in soshi?
Nida nake da kai, na shaida Allah yamin kyakkyawan zaɓi! Ina sonka sosai Yah Sheykh nah, Hamma Jabeer, kuma Malam d’ina, ina sonka, zan kuma ci gaba da sonka iya rai da mutuwa, sannan please ka yafe min zuwan da banyi gareka ba, ka d’aukeshi amatsayin ajizanci da kowani d’an Adam keyi, then maganan Afreen kuma kaina ke ciwo shiyasa na barta dasu Junainah, ka yafe min ni bani da sama daku kaida Afreeen kune farin cikina. Kune silar dawowata Nigeria’n rankune ke ajiye dani a masarautar Joɗa”.

Wani irin sasayyan kiss ya manna mata a goshinta.
Cikin kuma yanayi jin sanyi da daɗin kalamanta yace.

“I Love you Aysh, I always Love you, I love you so much, Tabbas nayi farin ciki da samun aurenki farin ciki marar misaltuwa,
Kece cikon farin cikina My Wife, kece sanyin zuciya da idanuna! sannan kuma har lau kece GARKUWA ta! Duk wani farincikin da zan samu yana tare dake ne, hakika ke HASKE ce acikin rayuwar Jabeer, zan rayu dake har abada!!”

Yakai ƙarshen maganan nasa cikin wani irin murya, mai sauƙar da kasala, tare kuma da zame jikinsa, ahankali ya kwanta kana ya jawota ya kwantar da ita ajikinsa.

Idanunta ta zubawa kyakkyawar fuskarsa, Cikin kuma yanayin sanyi tace.
“Please Yah Sheykh, idan da hali kayi wa ya Ba’ana wata al’farma mana”.

Kallonta shid’inma yayi kana hankali yace.
“Wacce irin alfarma kikeso ayi masa?”

Cikin zubda hawaye tace.
“Dan Allah kasa a meda case ɗinsa kotun musulunci, a yanke masa hukuncin Musulunci dan Allah”.

Kansa yaɗan jinjina, cikin yanayin jin rauni da tsananin tausayi kuma yace.

“I’m understand My Shatu, but amma kiyi haƙuri kinji, ki daina kuka domin dama tuntuni kotun musulunci aka kai ƙarar, kotun su Abban Yusuf (HUKUNCIN ALLAH) za’a yanke masa Insha Allah”

Wani sassayan numfashi ta fesar tare dasa hannu ta share hawayen ta.
Kana anutse tace.
“Alhamdulillah!”

Shiru ta ɗanyi sakamakon jin yanda ya soma yawo da hannnunsa akan waist dinta, akasalance ta ɗago kanta ta kalleshi, wanda shi ɗinma kuma kallonta yake da lumsassun idanuwansa.

Ahankali ta matso da fuskarta gab da nasa, tare da zaro harshen ta ta ɗaura akan lips ɗinsa, domin ta fahimci a irin wannan yanayin sam ba buƙatar ace, sai ta jira shi ya fara kissing ɗinta.

Idanunsa da suka ɗan sauya kala lokaci daya ya lumshe, musamman alokacin da yaji sauƙan harshenta akan laɓɓansa.
Wani irin sha’awa da shauƙinta yakeji, hakanne ko yasa shi buɗe bakinsa, ahankali ta zura harshenta acikin bakin nasa.

Wani irin dogon numfashi dukansu suka Sauƙe alokacin da tongues ɗinsu suka had’e waje ɗaya.
Azafefe suka shiga kissing din juna, Yayinda kowannensu ke transferring yawun bakinsa wa ɗan uwansa.

Kissing ɗin juna sukeyi sosai, Yayinda Aysha’n ke neman zautar masa da lissafi, hakan kuwa shiya sanya azafafe ya zare vail ɗin da ta rufe jikinta dashi.
Ganinta da yayi acikin royal blue sleeping gown ɗin da yayi ne kuma, yasa shi jin wani hot feeling ɗin ta.
Lokaci guda ya soma sakar mata kiss tako ta Ina.
Yayinda daga gefe guda kuwa daddaɗan kamshin Oud dinta ke sake kunna sa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button