GARKUWA PART 3

Dai-dai lokacin Ummi kuma ta isa falon Shatu, da gudu ta ƙara sa gabanta, ita kuwa Shatu dai-dai lokacin ta kuma yin wani irin ƙara tare da sa hannunta duka biyu ta dafe bayanta,
“La’ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam”. Ta faɗa cikin wani irin masifeffen azaban sarawar da gugunta ya fara da ƙarfi naƙudar ta baro jikin Sheykh ta dawo gareta gadan-gadan.
Cikin tsananin tashin hankali Ummi ta iso gareta,
Ruggume ta tayi a jikinta ganin yadda take karkarwa, wani irin masifeffen zufa mai tsananin zafi ya keto mata tako wani hudan gashin jikinta.
Cikin tsananin kiɗima Ummi ta fara kiciniyar zaunar da ita, jin yadda ta ƙaƙƙandare ne, yasa Ummi cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun. Sheykh! Sheykh!! Sheykh!!!”.
Ta ƙarashe kiran sunansa murya a hargitse.
Shi kuwa Sheykh wani irin ajiyan zuciya mai azaɓan ƙarfin da nauyi ya sake.
“Bismillah”. Ya furta da ƙarfi tare da yunƙura ya miƙe tsaye jin lokacin ɗaya gaba ɗaya ciwon da yakeji ya sakeshi, tamkar a zare zirin gashi cikin man shanu.
Cikin tsananin tsuma da tashin hankali ya nufi, falon sabida jin yadda Ummi ke auna mishi kira babu ƙaƙƙautawa.
Yana shiga falon.
Kuma dai-dai lokacin faya ta fashe a jikin Shatu.
“Fushhhi”.
Cikin gigita Ummi tace.
“Sheykh kayi sauri haihuwace.
Wani irin saurin isowa garesu yayi.
Yana isa yasa hannunshi ya tallabo ya mannata da jikinshi.
Cikin tsananin tausayawa yanayin da take cike yace.
“Aish! Aishhhhhhhh”.
Ina bata amsa mishi sai karkarwar da jikin ta, keyi kana hannunta na dama tasa tana nuna musu tv da har yanzu ake nuna fuskokin yayun nata, cikin tsananin wahala da azabar naƙuda da gigi da kiɗimar ganin ƴan uwanta tace.
“Yah Sheykh kalli wlh ƙarya akeyi musu, wlh yan uwana ba ƴan ta’adda bane, su kam ba ƴan kinnafin bane, wlh ƙarya akeyi musu ƙazafine”.
Ta ƙarashe mgnar da ƙarfi tare da fara wani irin gigitaccen nishi wanda yasa jikin Ummi karkarwa ta kasa koda motsa ƙafarta, bata taɓa haihuwa bata san cewa azabar haihuwa ta kai hakaba.
Shi kuwa Sheykh idonshi ya zubawa, tv inda take nuna mishi.
Yanayi yana zaunar da ita kan kujerar yana cewa.
“Aishhhhhhhh ki zauna ki nitsu”.
Cikin ƙarfi ta cakumo wuyan rigarshi sabida azabar da taji ta tsargun mata, cikin gigin wahala tace.
“Ina nuna maka su Yah Giɗi Seyo Gaini kana cemin in zauna wlh ƙarya akeyi musu”.
Da sauri yace.
“Eh A’ish na sani ƙarya akeyi musu, ki kwantar da hankalinki zan fito dasu, ki nitsu kinga haihuwa zakiyi.”
Da sauri ta rumtse idanunta wasu hawaye masu ɗumi suka kwaranyo mata ga cutar naƙuda ga fargar abinda ta gani murya na rawa tace.
“Kayi min al’ƙawarin zaka taimakawa ƴan uwana Yah Sheykh wlh basu da laifi”.
Cikin tashin hankali ganin yadda idonta suke juyewa yace.
“Nayi miki al’kawari Aysha zanyi duk iya iyawata zan fito dasu, kotu zata wonkesu fiye da yadda gurɓatattun jami’an tsaron kasar nan suka ɓatasu.
Ido ta lumshe a hankali, kana ta sake wuyanshi.
Sai kuma ta kamo hannun Ummi dake gifenta.
Cikin rawan jiki ta zamo ƙasa bisa carpet,
kanta ta jingina jikin Ummi ta riƙe ta gam-gam tare da karkarwa murya a fizge tace.
“Yah ilahi ya mujibadda’awati Yah Sheykh riƙe min ƙafata”.
Da sauri ya zamo yayi ƙasa,
hannunshi yasa yayi sama da rigarta, robar ƙugun gajeren wondon jikinta, ya kamo, da sauri yayi ƙasa dashi, ya zare shi.
Kana ya gyara mata zamanta sannan ya meda doguwar rigar tata ya rufe mata jikinta.
Hannunshi ɗaya yasa ya share mata zufar dake tsastsafo mata bisa goshinta tare da hura mata sassanyan iskan bakinshi a wuyanta.
Cikin zubda hawaye tausaya mata yace.
“Kiyi nishi Aish kiyi nishi”.
Cikin tattaro sauran kuzarinta tayi nishi mai karfi.
Ai kuwa cikin ikon Allah da sahalewarsa sai ga yarinya mace fara ƙal ta faɗo kan hannunshi da yasa ya tare.
Ita kuwa Shatu wani irin numfarfashi masifeffen wahala ta sauƙe tare da komawa ta jingina da jikin kujera.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin murmushi mai tafe da hawaye da rawan jiki yakeyi tare da kallon agogon Daimond dake ɗaure a hannunshi murya na rawa cike da rauni da tsananin farin ciki yake cewa.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Ummi ta haihu”.
Ita kuma Ummi wani irin zamewa tayi ta zauna bisa kujerar kana tasa hannun tana shafa kan Shatu tare da cewa.
“Allahu Akbar duniya Allah mai iko”.
Shi kuwa Sheykh cikin rawan jiki ya fito da yarinyar, zama yayi dirsham a gaban Shatu, tan kwashe sawunshi yayi ya buɗa gariyar jikinsa da kyau, yasa yarinyar da ita kuma taketa cillara kuka.
“Yaray, yaray, inyararray inyararray”.
Wani irin Murmushin mai cike da zubda hawaye itama Shatun tayi tare da kallon Sheykh ɗin yadda yasa yarinyar cikin jikinshi, murya na rawa tace.
“Malam Dactor Hamma Yan Sheykh me Allah ya bamu?”.
Wani irin matsowa gareta yayi jin yadda ta jero mishi sunayen dake da cikekkiyar ma’ana a gareta gareshi, jawota jikinshi yayi ya ruggumeta gam-gam cikin tsananin jin daɗi yace.
“Aysha Aish Mar’atussaliha my dear sweetheart my everything ɗiya mace Allah ya azurtamu da ita yau jumma’a ɗaya ga watan ɗaya da ƙarfe shida na yamma dai-dai”.
Cikin sanyi tace.
“Alhamdulillah Yah Sheykh Allah ya raya mana ita bisa imani ya al’barkaci rayuwar ta, yasa ta kasance mana Jabbo a ahlinmu Allah yasa ta marabci su Yah Giɗi”.
Da sauri yace.
“Amin Amin Ameeeeeeen ya rabbil izzati Allah yasa tare da Mamey na, ya Kuma amsa addu’ar da kikayi mata a matsayin mahaifiyarta”.
Amin Amin tace tana kallon fuskarshi data yarinyar, cikin sanyi ta koma ta jingina da kujera a hankali tace.
“Alhamdulillah Yah Sheykh da Junainah take kama”.
Tayi mgnar tana mai sakin kuka mai cike da raunin ganin an sake hasko fuskokin su Giɗi.
Da sauri ya ɗan ɗago yarinyar ya manna mata ita kan cikinta, kana cikin rauni yace.
“In sha Allah hawayenki zasu dena zuba, Aish da izinin ubangiji zan zame miki GARKUWA keda ƴan uwanki, naji daɗin da ɗiyarmu tai kama da tsatsonki jininki koda ban san Junainah a fuskaba ina zaton dake take kama”.
Ina zuwa yanzu bazata iya mgna ba, sabida kukan da take son dannewa.
Shi kuwa Sheykh cikin murmushin hawaye yace.
“Ummi a kawo mana kayan amsar haihuwar masarautar Joɗa zan yanke mabiyar dan ta faɗo”.
Cikin tsananin sauri Ummi ta miƙe, kai tsaye wonje tayi.
Shi kuwa Sheykh ronƙo fowa yayi kanta a hankali yasa tafin hannunshi ya share mata hawayenta, kana ya manna mata kiss kan goshinta cikin jin daɗi yace.
“Alhamdulillah Noor Hayat komai naki mai tsabta kalli haihuwarki ma mai tsabta babu jini ko ɗigo, tsabtar zuciyarki ta wadaci komai, ga Babynmu tas da ita ba datti”.
A hankali ta buɗe idonta, sosai take jin abubuwa biyu a zuciyarta a lokaci ɗaya tsananin farin ciki da kuma tsananin baƙin ciki da tashin hankali, sai dai farin cikin yana gab da danne baƙin cikin.
Hannunshi yasa ya ɗan ja ƙafarta, ya jawota kusa dashi ta matsa daga jikin mabiyar, cikin sanyi yace.
“Bari a kawo abun karɓar haihuwar masarautar Joɗa, in na yanke cibiyar sai muje Bathroom dan masu irin haihuwarki haihuwar kulle inji hausawa, sukan haihu babu jini, amman bayan kamar mintuna talatin zuwa arba’in jinin zai taho sai dai bai musu zuba da yawa yakanyi dai-dai misali ne”.
Cikin nitsuwa tace.
“To Doctor Hamma Sheykh Jabeer”.
Ummi kuwa tana fita kai tsaye Part ɗin Lamiɗo ta nufa.
A can babban falon su ta zube gaban Lamiɗo da Galadima da Abba da Gimbiya Aminatu dake dama musu fura.
Cikin kula Lamiɗo yace.
“Bisa alamu dai yau da babban Al’bishir kike tafe”.
Cikin zaƙuwa tace.
“Allah rene, Allah hokke sabbugo, Alhamdulillah Aysha matar Muhammad Jabeer ta haihu yanzun nan”.
Wani irin miƙewa tsaye Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah.”
Shima Lamiɗon da Galadima, kusan a tare suka cewa.
“Alhamdulillah masha Allah. Me muka samu?”.
Da sauri tace.
“Ɗiya mace”.
Murmushi sosai Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Allah ya raya mana ita bisa imani ya bawa mahaifiyarta lfyar shayarwa”.
Amin Amin sukace.
Gimbiya Aminatu kuwa da sauri tace.
“Taso muje da kayan amsar haihuwa”.
Da sauri Ummi tace to kana tabi bayanta, ɗakin ta suka shiga ta dauko wani babban ƙorya ta miƙawa Ummi kana suka juyo suka nufi gidan Shatun.