GARKUWA PART 3

Ita kuwa Junainah a hankali ta kalli Ummi data iso gabansu.
Tare da kallon yadda suke a hankali tace.
“Uhm autar Mamey kawo ɗiyar taki in kaiwa su Inna Amarya ita”.
Da sauri tace.
“Toh”. Ta ƙare zancen tana miƙa mata ƴar.
Jalal kuwa ido ya zubawa Ummi.
Sheykh kuwa juya kanshi yayi yana kallonta yana nazartan kalmarta, itama taga kamar kenan.”
Ya faɗi a ransa.
A fili kuwa murmushi suka ga Jafar yayi tare da miƙewa tsaye murya can ƙasa yace.
“Autar Mamey nima haka idona ke sanarwa zuciyata Ummi”.
Da sauri suka kalleshi.
To daga jiya zuwa yau dai sun saba da yayi mgn a fizge sai dai bai kuma ƙarayin wata duk mgnar sa za’ayi mishi.
Yana faɗin haka shi kuma ya juya ya tafi.
Da sauri Jalal yabi bayanshi.
Affan kuwa a hankali ya miƙe ya fita ya nufi falon Hajia Mama.
Jamil kuwa sashin Gimbiya Aminatu ya nufa.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya yunƙura ya gyara zamanshi ya koma bisa kujera, kana ya kalli Junainah dake tsaye tana gyara tarhan da tayiwa ɗan kwalin hijab din jikinta.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
“Wannan ɗayar itace Ummey?”.
Da sauri ta matso kusa dashi a hankali tace.
“A a Ummeynmu tana gida bata zoba.
Wannan Aunty Amina ce ƙanwar Dedde, ɗayar kuma Inna Amarya ɗayar kuma Adda Khadija ƙanwar Adda Shatu ne. Na fita kyau ko?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Sosai ma kuwa, ke mai zubin larabawa”.
Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
“Yessss my Hamma ka iya gayan gsky”.
Sai kuma ta juya ta nufi falon Shatu tana cewa.
“Bari inje inga Adda na da kyau”.
Da ido ya rakata.
Jamil kuwa yana shiga ya gayawa Gimbiya Aminatu cewa wasu baƙi sunzo wurin Shatu da wata yarinya mai kama da Mameynsu.
Tofa wannan al’amari yasa Gimbiya Aminatu sanarwa Lamiɗo haka, da kanshi yace taje tai musu sannu da zuwa.
Yah Jafar kuwa yana shiga, falon shi ya samu Juwairiyya na tsaye.
A hankali yaja hannunta suka wuce bedroom ɗinsa.
Haka nan yaita maimaita kiran sunanta tana amsawa.
Shi kuwa Jalal juyawa yayi ya fita.
Affan kuwa a hankali ya kalli Hajia Mama cikin sanyi yace.
“Mama ƴan uwan Shatu sun zo, sai kinga wata yarinya mai kama da Mameynmu, ko muryarsu iri ɗaya, anjima kije ki ganta”.
Cikin tsuke fuska tace.
“Toh uban marasa zuciya, kullum kai ke cemin in jene”.
Da sauri ya kuma juyo ya kalli Rumaisa yayarshi.
Dake jan dogon tsaki tare da cewa.
“Shi bai san damuwar mutane ba, da kishin uwarsa, kana da rashin kunyar da yarinyar nan kewa Mama kake wani cewa taje taga ƴan uwanta.”
Idonshi ya kuma juyowa kan Maman tasu jin tana cewa.
“Barshi sakarai ni ko ƴar da aka haifanma banje na ganiba bare wata can baƙuwar ba hillatanar daji, mitssssss”.
Cikin sanyin jiki yace.
“Uhumm”.
Daga nan bai kuma cewa komaiba, baisan komai kan makirci mahaifiyar tashi ba, iya saninsshi tana son su Yah Sheykh fiye da yadda take sonshi sai dai wasu lokutan yana zargin tana da wani manufa a kansu.
A hankali ya miƙe ya fita ya nufi Part ɗinsa.
Ita kuwa Hajia Mama cikin fidda numfashi ta kalli Rumaisa tare da cewa.
“Sai gobe zanje duba jaririyar, kuma zanje da garin batur, tabbas zan zuba matashi a baki.
Tana haɗiyewa zai tsistsinka ƴaƴan hanjita ta mutu kowa ya futa, shegu masu yawan haihuwa”.
Cikin cin daɗin haka Rumaisa tace.
“Dai-dai kenan”.
Gimbiya Aminatu kuwa anayi sallan la’asar taje,.
Tabbas itama tayi mmkin kamannin.
Koda ta dawo ta sanarwa Lamiɗo da Abba da Gimbiya, cikin al’ajabi Lamiɗo yace.
“Yarinyar zata kai shekara nawa?”.
Da sauri Gimbiya Aminatu tace.
“To gsky bana ceba dan irin yaran nanne masu jiki ɗan cafal ba wawan girma ku ba ƙaramin ruwa da wuya ka iya ƙiyasce shekarunta kai tsaye”.
Wani irin dogon numfashi Abba ya sauƙe tare da cewa.
“Shi Muhammad ɗin zai tambayi yayar tata”.
Galadima kuwa cikin nitsuwa yace.
“Uhummm babu shakka akwai abinda ke shirin tabbata daga zantu kan Malam Musa, yace ƴa mace mai kama da ita zata fara zuwa kafin ita.
Amman bai saniba ƴartace ko ba tataba, ya kuma ce mana a haihuwar matar Muhammad ne zai sanadin zuwanta.
Tabbas bawai munyi imani da abubuwan daya faɗa bane. Wasu ma mun mancesu.
Sai dai gashi bayan shekaru goma sha biyu abubuwan daya faɗa sun fara baiyana na aure ba fullatar daji.
Sai kuma batun haihuwarta da zuwan yarinyar koda banga ƴarba inaji a jikina itace ƴarinyar dayake nufin”.
Cikin nitsuwa Abba ya gyara zamanshi a hankali yace.
“Ni dai yanzu inga yarinya ce damuwa ta, inji shekarunta.
Domin na sani tabbas kafin Aisha ta haɗu da ibtila’in juyewar halinta wlh tanada shigar juna biyu wanda ita kanta bata saniba, saida na gaya mata.
dan lokacin baifi kwanaki ba.
Kuma har bayan ta juye naci gaba da jin abubuwan da nakeji muddin tanada juna”.
Cikin rauni ya ƙarashe mgnar.
Daga nan sukaci gaba da tattaunawa kan batun.
Washe gari yau kwanan Baby uku da zuwa duniya.
Ƴan uwa da abokan arziƙi duk sun zo, kab Masarautar Joɗa hatta matar Galadima da take tsohuwa sosai tazo, sai Hajia Mama ce kaɗai bata zoba.
Zaune suke a falon Shatu.
Lokacin suka dawo daga yiwa Inna Amarya rakiya dan Salmanu yazo ya ɗauke ta ya meda ita gida.
Ya rage Khadijah Aunty Amina da Junainah.
Zaune suke a falon Shatu, Ummi ce zaune gaban Shatu ta zuba mata abinci a plate ta bazashi yayi sanyi.
Kana tana jujjuya zumar data saka mata cikin kunun tsamiyar data dama mata mai citta.
Cikin sauƙe numfashi Aunty Amina tace.
“Oh ikon Allah ko ina da al’adarsu mu ai mai jego in dai abinci yayi sanyi to bazata cishi ba”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Uhum kinga mu kuma nan sai abincin yayi sanyi ƙalau ma kafin mai jego taci, tai wonka da ruwan sanyi, tasha mai sanyi taci mai sanyi kuma babu abinda ke damunsu”.
Hannu Shatu tasa ta amshi ɗan ƙwaryar da kunun yake ciki ludeyin dumar tasa ta ɗan ɗebi kunun ta kurɓa, ido ta ɗan lumshe dan tana jin daɗin shi a bakinta.
Ita kuwa Aunty Amina riƙon da tayiwa Babyn ta gyara tare da cewa.
“Gari banban Allah ɗaya kenan”.
Junainah ce ta miƙe tsaye alamun zata fita.
Shatu ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
“Ina zakije Junnu?”.
Ba tare da ta juyo ba tace.
“Zanje kitchen wurin Adda Khadijah da Sara in tayasu girki”.
Sai kuma tayi sauri ta ɗan ja da baya, ganin Sheykh da sauri tace.
“Hamma Jabeer ina kwana”.
Murmushi ya ɗan yi tare da cewa.
“Lfy lau Alhamdulillah”.
Sai kuma ya ɗan juya tare da cewa.
“Yauwa Junainah jeki kira Adda Shatu kice tazo da Baby”.
To tace kana ta koma ciki shi kuma ya nufi ɗauki sa.
Bayan ta gayawa Shatu saƙon nashinne ta juya zata fita kuma tayi kiciɓis da Hajia Mama da hadimanta.
Cikin zuba mata ido Hajia Mama ta ɗan kauda kai ta wuce.
Ummi ce ta ɗan miƙe tare da cewa.
“Sannu da zuwa”.
Cikin sakin fuska tace.
“Yauwa Ummin Jabeer ina kishiyar tawa kishiya ban haushi”.
Ta ƙare mgnar tana zama bisa kujerar dake gefen Ummi ya zama suna fuskantar juna da Shatu.
Cikin sakin fuska Aunty Amina tace.
“Ina kwana?”.
“Lfy lau Alhamdulillah ya yar jikallena?”.
Hajia Mama ta faɗa.
“Gata lfy lau”.
Aunty Amina ta faɗa tana yunƙurin tashi zata miƙa mata ƴar.
Da sauri Shatu tace.
“A a Aunty Amina kada ki bata ita dan Allah”.
Da sauri tace.
“Sabida me?”.
Ajiye kwaryar hannunta tayi tare da cewa.
“Haka kawai”.
Ta ƙare mgnar tana miƙo hannun ta amshi ƴar.
Tare da jan dogon tsaki kana a hankali tace.
“Aniyar kura tabi daji aniyar moɗa tabi randa, wannan dai nan gani nan bari da izinin ubangiji”.
Ta ƙare mgnar tana juyawa ta fita ta nufi falon Sheykh.