GARKUWA PART 3

Lamiɗo kuwa a hankali ya dawo kusa dashi hakama Galadima, sai ya zama sun sashi a tsakiyarsu.
Abban da Sheykh kuwa suna gabansu da sauran Juwairiyya da Ummi kuwa suna gefe”.
Cikin nitsuwa Abba yace.
“Jafar! Jafar!! Jafar!!!”.
Shiru babu amsa.
Da sauri Lamiɗo ya jujjuya mishi kai tare da cewa.
“A a barshi, dole sai a hankali komai zaiyi dai-dai.”
Sai kuma ya gyara zamanshi ya kalli jikokin nashi ya juya dama da hauni kana cikin yin ƙasa da murya yace.
“Toh wannan al’amari ya zama sirri tsakaninmu har zuwa ɗan wani lokaci kada ku gayawa kowa na cikin masarautar Joɗa”.
Da sauri sukace “To”.
Shi kuwa Sheykh a hankali yasa hannunshin ya ɗauki Jaririyar ya miƙa Lamiɗo ita.
Addu’o’in yayi mata sosai kana ya miƙawa Galadima ita, sannan Sheykh ya ɗauƙeta ya miƙa Abba ita cikin murmushi yace.
“Aisha ta tafi Aisha ta dawo”.
Murmushi Ummi tayi sabida tuno irin tarin son da Abba kewa Mamey wanda shiga goma zai zaka jishi yana kira Aisha! kaxa Aisha kaza da kaza yayi kaza ko?,”.
Shima addu’o’in yayi mata kana, suka ɗan tattauna kaɗan suka tafi.
Su Jamil kuwa suma ɗaya bayan ɗaya suka amsheta.
Cikin murmushi da tarin son yarinyar Jalal yace.
“Masha Allah da Ishma take kama”.
Da sauri Jamil ya amsheta tare da cewa.
“Kace da Mamey take kama tunda Ishma dai da Aunty Rahma take kama Aunty Rahma Kuma da Mameynmu take kama”.
Da sauri Affan ya amsheta tare da cewa.
“Masha Allah wlh da Mamey take kama, Alhamdulillah Yusuf ƙarami yayi kamu”.
Ɗan shi kenan takwaran Hamma Yusuf ɗin Zahra dariya sukayi baki ɗayansu.
Kana Aunty Juwairiyya ta amshi yarinyar ita da Ummi suka nufi ɗakin Shatu.
Suna shiga suka sameta zaune bakin gado da alamun waya takeyi da Rafi’a.
“A a bazan gaya miki ba sai kinzo kiga mai aka samu”.
Tayi mgnar tana amsar Babyn da Aunty Juwairiyya ke miƙo mata.
Ita kuwa Rafi’a cikin tarin jin daɗi tace.
“Ai kuwa gobe da sassafe zan muku sammako”.
Da sauri tace.
“Rafi’a baza kizo mu kwana ba”.
Cikin dariyar jin daɗi ta e.
“Zan dai zo gobe kam da wuri”.
Daga nan sukayi sallama.
Ita kuwa Ummi abinci ta zuba mata mai rai da lfy cimar jegon gaske.
Tuƙeƙƙen tuwon shinkafa da miyar ɗanyar kuɓewa tasha man shanu da yajin daddawa da nama.
Sosai ta tasata gaba taci.
Ita kuma Juwairiyya tana riƙe da Ƴar.
Bayan taci tuwon ne kuma Ummi tasa mata gashin da yaketa tururi yaji yaji tana fifita matashi dan yayi sanyi.
Kana ta haɗa mata kunu da zuma ta bata, tanaci tana ɗan korawa.
A hankali ta ɗan jingina bayanta da gado a hankali tace.
“Ummi na ƙoshi”.
Da sauri tace.
“A a Shatu ƙara sashi kada kice zakiyi jegonku na yaran zamani jego da soyayyan Arish da tea”.
Cikin sanyi tace.
“Allah Ummi cikina zai fashe”.
Jin hakane tace.
“To sai anjima ki ƙara”.
Gyaɗa kai tayi kana ta gyara zamanta.
A can falon kuwa su Jamil duk Dinning area Suka nufa, suka zauna suka fara cin abinci.
Yah Sheykh kuwa falonshi ya wuce, wayarshi liƙe a kunne wanda Bappa yake kira.
Shi kuwa Bappa a can Rugar Bani yana zaune a tsakar gida Junainah na gefenshi su Ummey na gefenta.
Da sauri Junainah ta miƙo mishi wayar da dama Game takeyi da ita.
Amsa yayi da sauri ya amsa kiran.
Gyara zamanshi yayi jin muryar Sheykh na cewa.
“Assalamu alaikum”.
Cikin kulawa yace.
“Wa alaikassalam Muhammad”.
Da sauri ya zauna bisa kujera cikin tarin jin daɗi da son tsohon da tausayinsa yace.
“Na’am Bappa na Ina wuni”.
Fuska ɗauke da murmushi yace.
“Lfy lau Alhamdulillah Muhammad ya su Lamiɗo ya Abbanka dasu Jalal duk suna lfy koma?”.
“Alhamdulillah Bappa duk suna lfy cikin farin ciki”.
Ya bashi amsa yana murmushi.
Shi kuwa Bappa cikin kula yace.
“Yah Shatu na?”.
Murmushi Sosai yayi kana yace.
“Alhamdulillah Bappa Shatunka ta girma yau ɗazu da yamma gabanin magriba ta zama uwa”.
Cike da tsananin farin ciki Bappa yace.
“Masha Allah! Alhamdulillah yaushe ta haifu mata na samu ko aboki mai tayani kiwo?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“A a Bappa wannan Gimbiya ce amrya ka samu”.
Cike da farin ciki Bappa yace.
“Alhamdulillah Allah ya raya mana bisa imani”.
“Amin Amin”.
Yace yana mai jin muryar Junainah tana cewa.
“Ayyah Bappa bani shi Adda Shatu ce ta haihu?”.
Cikin kula yace.
“Bappa a bawa Junainah waya”.
To yace kana ya miƙa mata wayar, tare da juyowa ya kalli Ummey cikin murmushin yace.
“Alhamdulillah Shatu ta sauƙa lfy an samu ƴa mace yanzu da yamman nan”.
Wani irin ajiyan zuciya mai sanyi Ummey ta sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah yau kam zanyi bacci hankali na konce Shatuna ta haihu lfy”.
Murmushi Inna Amarya tayi tare da cewa.
“Wlh kuwa kai Alhamdulillah Metai fi haka daɗi kaji kawai ɗan ka ya haihu lfy”.
“Wlh kuwa fa”. Cewar Bappa.
Sai kuma suka juyo suna kallon Junainah dake tsalle tana cewa.
“Alhamdulillah Hamma Jabeer kace dani takeyin kama?.”
Murmushi yayi tare da cewa.
“Sosai ma kuwa Junainah”.
Cikin dariya tace.
“Allah shi ƙara dama kullum Addana sai tace wai ta fini kyau wai inada dogon bakin kwaɗayi, ni kuma kullum ince Allah yasa ta haifi irina ai zata dena cemin mummunan”.
Dariya yayi sosai kana yace.
“Toh gobe dai zaki zo mana ko?”.
Da sauri tace.
“Eh zanzo Bappa na da Ummey ma zasu zo”.
Katse kiran tayi kana ta miƙawa Bappa wayar.
Shi kuwa kiran Abboi yayi ya kara wayar a kunne tare da cewa.
“Assalamu alaikum”.
“Wa alaikassalam”.
“Barka da dare Abboi”.
“Barka dai Bappa Shatu.” Abboi yace yana murmushi tare da kallon Dedde dake gefensa.
Cikin jin daɗi Bappa yace.
“Alhamdulillah yau Shatu na ta hau matakin uwa ta sauƙa lfy mun samu ɗiya mace”.
Wani irin yalwataccen murmushi mai cike da jin daɗi Abboi yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah kai yau naji labari mai daɗi masha Allah. Kace lallai zuwa Nigeria ya kamani”.
Da sauri Bappa yace.
“Sosai ma kuwa, yanzu dai su waye zasu fara zuwa”.
Da sauri yace.
“Khadijah da Amina ƙanwar Deddena Shatun, dama nayi mgnar da mijinta tun kwanaki to yanzu kuwa zan kirashi in sanar mishi anfa yi haihuwar ba mamaki gobe ko jibi su taho da safe zuwa gidan naka.
Kaga da azahar sai su wuce masarautar da iyalin taka”.
Cikin gamsuwa Bappa yace eh hakan yayi.
Yana katse kiran yayiwa Ummey bayani cikin gamsuwa tace.
“Eh hakan yayi amman in Amina da Khadijah sun zo suje da Junainah ni sai bayan suna sai inje ko”.
Cikin gamsuwa yace.
“Eh amman bayan suna da kwana ɗaya zakije in anyi suna kamar yau sai gebe kije ko”.
“Eh hakanma yayi”. Tace cikin jin daɗi.
Shi kuwa Abboi a ya juyo ya kalli Dedde ya mata bayani.
Sosai ta shiga cikin farin ciki a take ta miƙe ta nufi ɗakinta.
Nan ta gaya Khadijah ta fara shiri Addanta ta haifu.
A masarautar Joɗa kuwa gaba ɗaya a daren labarin haihuwar Shatu ya karaɗe ko ina lungu da saƙo na masarautar.
Riskar wannan lbrin a kumnunwan Magauta yayi masifar tada musu hankali.
Hajia Mama kuwa a dare cikin masifar tashin hankali ta wuce gidan bokanta.
Tana shiga tace.
“Meyasa ne wai ku bokaye babu wasu maƙaryata a duniya sama daku, ya mukayi da kai da shaiɗanun makaranka maƙaryata. Shin ba cewa sukayi randa aka haifi yarinyar a wurin yanke cibiya zasu kashe min itaba”.
Cikin wani irin masifeffen razana ta daka tsalle tayi baya, sabida wani irin razanenne tsawa da bokan ya daka mata da ƙarfi.
Cikin ɗaga amo yace.
“Ke tafi daga can waya isa ya cutar da wanda Allah ya kare, dama ai na gaya miki babu abinda da zai samu cikin nan sai al’khairi.
Amma da yake ke tinkiyace ƙidahuma kikazo kina min ihu a kai in zaki iya cutar da itan ke kije ki gwada mana”.
Cikin tashin hankali gano tayi asarar kuɗaɗenta a banza ta juya ta fita tana cewa.
“Tabbas sai na kashe yar nan babu shakka bazata rayuba”.
Shi dai boka tsaki yaja.
Ita kuma ta juyo ta dawo hankali a masifar tashe.