NOVELS

GARKUWA PART 3

Allah ya sa haka.
Umaymah tace.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Suna masu kauda kansu kan fatar dan wani irin warin da basu gane kamsaba da fatar keyi wanda dole in kaji zakayi zaton ƙarnin ɗanyar fatarne.
Wanda fiyafiyen ya gauraye dashi sai dai shi kanshi sarkin al’adun sunan kauda kanshi yakeyi dan azabar warin fiyafiyar da Hajia Mama ta turbuɗa cikin fatar.
Kansu suka ɗan kakkauda tare da cewa.
“Dan Allah kayi maza ka gama ka fito da baiwar Allah”.
Cewar Umaymah da Mamma.
Shi kuwa Sarkin al’adun suna murmushi yayi tare da naɗa Afreen cikin fatar ragon sunan,
da Hajia Mama ta gama zazzaga mata madarar fiyafiya mai masifar ƙarfi.
Sai dai da yake fatar a ninke take yana kuma warewa ya naɗe da sauri to sai ya zama kamar a rufe yake, shiyasa basu ji wari sosai ba.
Dan duk wari shi ai in a rufe yake bakajin warin sosai.
Cikin murmushi mugunta ya haɗe yarinyar ya ninke ciki ya matse da ƙarfi kana ya ɗagata ya nufi Bedroom ɗin Shatu.
Zaune ya sameta bisa bakin gado.
Tayi masifar kyau cikin wata dakekkiyar Getzner Orange color mai masifar kyau da sheƙi.
Khadija na tsaye gefenta tana ninke ɗan kwalin zatayi mata ɗauri.
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli Sairkin al’adun Suna cikin mamaki tace.
“A bawan Allah ya da kawo fatan rago kuma har cikin ɗaki”.
Cikin yin ƙasa da kai yace.
“Al’adar ranar suna zamuyi”.
Hannunta tasa ta dafe kanta kana ɗaya hannun ta ɗaurashi kan ƙirjinta dake harbawa da azaban ƙarfi da sauri-sauri kuma.

Aunty Amina ce tace.
“Kai gsky yana wani irin wari fa”.
Ummi dake biye dashi a baya da ita da Umaymah da Gimbiya Aminatu ne suka haɗa baki wurin cewa.
“Toh ka fara mana”.
Juyowa Khadijah kam tayi ta zauna tana kallon ikon Allah.
Itama Aunty Amina hannu tasa ta dafe haɓarta tana kallon ikon Allah.

Dan dagasu har Shatu basuma gane cewa.
Afreen ce a naɗe a cikiba.

Shi kuwa a hankali yake komai yana mai jin yadda yarinyar take mutsu-mutsun neman ceton rai sai ƙara danneta yakeyi.
Ƙarshen ginin ɗakin yaje kana ya sunkuya ya ajiyeta tare da garata ta gangaro har gaban gadon.
Tuni zuwa yanzu numfashin yariyar in ya fita baya komawa.
Gaba ɗaya fatan jikinta yayi jazir idanunta sun ƙaƙƙafe.

A can ɗakin Sheykh kuwa cikin tsananin hatsala da gajiya da dariyar muguntar da Hajia Mama ke kerketa mishi cikin kunnensa tsawon lokaci a tsale yaja tsaki tare da cewa.
“In kin san bazaki gaya minba meyasa kika kirani ina tambayarki me kikasa cikin fatar ragon sunan kina tamin dariya”.
Cikin dariyar mugunta tace.
“Hahahahahhh madarar fiyafiyar mai surke da garin sukudaye na turbuɗa cikin fatar da nasan yanzu ana can an naɗe musu ƴar tasu a ciki, kafin miti biyar da za’ayi ana garata ta zama gaw…”
Cikin wani irin tashin hankali ruɗani da firgici da gigita ya cilla wayar ya liƙata da jikin gini a take ta buɗe batir ɗin ya rabu da wayar.
ba tare daya bari ya ida jin me zata ceba.
Cikin tsananin tashin hankali ya fito da gudu.
Gaba ɗaya jikinsa tsuma da karkarwa yakeyi tamkar mazari namfashinsa tamkar zai bar gangar jikinsa.
Daga falonshi yake rabkawa Shatu da Umaymah kira da ƙarfi yana cewa.
“Aysha! Aysha!! Umaymah! Umaymah!!! Ummi! Kada ku bari asa Ƴarinyar nan cikin fatar nan”.
Da sauri Aunty Rahma da Aunty Juwairiyya da Haroon da Jannart suka miƙe tsaye.
Da sauri Haroon ya nufi falonshi su Jamil ma kan tashi tsaye sukayi jin yadda yake mgn da azaban ƙarfi.
Kiciɓis sukayi da harun.
Da ƙarfi yace.
“Haroon ina Aysha ina Baby Ina Umaymah?”.
Cikin tsoro Aunty Rahma tace.
“Suna ɗakin Shatu ana al’adar fata”.
Da ƙarfi ya ture Haroon dake gabanshi.
Cikin tsananin masifar tashin hankali da ruɗani ya nufi Bedroom ɗin Shatu.
Wanda haka yasa suka kab suka bishi a baya.

Da sauri Shatu ta miƙe tsaye tare da cewa.
“Na’am Yah Sheykh”.
Sabida jin yadda yake abka mata kira tare da cewa.
“Aysha Aish Ina kike ina ƴata?”.

Kiciɓis sukayi a bakin ƙofar shigowa ita zata fita shi zai shiga.
Da sauri tasa hannun shi ya tureta har saida ta faɗa jikin Umaymah sabida hango Sarkin Al’adun suna yana gara Afreen dake cikin fatar a ƙasa a tsakiyar ɗakin.
Cikin wani irin masifeffen tashin hankali yasa hannunshin da ƙarfi ya ture sarkin al’adun sunan
Ya faɗi ƙasa tib.

Cikin rawan jiki da tashin hankali Umaymah da Ummi sukayi kanshi.
Aunty Amina da Khadijah kuwa cikin mamaki suka zuba mishi idanu.

Su Aunty Juwairiyya kusa duk shigowa sukayi cike da mamaki.
Ita kuwa Shatu da sauri ta gyara tsayuwarta tare da nufoshi.
Ganin yadda gaba ɗaya jikinshi ke karkarwar tamkar mazari.
A gigice ya sunkuyo ya zaro Afreen dake naɗe cikin fatar da sauri ya fara worwore fatar.
Gani yakeyi ma tamkar baya sauri murya na rawa hankali a tashe yake cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil Aish zasu kashe mana ita.”
Dai-dai lokacin kuma ya gama woreta.
Cikin wani irin tashin hankali Ya juyo a gigice yace.
“Innalillahi Umaymah sun kashe min ita”.
Jiki na rawa hankali a tashe Umaymah ta iso gabanshi da sauri tasa hannunta ta amshi yarinyar ganin yadda jikinsa ke karkarwar.
Da Sauri ta juyo gaban Gimbiya Aminatu tare da cewa.
“La’ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam.
Ta rasu.”
Da ƙarfi Shatu tace.
“Innalillahi Umaymah me kikace kada kice haka dan Allah ku duba da kyau”.
Cikin tsananin tashin hankali Gimbiya Aminatu ta amshi Afreen jujjuya yaya tayi da sauri tace.
“Ta…!

                       By
         *GARKUWAR FULANI*

4/6/21, 4:15 PM – &: “Ta Suma ne!”. Da sauri Sheykh ɗin ya taso, tare da sa hannunshi ya amsheta, da sauri ya juya.
Itama Umaymah da sauri tabi bayanshi.
Side ɗinsa ya koma da sauri key ɗin motarsa ya ɗauka Umaymah na biye dashi a baya kana Haroon ma na biye dasu a baya.

Shatu kuwa cikin wani irin kuka mai rauni daya kubce mata ta koma bakin gado ta zauna gaba ɗaya jikinta kerma yakeyi.

Shi kuwa Sarkin al’adun suna, da rarrafe ya fita ya bar ɗakin yana fita falon ya miƙe a guje ya bar Part ɗin da sauri Jalal ya mara mishi baya, kafinma ya bar Part ɗin ya damƙeshi Part ɗinsu ya wuce dashi.

Mamma kuwa da Gimbiya Aminatu gefen Shatu suka zauna.
Hannunta tasa bisa kafaɗarta a hankali tace.
“Kiyi haƙuri Aysha in sha Allah babu abinda zai samu ƴarki da izinin ubangiji, zata samu lfy”.
Cikin rauni murya na rawa ta juyo ta kalli Mamma ido cike da hawaye tace.
“Mamma me tayi musu, da zasu cutar da ita ba tare da haƙƙinta ba, shike nan yanzu duk magautan Yah Sheykh sai su dawo kanta, kawai dan ta kasance ƴarsa, Mamma ya zamuyi”.
Da sauri Gimbiya Aminatu tace.
“Babu komai Shatu da izin Ubangiji baza suci nasara a kankuba”.

Aunty Rahma da Aunty Juwairiyya da Jannart kuwa jiki a mace suka koma falon Shatu suka zauna.
Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi.

Khadija da Aunty Amin kuwa tsoron al’amarin masarautar Joɗa ne ya rufesu.

Da sauri Mamma ta miƙa ganin Shatu ta zabura ta miƙe tsaye da sauri tare da tallabe breast ɗinta.
“Aysha zauna”.
Murya na rawa tace.
“Mamma maman Afreen na tsastsafo da ruwa,
Ina Yah Sheykh ya tafi da ita? Ni kam zanje inga halin da take ciki”.
Ajiyan zuciya mai nauyi Hajia Kubra dake tsaye gefen Mamma tace.
“Asibiti suka tafi, kuma insha Allah zataji sauƙi”.
Kai Gimbiya Aminatu ta gyaɗa tare da cewa.
“Sosai ma kuwa tunda har kikaji haka to ta farfaɗo ne”.

Dai-dai lokacin kuma Umaymah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin da Sheykh da wasu manyan likitocin su na Valli Hospital Suka shiga da Afreen a sume.
Ta sauƙe wata ƙaƙkarfan ajiyan zuciya jin kukan da Afreen ta cillara da ƙarfi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button