NOVELS

GARKUWA PART 3

Ana idar da sallan isha’i suna fitowa Sheykh yayi sauri yabi bayan Abbanshi.
Kana ya bar Jalal Jamil Yah Jafar, Yah Hashim Affan Laminu Sulaiman a bayanshi.
Da sauri yace.
“Assalamu alaikum, Abba”.
Da sauri Abban ya juyo wanda Dr Aliyu da Baba Basiru Baba Kamal Baba Nasiru da sauran ƙannen Abban nasu suka tsaya da sauri jin yana cewa.
“Alhamdulillah Aysha ta sauƙa lfy”.
Yayi mgnar a hankali ne cike da nitsuwa da zallan farin cikinsa daya kasa ɓoyuwa.
Cikin sauri Dr Aliyu ya juyo tare da cewa.
“A a masha Allah, Masha Allah”.
Baba Kamal ma kalmar yake faɗi.
Baba Nasiru kuwa cikin wani irin masifeffen tashin hankali da tsana yace.
“Me aka haifa maka?”.
Da sauri Baba Basiru yayi wani irin murmushi tare da cewa.
“Sa ranka a inuwa ƴan macece ba mai gadan mulki aka haifa mishi ba”.
Karo na forko a lokaci na forko Abbansu yasa hannunshi ya jawoshi jikinshi ya ruggume shi, gam a jikinshi tare da cewa.
“Alhamdulillah Muhammad Allah ya raya mana ita bisa imani ya bawa mahaifiyarta lfyar shayarwa da bata kekyawar tarbiya, nayi farin ciki mai tarin yawan da jin wannan Magauta zasuyi rabkanuwar aiyukansu”.

Ya ƙare mgnar tare da sakeshi.
Tabbas shi kam haihuwar nan tazo mishi da wasu abubuwa manya, wai yau shine har Abbansu ya ruggume shi.
Su kuwa gaba ɗaya tafiya sukayi.

Shima binsu a baya yayi.
Su Jalal kuwa da Yah Jafar da Jamil da Affan da sauri sukabi Yah Sheykh ɗin nasu a baya.
Sabida suna cike da mamakin yadda suka hango Abbansu ya ruggume shi.

Kusan a tare suka kutsa kai cikin falon.

Ummi dake riƙe da babban kular da tasa gasassun zabbin ne ta juyo da sauri, ta kalli Juwairiyya dake bayanta tana cewa.
“Iye gafa Daddyn Baby da Uncles ɗinta”.
Da sauri Jamil ya shigo cikin falon yana cewa.
“Kai haba dai My Adda Shatu ne ta haihu?”.
Yayi mgnar cikin zumuɗi suma sauran gaba ɗaya ido suka zuma mata jiran amsarta.
Shi kuwa Sheykh murmushi mai cike da yelwa yake, tare da zaro wayarshi a aljihu.

Ummi ce tayi dariyar jin daɗi tare da cewa.
“Wlh kuwa Alhamdulillah Shatu ta haifo mana Kekkyawar ɗiyar fulani fara ƙal”.
Kusan a tare Jamil da Affan sukace.
“Yesssss masha Allah Alhamdulillah”.
Jalal kuwa wani irin murmushi yayi mai baiyana farin cikinsa a hankali yace.
” A a kai Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah ka raya mana ita bisa imani”.

Yah Jafar kuwa da sauri ya juyo ya kalli Sheykh ga mamakinsu babu zato babu tsammani sukaji yace.
“La’ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam. Alhamdulillah Allah na gode maka, daka c nuna min wannan ranar Alhamdulillah ni Muhammad Jafar Allah na gode maka”.
Wani irin juyowa da ƙarfi Sheykh da zai shige falonsa yayi cikin tsananin kaɗuwa da tarin al’ajabi da mamaki da rantsar kokonton shin muryar Yah Jafar ce kuwa da tsawon shekaru 13 baiyi mgnaba yake mgn?.
Jalal kuwa da sauri ya koma da baya ya faɗa kan kujera sabida rawan da jikinsa keyi.
Jamil da Affan da sauri suka matso kusa dashi.
Ummi kuwa da sauri ta saki kular dake hannunta.
Ita kuwa Juwairiyya cikin tsananin kaɗuwa da tsoro ta matso gabanshi bakinshi take kallo tamkar zata cire idonta ta mannasu jikin lips ɗinsa gaba ɗaya sun kasa mgn.

Shi kuwa Sheykh da sauri ya iso gabansa hannunshi ya kamo ya riko gam gam tare da cewa.
“Yah Jafar mai-maita abinda kace Yah Jafar sake mgn inji maimata”.
Yayi mgnar da ƙarfi cike da kaɗuwa.
Ga mamkinsu sai ga Yah Jafar ɗin yayi shiru yana kallonsu Tamkar kurma.
Cikin wani irin tsuma da kaɗuwa duk suka zagayeshi.
Cikin tsananin farin ciki Sheykh ya ruggume shi gam-gam a jikinshi murya cike da al’hini da hamdala yake cewa.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!. Yah Jafar kayi mgna ka sake yin mgn dan Allah kayi mgn”.
Ya ƙarashe mgnar yana mai janye jikinshi daga jikin Yah Jafar ɗin tare dasa hannunsa bisa kafaɗunsa duka biyu yana jijjigawa.
Itama Juwairiyya cikin rauni murya na rawa cike da kukan hamdala tace.
“Yah ilahi ya mujibadda’awati ya Allah idan mafarki nakeyi ka tabbatar min dashi”.
Cikin sauri Jalal dake zaune yace.
“Ba mafarki bane Aunty Juwairiyya”.
Affan ne ya matsosu tare da haɗe su duka ya ruggume sai kawai ya saki kuka.
Ummi kuwa cikin shassheƙan kuka tace.
“Sheykh ku barshi mu bishi a hankali tabbas mgn yayi kuma in sha Allah zai kumayin mgn”.
Jamil kuwa gaba ɗaya jikinshi kerma yakeyi wayarshi ya zaro Umaymah ya kira tana ɗagawa ya fashe da sassayan kuka tare da cewa.
“Umaymah! Umaymah!!”.
Cikin tsananin ruɗani da kiɗima tace.
“Innalillahi Jamil mene! Jamil gaya min meyasa ka kuka”.
Da ƙarfi yace.
“Umaymah kukan farin cikine.
Yau Yah Jafar yayi mgna kuma ya maimaita Umaymah farin cikine ya samu kuka”.
Cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa Umaymah ta saki wayar tare da juyowa ta kalli Sitti da Jaddansu da sauran ƙannenta da babban yayansu baban Aunty Juwairiyya da Ibrahim kenan.
Cikin wani irin murmushi mai haɗe da hawaye tace.
“Sitti Jadda Jafar ya fara mgn”.
Gaba ɗaya salati suka ɗauka a tare, suka direshi da kalmar.
“Alhamdulillah ala kulli halin, Alhamdulillah lallai tabbas dukkan tsanani yana tare da sauƙin.”
Kawai sai kuma duk suka matso gaban Jaddansu da ya saki kuka kamar ƙaramin yaro cikin rawan murya yace.
“Ɗaya daga cikin burukana ya cika, kafin mutuwata ko yanzu na kwanta dama nasan bakin Jafar ya buɗu.
Sai dai har yanzu ina da wani babban buri Yah Allah ka bani aron rai da lfy ka ka baiya na min ƴata Aisha ka tsare min ita a duk inda take ka dawo da ita kan ƴaƴan ta al’farmar Annabi da al’ƙur’ani”.
Cikin zubda hawaye suka amsa da Amin Amin gaba ɗayansu.

A nan masarautar Joɗa kuwa,
Cikin tsananin tarin farin ciki Sheykh ya kamo hannun Yah Jafar ya zaunar dashi bisa kujera kana da sauri ya juya ya nufi ɗakin Shatu.
Konce ya sameta da alamun bacci takeyi.
Hannunshi yasa ya ɗauki Jaririyar kana da sauri ya juyo ya fito.

Yana fitowa kuma dai-dai lokacin Lamiɗo da Galadima da Abbanshi suka shigo falon.
Cikin sauri ya matso gaban Yah Jafar miƙa mishi ƴar yayi ga mamakinsu sai sukaji yace.
“Bismillahi”.
Cikin tsananin kaɗuwa da mamaki Lamiɗo Galadima da Abba suka zauna, Lamiɗo da Galadima da Yah Jafar bisa kan kujeru sauran kuma duk kowa na ƙasa harda Abbansu.
Kallon kallo sukayiwa juna lokacin da suka ga yana shafa kan yarinyar tare da buɗe baki a hankali yace.
“Masha Allah. Allah ya raya mana ke bisa imani yayi miki al’barka”.
Zuwa yanzu Lamiɗo da Galadima cikin kaɗuwa suke cewa.
“Jafar”.
Da sauri Sheykh ya juyo ya kalli Abbansu da tuni hawaye suke tsastsafo mishi ya kasa cewa komai sai tallabe haɓarsa yayi da hannu bibbiyu yana kallonshi.
A hankali Sheykh ya juyo kamar ƙaramin yaro haka ya iso da rarrafe.
Ya zauna gaban mahaifin nasu ya fuskanceshi da kyau hannunshi yasa ya kamo hannun Abban nasu ya zare mishi tagumin da yayi, kana yasa tafin hannunshi ɗaya ya share mishi hawayen da yakega suna zubo mishi cikin ƙarfin zuciya da tsananin farin ciki kan farin ciki murya cike da girmamawa yace.
“Abbanmu kace Alhamdulillah kada kayi kuka, Abba kaga ikon Allah ko Yah Jafar yayi mgn a yau yayi hamdala yace ya godewa Allah daya nuna masa wannan ranar muma muce mun godewa Allah mana sai ya ƙara mana wata ni’imar domin indan Allah yayi maka wata ni’imar ka gode mishi sai ya ƙara maka da wata, muce Alhamdulillah”.
Kusan a tare gaba ɗayansu sukace.
“Alhamdulillah”.
Harda shi Yah Jafar ɗin.
Ya ilahi wannan shine kyautar Allah.
Juwairiyya kam hawayenta yaƙi barin zubowa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button