NOVELS

GARKUWA PART 3

A cikin ɗakin kuwa.
Kusan a tare sauran likitocin suka sauƙe ajiyan zuciya tare da ɗagowa suna kallon Sheykh daya ruggumeta jikinshi tare da cewa.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!”.
Sai kuma ya juyo da sauri ya kalli Dr Lukman Ibrahim babban likitan yara kenan na asibitin na cewa.
“Ina Maman baby a yi maza a bata mama tasha shi zai taimaka wurin ƙara ƙarya ƙarfin gubar”.
Da sauri Sheykh yace.
“To”.
Kana ya juya.
Yana fitowa Umaymah tabi bayanshi.
Tana tambayarshi.
“Ta farfaɗo ko?”.
Cikin ƙara saurin tafiyarsa yace.
“Eh Umaymah”.
Suna shiga motar yaja da sauri ya nufi masarautar Joɗa a guje.

A can part ɗinsu Jalal kuwa.
Wani irin gigitaccen mari Jalal ya yarfawa Sarkin al’adun suna.
Wanda yasa shi jin fitsari ya kubce mishi.
Ba tare daya gama dawowa hayyacisa ba ya kuma jin saukan wasu tagwayen maruka a gigice ya kurma ihu tare da cewa.
“Wayyoooooooo Allah na na shiga uku ni ilu Jalaluddin kayi haƙuri”.
A fusace Jalal yasa ƙafarshi ya taɗe sawunshi har saida ya faɗi tib! A ƙasa hannunshi yasa ya tallabe ƙeyarsa tare da sakin wani gigitaccen ihu.
Da sauri Jalal yasa ƙafarshi ya taƙa yatsun hannunshi tare da cewa.
“Sheeeyyt rufe min baki, uban me kuka sa a cikin fatar ragon sunan?”.
Cikin kerma da zare ido yace.
“Wlh bani ne na sakaba”.
Ƙara taka yatsun yayi tare da murjesu da ƙarfi yace.
“Me akasa a cikin fatar ragon? kuma waya saka? Nawa kuma aka biyaka?”.
Cikin sakin fitsarin azaba yace.
“Madarar fiyafiya ce aka saka cikin fatar. Hajia Mama ce ta saka! Dubu ɗari bakwai ta biyani”.
Wani irin murza yasun yayi da ƙarfi tare da cewa.
“Okay bari in daddage yatsun hannun da zaiyi kisan kai da amsar kuɗin yin kisan kai ɗin”.
Zuwa yanzu ya gigice ihu kawai yakeyi, shi kuwa Jalal rufe Windows ɗinsa yayi ya mishi ɗan karen duka.
Kana ya kira ɗaya daga cikin ma’akatansu na jami’an sirri na soja yazo ya tafi dashi.

A nan falon Shatu kuwa, a hankali Jamil da Yah Jafar Suka koma suka zauna.

Yana gaba Umaymah na binshi a baya a haka suka shigo.
“Aish Aish Aysha!”. Ya ɗan ƙare kiran da ƙarfi.
Da sauri Shatu ta miƙe da sauri ta nufo falon.
Ummi da sauran na biye da ita a baya.
Aunty Amina da Khadijah kuma suna zaune.
Da sauri ya kamo hannunta bisa kujera ya ajiyeta gefen Aunty Rahma da sauri yace.
“Bata nono yi sauri”.
Da sauri tace to tare da fara kiciniyar ɗago rigarta.
Ina gani yake bata sauri shiyasa cikin sauri ya ɗaura mata ita kan cinyarta.
Kana yasa hannunshi ta baya ya zuge zip ɗin rigar yayi ƙasa da ita.
Hannunshi yasa ya fito da breast ɗinta na dama.
Tare da ɗago kan Afreen daketa fidda wani irin numfarfashi alamun har yanzu numfashin bai dai-dai taba.

Da sauri kuwa ta damƙi nonon tare da fara zuƙa.

Wani irin dogon ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe a tare shi da ita.
Lokaci ɗaya kuma hawayensu ya kwaranyo bisa fuskokinsu.
Cikin sanyin murya yace.
“Alhamdulillah Aish kada kiyi kuka kiyi mata addu’o’in samun lfy ke wuce addu’aki gareta bata da hijabi”.
Hannunta tasa tana ƙara tallaɓe kan Babyn murya na rawa tace.
“Yah Allah ka bawa wannan baiwa taka lfy ka yaye mata wahalar shaƙar numfashi ka sauƙaƙa mata shi al’farmar Annabi da al’ƙur’ani.”
“Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati my Dear”.
Ya faɗa yana share mata hawayen fuskarta da hannunshi na hagu.

Su kuwa saura kab ajiyan zuciya sukayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”..
Sai lokacin ya ɗan kalli Aunty Rahma dake gefen Shatu tana zubda hawaye a hankali yace.
“So sorry my Aunty in Sha Allah babu komai likita yace, da shayar da ita shi akayi zaifi mata illa yanzu kuma shaƙane an mata duk wani taimakon gaggawa daya kamata”.
Cikin gamsuwa ta gyada kai.
Sai kuma ya ɗan taso tsaye sai lokacin yaga yawansu.
A hankali ya ɗan sunkuyar da kanshi cikin sanyi yace.
“Gimbiya Aminatu in sha Allah daga yau wannan al’adar zata kau a masarautar Joɗa dama duk wasu tarkacen al’adun daba addiniba ki gayawa Lamiɗo”.
Cikin jin daɗi tace.
“Ai ba ita kaɗai ba in dai ka yarda ka mulki masarautar Joɗa duk wata al’ada na masarautun gargajiya kana da damar datsesu ka wanzar da Sunnah”.
Wani irin dogon ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe.
Tabbas masarautar Joɗa tana buƙatar sabon Sarki sabon tsari sabon zubi bisa koyarwar musulunci da sunnar manzon Allah a kauda bidi’a a kawo sunna.
To amman shi baida ra’ayin mulki.
Cikin sanyi yace.
“Gyaran ba lallai sai ni ɗaya zan yi shi ba ai, kuma ko bani ke mulkiba zan iya bada shawara in an yarda a amsa”.
Cikin sauri Umaymah tace.
“Idan dai har kana son kauda al’adun a wanzar da sunna to dole ka mulki masarautar Joɗa da kanka”.
Kanshi kawai ya jingina jikin kujerar kana a hankali ya sunkuyo yana kallon Shatu dake cewa.
“Baiyi mulki Bama Umaymah ana neman ransa da na ahlinsa”.
Lamiɗo da Galadima dake shigowa ne dan jin lbrin abinda ya faru a bakin Jalal ne.
Suka haɗa baki wurin cewa.
“Ƙi gudu sa gudu, Shatu ke muke zaton zaki bashi ƙarfin guiwa kuma sai ki karaya da wuri haka.”
Da sauri su Umaymah kab suka ja da baya suka basu wurin zama.
Suna zama dai-dai lokacin kuma Shatu ta zare mamanta daga bakin Afreen ɗin cikin tsoron ganin yadda ta ke ɗan yunƙuri tana kwaro amai.
Da sauri Sheykh ya matso tare da cewa.
“Innalillahi”.
Ita kuwa Shatu ɗagota tayi da sauri ganin yadda taketa yunƙirin kakarin amai ba ƙaƙƙautawa.
Da sauri Gimbiya Aminatu ta matso tana cewa.
“Subahanallahi”
Shi kuwa Sheykh wayarshi dake cikin al’jihun rigarsa ya zaro da sauri ya kira Dr Lukman Ibrahim yana ɗagawa yace.
“Dr Baby fa sai amai takeyi ba tsayawa”.
Da sauri Dr Lukman Ibrahim yace.
“Alhamdulillah tasha Mamanta ko?”.

“Eh tasha, tana shane ma ta fara aman”.
Ya bashi amsa.

“Yauwa haka akeso Sheykh ba komai yanzu duk kaifin gubar ya karye ta harar dashi yanzu zatayi bacci kuyi mata wonka da ruwan sanyi.
Tana farkawa kuyi mata wonka da ruwan sanyi kuma zata dawo dai-dai da izin Ubangiji”.

Da sauri ya katse kiran bayan yace.
“Ok thanks Dr”.

Ita kuwa Shatu ajiyan zuciya ta sauƙe tare da meda kanta ta jingina da kujera ganin ta bar aman.
Shi kuwa Umaymah ya kalla tare dayi mata bayanin da Dr yayi mishi.
Da sauri ta iso garesu ta amshi ƴar kana ta wuce Bathroom.
Wonka tai mata da ruwan sanyi ɗan kwalinta ta wore ta naɗeta a ciki.
Tuni tayi bacci kafinma ta fito da ita.
A hankali ta zauna bakin gadon Shatu gefen Aunty Amina da Khadijah dake waya da Abboi Appansu kenan tanai mishi bayanin duk abinda ya faru.
Cikin tashin hankali da mamaki Abboi yace.
“Subahanallahi, kai wannan gida nasu akwai sarƙaƙiya.
yanzu ina Parvina?”.
A hankali tace.
“Tana falo can naji kamar harda Lamiɗo ma yazo da kanshi, amman yanzu yarinyar gata nan ta farfaɗo harma tayi bacci”.
Cikin kula da son ahlinshi especially Parvina a hankali yace.
“In sha Allah nida Dedden ku da Al’ameen zumu zo gobe gobe da izinin ubangiji, dama tun tuni ma shiryawa hakan, in Parvina ta shigo kice ta kirani”.
Da sauri tace.
“Toh Appa”.
Guntun murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“Babanku kika gayawa ne?”.
Cikin alamun karaya da lamarin gidajen sarauta tace.
“Eh Umaymah”.
Kai kawai ta gyaɗa tare da gyarawa jaririyar kwanciya.
Aunty Amina kuwa sunkuyowa tayi tana kallon fuskar Babyn.

A falon Shatu kuwa sosai Lamiɗo ya kwantar mata da hankali kana suka tafi Gimbiya Aminatu na biye dasu a baya.
Bayan ta shiga ta ƙara duba Babyn.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button