NOVELS

GARKUWA PART 3

Gobe za’a zauna a kotun.

Alhamdulillah yau kwana biyar da haihuwar Shatu.
Anata shirye-shirye bikin suna.
Su Umaymah ma yau tunda safe suka iso, ita da Hibba da Aunty Rahma da Mamma da Ishma.
Sai Haroon da Jannart ɗinsa.
Gaba ɗaya gidan ya cika da ɓakin.

Junainah kuwa tun kafin su iso take Part ɗin Mami matar Affan da yaransu Zahra’n Hamma Yusuf ce da tazo take zana musu lalle.

Gaba ɗayansu cike suke a falon.
Sai hadimai dake can kitchen sunata faman aiki.

Umaymah ce riƙe da jaririyar cikin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah yau gani riƙe da Yar Jazlaan.
Alhamdulillah ƴarinya kuwa sak Mamey.
Cikin sauri Aunty Rahma ta ajiye cup ɗin da take shan ruwan da shi tare da leƙo fuskar ƴar tace.
“Alhamdulillah kuce dani take kama”.
Murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
“Sosai ma kuwa”.
Jamil ne ya ɗan jujjuya kanshi tare da cewa.
“Yoh ai ke masu kama dake sunada yawa Adda Shatu ina Junainah ne”.
Khadija ce ta ɗan kalleshi tare da cewa.
“Uhumm Junainah kuwa Sarkin yawo tun da sassafe ta tafi gidan Affan har yanzu bata dawoba”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Tanada saurin sabone ba ruwanta kowa natane”.
Kai Sheykh ya jingina jikin kujera yana kallon Shatu dake lumshe idonta alamun bacci takeji.

A hankali Jalal ke tafiya tana riƙe da yatsarsa manuniya tana ɗigirgire da sawunta.
Wanda takalmanta ke hannun Jalal ɗaya cikin yawan surutunta tace.
“Yah Jalal lallena zai ɓaci fa.
Ni mu zauna a nan sai ya bushe mu tafi”.
Sunkuyowa yayi ya ɗan kalleta fuska ɗauke da murmushi yace.
“Mun isofa Junnu saura kaɗan”.
Tura baki tayi dai-dai lokacin da yasa hannunshi ya tura ƙofar tare da sallama a bakinshi.
“Ni dai bana son Junnu Hamma Jabeer yace ba kyau ace Junainah yafi daɗi”.
Tayi mgnar tana ƙara riƙo hannunshi.
Da sauri Umaymah ta kalleta ta kuma juyo ta kalli Ishma dake lafe jikin Shatu.
Ita kuwa Junainah da sauri ta saki hannun Jalal tare da rugowa a guje tare da cewa.
“Lah oyoyo Ummey na”.
Tayi mgnar tana nufo gaban Aunty Rahma data hango tamkar Ummey’nta.
Da sauri ta tsaya tare da cewa.
“Laah”.
Sai kuma ta juyo ta kalli Ishma kana ta kalli Aunty Rahma.
A hankali ta ɗan matsa kusa da Shatu cikin yanayin jin kunya tace.
“Ina kwana”.
Ta ƙare mgnar tana kallon Aunty Rahma da suma duk ita suke kallo.
Da sauri Mamma tasa hannunta ta kamo hannun ta jawota kusa da ita kusan a tare sukace.
“Ikon Allah kenan dan Allah kalli kama”.
Murmushi Shatu tayi tare da cewa.
“Ai natama dana Ishma wasane na Ummey na da Aunty Rahma shine gaske”.
Cikin sauri Jalal yace.
“Dan Allah yaushe Ummeynki zata zo mana ne kam”.
Murmushi Aunty Amina tayi tare da cewa.
“Ai kam zata zo wata rana amman ba yanzuba”.
Da sauri Aunty Rahma tace.
“Ai kuwa in sha Allah mu kam zamuje mu ganta”.
Junainah ce ta ɗan lafe jikin Mamma tana kallon Umaymah a hankali tace.
“Itama ai zata zo taga Baby”.
Murmushi Umaymah tayi tare da shafa fuskarta.

Hibba kuwa Jawo Ishma tayi ta ajiyeta kusa da Junainah hota ta fara ɗaukansu tana cewa.
“Masha Allah tagwayen kamanni”.
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
“Wlh kuwa”.

Ranar dai haka suka wuni.
Anata hira da raha.

Ranar suna bayan sallan asuba, aka raba goro da dabino.
Kana akayi yanka yarinya taci sunan Ummey kuma Mamey Aisha.
Jamil na shigowa ya faɗawa Umaymah dasu Mamma dake cike a falon.
Da sauri Hibba tace.
“To da wanne sunan za’a kirata?.”
Shiru Shatu dake cikin shiga ta al’farma tayi tana kallonsu.

Khadija ce ta ɗan gyara zama tare da cewa.
“Afreen yayi”.
Da sauri Jamil yace.
“Sosai ma kuwa kin iya zaɓi mai kyau kamar yadda kike mai kyau”.
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa cikin kunya, sai kuma ta tashi da sauri tayi falon Shatu jin Jamil ɗin na cewa.
“Umaymah tayi ko surkaki ce”.
Ya ƙare mgnar yana kallon Shatu.
Murmushi sukayi tare da cewa.
“A tayi sosai ma kuwa”.
Sai kuma yace.
“Ko dai baza’a bani ita bane Adda Shatu?”.
Da sauri tace.
“A a ni kam banceba ba ruwana, ai ina ganinku bini-bini kuna tare”.
Sheykh da yanzu shigowarsa ne yace.
“In ka nitsu mu baka ita in Kuma baka bar ƙelle-ƙellen idoba da kallon mata mu habaka its”.
Ƙeyarshi ya sosa tare da cewa.
“A ai yanzu na girma na bari ko Yah Haroon.”
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Haroon dake bayan Sheykh.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Shi kuwa Haroon zama yayi gefen Mamma tare da cewa.
“Ai kam yanzu ka girma”.

Ummi ce ta fito daga kitchen da akoshin cike da hanta gashin tukunyar da akayiwa Shatu.
Sai Jannart kuma riƙe da gashin da tayi musu nasu daban.
Sara da Larai kuwa da sauran duk riƙe da manyan Foodflaks suka shigo dasu a hannunsu.
Kana suka koma suka dauko plates da cups da spoons.
A tsakiyar falon suka ajiyesu.

Nan suka taru gaba ɗayansu suka zauna a falon.
Harda Junainah.

Aunty Amina kuma da Khadijah da Shatu falonta suka tafi.
Shi kanshi Sheykh a nan kusa da Umaymah ya zauna a plate ɗaya sukeci shida Haroon.
Ishma da Junainah.
Jannart da Hibba da Aunty Juwairiyya.
Rahma Kuma ita da Mamma Umaymah kuwa ita da Ummi.
Jalal da Jamil.

Affan kuwa yana can Abuja bai dawoba shida Sulaiman da Malam Abubakar sai dai Alhamdulillah shariya tayi kyau babu jeka ka dawo kasan cewar akwai manyan shaidu kuma ga yawan Addu’o’in iyaye da yan uwa kan su Gaini da Addu’o’in masallatan jumma’a kana ga taimakon gskya. Da samun ƙwararren lawyer da kuma sa bakin babban mutum Lamiɗo da Jadda da kuma shi kansa Sheykh.
A ranar kotu ta wonkesu tsab.
Kana akayi ram da Dineal dama sauran ɓata garin jami’an tsaron kasar da suke da hannu cikin irin wannan kitimurmurar.

Shi kuwa Sheykh Affan ya gaya mishi komai amman yaƙi ya yardama suyi mgnar da Shatu da zaran ta fara mishi mgnar sai ya zille yafi son yayi mata ba zata.

Bayan duk sun gama cin abinci ne, kowa wacce ta fesa wonka da kolliya
Sosai sukayi kyau cikin shiga ta al’farma, Hajia Kubra ma tazo.
Dama sauran abokan arziki.

A hankali Sheykh ya meda ƙofar ɗakinshi ya rufe, tare da amsa kiran Hajia Mama.
Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
“Hahaha shegu zanyi mgninsu yau.
Tuni fatar ragon sunan ya shiga hannuna na gama yin shirina har na meyar musu da ita.
Da sauri cikin tsoro yace.
“Toh me kikasa a cikinta”.

Dai-dai lokacin kuma sairkin al’adun Sunan masarautar Joɗa ya shigo falon wurinsu Umaymah tare da Gimbiya Aminatu da
Yana riƙe da fatar ragon sunan.

Bayan sun zauna ne ya sun gaisa ya shimfiɗa fatar ragon sunan.
Tare da miƙowa Ummi dake riƙe da Afreen yace.
“Masha Allah kawo Aisha ƴar Aysha jikar Aisha mu cika mata masakinta”.
Da sauri Ummi ta miƙa mishi Afreen dake naɗe cikin shawul fari ƙal mai taushi da ɗaukan, ido.

Hannunshi yasa ya fara zare Shawul ɗin yayi kana ya fara cire mata kayan jikinta ya rage daga ita sai Pampers.
Aunty Rahma ce ta ɗanyi ajiyar zuciya tare da cewa.
“Kai wannan masarautar Joɗa taku tanada tsarabe-,tsaraben al’adu masu masifar tsauri.
Allah ya baku cikekken ahlul sunna ya mulki masarautar shine kaɗai zai kauda al’adun ya wanzar da sunna, ina dalili a ninke yarinya cikin ɗanyen fata ayi ta garata a tsakiyar ɗakin mahaifiyarta ai ko ba’ayi hakaba dole zata san ɗakin uwartace”.

Umaymah ce ta ɗan gyara zamanta tare da cewa.
“Toh ya zamuyi tunda abu nasune”.
Gimbiya Aminatu ce tayi murmushi tare da cewa.
“Watan wata rana dai tabbas al’adun zasu kau sunna ta wanzu in wanda muke zaton ya yarda ya amshi masarautar”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button