NOVELS

GARKUWA PART 3

A falonshi ya sameshi zaune shida Sulaiman.
Da sauri Sulaiman ya tasa ya nufi inda yake.
Cikin yanayi sabo da shaƙuwa suka ruggume juna.
Murya na rawa Sulaiman yace.
“Sheykh ngd ngd Ngd matuƙa Allah ya saka da al’khairi ya rufa asiri duniya da ƙiyama ya ceceka da wahalar siraɗi kamar yadda ka zama sanadin cetoni daga azabar hukumar ƴan sanda da na faɗa ciki”.
Amin Amin yace cike da tausayin ganin yadda Sulaiman ya rame yayi duhu farin shin nan duk ya tafi.
Ga alamun tashin hankali da firgicin da basu gama sakeshi ba.
A hankali suka zauna gaban Malam Abubakar da yaketa sanya musu al’baka a duniya bai taɓayin ɗaliban da yake so da ƙauna sama dasu ba.
Cikin kula Sheykh ya ɗan rusunar da kai tare da cewa.
“Barka da hantsi malam”.

“Barka dai Muhammad, ya iyalin taka da ƴan tagwaye da Jafar”.

“Alhamdulillah duk suna lfy sai dai Yah Jafar yanzu kusan wata uku kenan, yake yawan yin bacci dare da rana safe da yamma, salla da cin abinci kaɗai ke tada shi.
Ni kaina wasu lokutan sai inyi kusan kwana biyar ban ganshi ba, sai in nine naje Side ɗinsa”.
Murmushi mai sanyi Malam Abubakar yayi tare da cewa.
“Uhummm Alhamdulillah waraka na bisa hanya, ai bacci ga irin mai larurarsa alamun sauƙi ne”.
Cikin jin daɗi yace
“Allah yasa haka”.
Amin Amin sukace.
Kana ya kalli Sulaiman cikin kula yace.
“Sannu Sulaiman Allah ya kiyaye gaba ya taƙaita, ya sauƙaƙa mana ƙadda rorinmu, dani da kai dama sauran al’ummar musulmi baki ɗaya.”
Cikin rauni murya na rawa hawaye na kwaranya, Sulaiman ya ɗago kanshi tare da son danne shessheƙan kukan da yake taso masa yace.
“Tabbas wannan yana ɗaya daga cikin manyan ƙaddarorina masu zafi a rayuwata, na kuma samu tsira da kuɓuta cikin sauƙi, kasan cewar inda masu damar yin mgn aji.
Amman tunda na dawo Jabeer ban bar yin kukan bayin Allah’n da na bari a tsare a can magarƙamar.
Ina kuka har inji numfarfashi na yana fizga, tunda na fito na barsu ban sake samun nayi bacciba.
Inajin tausayin kaina, inji tausayinsu, nayi ta kuka dana dawo da naga halin ƙunci da iyayena da yan uwana suka shiga.
Ina tuno su kuma wanne hali iyayensu da ƴan uwansu suke ciki.”
Sosai kukansa ya tsananta cikin tsananin kukan da yasa.
Malam Abubakar zubda hawaye Sheykh kuwa sai taune lip ɗinsa na ƙasa yayi cikin tausayin waɗanda Sulaiman yake mgn a kansu koda bai sansuba.

Shi kuwa Sulaiman murya na rawa yace.
“Yara ƙanana sun sadaukar da rayuwarsu domin tawa sun amsa laifin da ba nasuba domin ni in tsira.
Ko wani hali iyayensu ke ciki, kuma dukansu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya”.
Cikin rauni Sheykh yace.
“Me sukayi ne Sulaiman?”.
Cikin wani irin shessheƙan kuka mai ciwo da rauni da tausayawa yace.
“Wanna itace tambayar da kullum sukeyiwa haukumar dake tsare damu kullum in sun shigo suna dukansu suna azabtar dasu tammaya ɗaya sukeyi mushi nee.
“Wai me mukayi ne aka kawowu nan kuke ta dukanmu ku gaya mana laifinmu”.
Zuwa yanzu hawaye sosai Malam Abubakar yake zubdawa.
Sheykh kuwa tausayi da rauni sun adaddabi zuciyarshi hawaye musu masifar zafi ke tsastsafo mishi.
Cikin rauni yace.
“To Sulaiman sun gaya maka ya kayi aka kaisu can ne?”.
Kai ya fara jujjuyawa yana kuka murya a disashe kamar mace yace.
“Sunce suma basu san me sukayi ba, kawai suna kiwo sun shiga suyi al’wala akazo akayi ta kamasu ɗaya bayan ɗaya, daga nan aka rufe musu ido, su dai sunji an kwana tafiya dasu a wannan ranar da asuba aka iso dasu wannan magarƙamar. Ƙaramin cikinsu kullum yakanyi ta kuka yana kiran iyayensu”.
Da sauri Sheykh yace.
“To amman meyasa aka tsaresu kuma su kansu basu san laifinsu ba anya ba karya sukeyi ba ko dai criminals ne, kasan suna da taurin zuciya”.
Da sauri Sulaiman yace.
“Wlh wlh su ba criminals bane, tunda na gani a gaban idona akayi musu sharri kuma akasa suka yarda dashi dole, amman sun yarda dashi ne dan su tseretar dani”.
Da sauri Sheykh yace.
“Kamar yaya akayi musu sharri?”.
Hannu yasa ya share hawayensa murya na rawa yaci gaba da cewa.
“Tun randa aka kaini wannan magarƙamar nayi matuƙar mamkin ganin waɗannan yaran, yarane ƴaƴan Fulani masu tarin kyau da farin fata, saidai yanayin wahalar da ake gana musu kullum tasa sun rame sunyi baƙi.
Mafi akasarin kwanaki sai an daukesu hotuna ana tirsasu amsa laifinsu.
Ni da yake ko muntsilina ba’ayi wlh ana dukan yaran nan ina kuka, da fari na fahimci ko isasshiyar Hausa basaji tabbacin fulanine kamar dai yadda duniya takewa Fulani kuɗin goro ga duk wanda aka ji ya iya fillanci ko yana kiwo to ya zama ba fulatani, so nima kai tsaye nai zaton fulanine kuma sai akayi dace hakan ne.

Kullum ana dukansu ina kuka.
Idan an tafi sai manya biyun su taru kan karamin cikinsu, suyita mishi tofi dan shi irin mutanen nan ne da basa jurar wahala lokuta da dama yana sumewa in an dakeshi sai daga baya ya farfaɗo, sukanyi ta kuka ina tayasu.
Daga nan muka fara sabawa, ina mamakin rauninsu kan iyaye da yar uwarsu mace da kullum suke tunota nakan ruggume karamin inyi ta kuka dan yana tuna min yarana.
A haka dai har ranar wata jumma’a nace musu dan Allah zan tambayesu me sukayi aka kawosu nan.
To anane sukayi ta rantse min da Allah suna cewa wlh tallahi su basu san me sukayi ba, kawai an kamosu daga wurin kiwone aka kawosu nan,
Babban cikinsu ya ƙara da cemin.
“Yanzu shekararmu ɗaya a nan harda watanni, kullum in an zo an dakemu da dare akan dawo ace mana mu amsa cewa mu yan kinnafin ne, sukance mu yarda kawai cewa mu yan kinnafin ne za’a dena dukanmu, mu kuwa bamu ma san menene hakan ba sai daga baya muka fahimci masu sace mutane suce a basu kuɗine ƴan kinnafin ɗin.
Yace min wlh tallahi summa tallahi mu ko gyadar gonon wani bamu taɓa sacewa mu bawa dabbobin bama, bare mu sace mutane ta yaya zamu yarda da laifin da bamuyi ba.
Har ace muyi bayani a saka a gidajen tv da Radio, to nima a ranar na basu lbrin abinda ya kawoni nan ga mamakina sai sukayi ta kuka wai sun tausaya min gwara su basa da yara sai iyaye.”
Cikin rauni Sulaiman ya ɗan tsagaita kana ya ɗago kanshi ya kalli Sheykh da sai yanzu hawayenshi suka samu zubowa.
Cikin kukan yaci gaba da cewa.
“Inda na tabbatar da cewa,
sharri akeyi musu basu san komaiba.
Saida aka fara batun belina.
Randa aka kai kuɗin sukazo sukace an kawo belina amman ba kuɗinane zai fiddani ba.
Dole sai an samu wanda za’a liƙa sharrin sune suke kawo min kayan satan ina saya ta hakane za’a nunawa duniya an kama ainihin masu satan shiyasa ni za’a sakeni.
Hankalina ya tashi ina zan samo wasu ayi musu sharri a banza tunda asalin waɗanda suka saida min saraƙunan can dai sun gudu su kansu hukuma sun kasa kamosu.
Cikin tashin hankali nace.
“Musu ni kam babu wanda zan nuna ince shike kawo min kayan sata ina saya.
Sai suka cemin to asheko zanci gaba da tabbata a cikin magarƙamar babu belin.

Ga mamaki na, sai yaran nan sukace.
To su sun amince in nunasu su, da dai ace su masu satan mutanene gwara satan sarƙa kuma zasu samu a dena dukansu dan haka gwara su yarda su ɓarayin sarƙane, sabida su dai basu san darajar gold ba, basu kuma san saraƙunan matar gwamna bane.
Haka yasa nace musu a a ni kam bazan iyaba bazan bari a ɓata musu sunanba.”
Hawayensa ya share tare da cewa.
“Sai babban cikinsu ya matsoni cikin rauni yace.
Kada mu zauna damu da kai duk mu ƙare rayuwarmu a nan.
Mu dai bamu da gatan kowa a duniya sai Allah da iyayenmu, kuma mu yanzu iyayenmu su sadakar dan zasuyi tunanin kashemu akayi.
Kuma mu bamu da yara, kai kuma kana da mata da yara da ƙanne da yayu waɗanda kaine gatansu.
Mun amince zamuce duk abinda sukeso a fidda kai.
In ka fita in ka samu dama ka nunawa duniya halin da muke ciki, kasa makusantanka su samu a Addu’o’insu tabbas munsan watan wata rana gsky zatayi aikinta, mu mun ɗaukeka matsayin ɗan uwanmu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button