NOVELS

GARKUWA PART 3

Shi kuwa Sheykh yana gama mgn da Bappa DSS ɗinsu ya kira.
Cikin hikima da iya sarrafa harshe yace.
“Sir naga wasu yaran da akayi nasarar kamasu da laifin kinnafin ko?”.
Jim kaɗan yayi tare da cewa.
“Eh yaran fulani masu kiwo ko?”.
Da sauri yace.
“Eh su waɗanda akasa suka amsa laifin da ba nasuba akan dole.”
Da sauri yace.
“A a kamar yaya laifin da ba nasuba?”.
Cikin nutsawa ya gyara zamanshi kana yayi mishi duk bayanin da Sulaiman yayi mishi ɗazu.
Cike da al’hini irin yanayin nan na ba’a mugun sarki sai mugun bafade ogan nashi yace.
“Kai Malam ni bansan da zancen nanba, kawai nasan kotu ta bada beli babu batun a nemo wasu a basu laifin da ba nasuba”.
Da sauri Sheykh yace.
“Ni nasan baka saniba dan na yarda da adalci ka yanzu me abun yi a kan lamarin yaran nan?”.
Cikin takaicin yadda wasu jami’an tsaron kasar nan suka zama azzalumai yace.
“Dole zamu kai zancen kotu ayi bayani a gaban al’ƙali a kawo Sulaiman ya bada shaida, da kuma sauran ma zauna magarƙamar”.
Cikin wani irin jin daɗi sanin muddin mgnar taje kotu.
Komai zai iya dai-dai yace.
“To ka taimaka musu a meda case ɗin yaran zuwa kotu”.
Cikin nitsuwa yace.
“Toh ba matsala”.
Suna gama wayar kuwa ya fara bincikan lmrin a afaren ya turawa wani al’ƙali rahoton.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya miƙe ya nufi ɗakin Shatu.

Tuni tayi wani baccin gajiya.
Ummi na kwance gefenta.
A hankali yace.
“Ummi bakuyi bacci bako?”.
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
“To ita dai mai jego tayi sai nida ƙawar tawane muke hira”.
Murmushi yayi kana ya matso.
Miƙawa mishi yar tayi, amsa yayi, ya zauna a bakin gado gefen Shatu.
Addu’o’in ya farayi yana tofa mata.
Kana a hankali ya kalli Shatu data buɗe ido a hankali tana kallonsu.
fuskar yarinyar ya kalla yadda taketa wawure-wawuren hannunta.
Cikin nitsuwa yace.
“Ummi yunwa nefa ya hanata bacci”.
Ya ƙare mgnar yana kallon Shatu.
Ita kuwa Ummi da sauri tace.
“Yauwa tunda ta tashi ta bata maman ta tsotsa”.
Kai ya gyaɗa kana yasa hannunshi ya kamo na Shatu ta tashi zaune.
Ɗaura mata yar yayi bisa cinyarta, kana yace.
“Bata Baloon ɗin tasha”.
Cikin ɗan yamutsa fuska tace.
“Daga yanzu?”.
Da sauri yace.
“Eh”.
Ya ƙare mgnar yana tattaro rigarta yayi sama dashi, tare da ɗan ɗago kan Baby ya saita bakinta da nimple ɗin ya manna mata.
Ai kuwa da ƙarfinta ta damƙi nimple ɗin.
Wani irin zillo Shatu tai tare da yarfa hannun cikin sakin ƴar ƙara tace.
“Wayyo Allah na Yah Sheykh zafi”.
Da sauri ya saki dariyar mugunta.
Hakama Ummi dariyar suke mata.
Ita kuwa cikin kunya ta ɗan sunkuyo tana kallon yadda ƴar taketa zuƙam nonon da har yanzu bai tsastsafo da ruwaba.
Haka nan taji wani irin son yarinyar yana shiga ta.
Tsawon 5 minute tana tsotsar bakin nimple ɗin ta,
wanda saida yayi ja yayi tsami a hankali tace.
“Zafi wlh zata cinye min nimple”.
Murmushi yayi tare da lakace hancinta kana ya janye kan yarinyar.
Ya kwantar da ita, ai kuwa gajiya da tsotson yasa tayi bacci.
Ita kuma Shatu meda breast ɗinta cikin riga tayi kana ta koma ta konta.
Sunkuyowa yayi kansu yayi musu addu’a.
Kana ya juya ya fita yana cewa Ummi.
“Sai da safe”.
Allah ya bamu al’khairi tace.
Amin yace yana fita.

Yana komawa ɗauki shi yayi shirin bacci kana ya kira Haroon da ibrahima sukayi hira sosai cikin farin cikin.

Daga nan ya kwanta.

Washe gari da safe.
Gimbiya Saudatu ce zaune a falon Shatu.
A hankali ta fito ruggume da yar a hannunta sunyi kyau sosai cikin shigar tasu.
Especially Babyn da aka shiryata cikin wasu kayan sanyi masu taushi red color and white masu masifar kyau da taushi, tayi lib a ciki.
A hankali ta kalli Shatu dake miƙo mata ƴar amsa tayi tare da cewa.
“Masha Allah, ƴarinya kam kekkyawan sai dai Allah yasa kada ta gaji Rashin kunyar uwarta da ubanta”.
Sheykh dake shigowa ne yace.
“Ai kuwa zata gada dan kyan ɗan ya gaji iyayensa”.
Cikin watsa mishi harara tace.
“Kai matarka ta haihu ka girmama bazaka bar yiwa manya rashin kunya bane wai?”.
Da sauri ta juyo ta kalli Shatu dake cewa.
“Toh ai kema baki bar rashin kunyarba bare mu”.
Cikin ta kaici tace.
“To uwar fitsara ke kiji da jegon ma mana tukun”.
Murmushi tayi tare dasa hannun ta amshi babyn da take miƙo mata tare da cewa.
“Allah ya raya”.
Karo na forko a rayuwar Sheykh da yaji Gimbiya Saudatu ta mishi addu’a ko mgn mai kyau.
Cikin jin daɗi yace.
“Amin ngd”.
Tsaki taja tare da watsa musu harara ta fita.
Murmushi yayi mai sauti ƙana ya iso gareta.
Ya ruggumeta ita da Babyn cikin raɗa yace.
“Ana Uhubbuk ya habibi Da’iman”.
Murmushi tayi dan bata gane da ita yakeba, a zatonta da yar tasu yakeyi.
Shi kuwa ganin bata gane bane sai ya share tare da cewa.
“Ɗazu nazo kuna bacci”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ummi ta gaya min”.
Da sauri ya janye jikinsa gareta, jin Muryar Mom Maman Imran wacce itace matar Abbansu ta uku.
A daƙile ya amsa sallamar tata, sai ya kuma saki fuskarsa ganin harda Abbanshi da cingam ɗinsa amaryarsa kenan.
Bayan su zauna ne Shatu ta miƙa musu ƴar ɗaya bayan ɗaya, cikin murmushin Mom tace.
“Masha Allah, tana kama da kakarta”.
Amaryar Abban ta miƙawa amsa tayi tare da cewa.
“Kekkyawar Baby Allah ya raya amaryar Habibullah”.
Da sauri Abba yace.
“Uwar gida dai, ai kece amarya kam”.
Kauda fuska Sheykh yayi kamar baya wurin.

Haka dai sukayi musu Barka suka tafi.

Haka kuma mata da maza bayi da hadimai keta yiwa Sheykh Barka a duk sanda ya gilma cikin masarautar.

Rafi’a kuwa tazo wanda zuwanta yasa Shatu ƙara sakewa sosai gashi Khadija tace mata gobe zasuzo da sassafe, dan jirgin dare zasu biyo da yauma zasu isota.

Alhamdulillah kuma bayan sallan isha’i suka iso.
Salmanu ne ya ɗauke su ya kaisu Rugar Bani, shima zai kwana can saida safe zai taho dasu.

A masarautar Joɗa kuwa abin mamaki kowa yazo barka yaga baby ammma.
Banda Hajia Mama, Mami Matar Affan kuwa kusan nan Part ɗin Shatu ta wuni dan suna masifar ɗasawa.

Washe gari da safe, Aunty Amina ƙanwar Dedde da Khadijah ƙanwar Shatu da Inna Amarya da Junainah suka shirya zuwa masarautar Joɗa.
Inda Ummey ta haɗawa Shatu man shanu, kwan zabbi yajin daddawa dana borkono da zuma da madarar shanu, ko wanne mai yawa suka taho mata dashi.

Ƙarfe tara da rabi dai-dai Salmanu yayi parking a asalin babban gate ɗin masarautar Joɗa.
A hankali ya juyo ya kalli Khadija dake gefensa yace.
“Kira ta ki gaya mata kun iso a turo masu shiga daku”.
To tace kana ta kira Shatu.
Tana ɗagawa tace.
“Assalamu alaikum ƴar uwa rabin jiki kun isone?”.
Da sauri tace.
“Eh mun iso muna babban gate ki turo azo a shigo damu naga masu jajayen rigunar nan sai kallonmu suke tayi”.
Da sauri tace.
“Toh ba matsala bari yanzu Jamil ko Jalal zaizo”.
Tana faɗin haka ta katse kiran, tana ruggume da Babyn ta nufo falon.
Tana fitowa ta hangosu can bisa.
Dinning table suna yin breakfast harda Yah Jafar.
Da sauri Ummi ta nufi inda take tare da cewa.
“Yah dai Shatu kina son wani abune?”.
Gyara riƙon da tayiwa Babyn tayi tare da cewa.
“Eh Ummi dama su Junainah ne suka zo, suna can babban gate to inaso a shigo da sune”.
Da sauri Ummi tace to kana ta juyo tana ƙwalawa Sara dake kitchin kira.
Da sauri ta fito tare da cewa.
“Na’am”.
Cikin kula tace yauwa dan Allah jeki can bakin babban gate ki shigo da baƙi”.
Da sauri tace to kana ta fita.

Tana isa tace su shigo da motar har Salmanu yace a a sai kuma yace to sabida tuno akwai kaya.
A hankali tayi gaba motar na binta a baya suna kutsa hancin motar cikin masarautar Joɗa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button