GARKUWA PART 3

Umaymah kuwa fitowa falon tayi suka zauna a nan.
Ita kuwa Shatu bedroom ta koma ta konta tasa yarta a gaba tofi takeyi mata tana kallon fuskarta Allah ya sani ji takeyi kamar bata tsiraba shiyasa har yanzu hanjin cikinta ke kaɗawa.
A hankali ta jawo wayarta.
Abboi ta kira, bayan sun gama gaisa ya alhinta abinda ya faru ya ɗaura da cewa.
“Dama can gobe zamu zo ko ba komai zanzo inga amryata, inga mummunace ko kekyawa”.
Ya ƙare mgnar da ƴar raha da son kontar mata sa hankali.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Allah ya kawomku lfy Appa na, da Ummey na da Junainah take kamafa”.
Tayi mgnar cikin jin kunya duk da yawan shaƙuwa dake tsakaninsu.
Murmushi yayi tare da kallon Dedde dake jin duk tattaunawar da sukeyi yace.
“Ato kekkyawace sadaki ta garken shanun Bappa zai bata”.
Dariya sukayi baki ɗayansu kana sukayi sallama da juna.
Daga nan kuma Bappa ta kira, wanda tun ɗazu Abboi ya shaida masa abinda ya faru yana ɗagawa yace.
“Shatu na ya jikin Aisha ƙaramar dai?”.
A hankali ta ɗan shafa kan Afreen tare da cewa.
“Alhamdulillah Bappa na ba komai ta samu lfy gatama tana bacci”.
Cikin jin daɗi yace.
“Alhamdulillah ga Ummeynki tun ɗazu hankalinta a tashe yake”.
Amsa Ummey tayi cikin kula tace.
“Boɗɗo na me sukayi miki?”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ummey na so sukayi su kashe miki jikarki tun baki ganta ba, dan Allah da Manzonsa Ummey na kizo gobe”.
Cikin kaɗuwa da begen son ganin Shatu da ƴar tata tace.
“In Sha Allah Gobe za muzo tare da Abboi da izin Ubangiji”.
Cikin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah naji daɗi na, Gobe ina cikin gatana”.
Su kuma ta kalli Umaymah da ta shigo yanzu tare da cewa.
“Alhamdulillah Umaymah na Gobe Ummey na zatazo da Bappa na da Deddena da Abboi”.
Cikin wani irin masha’hurin farin cikin alamun son tabbatuwar wani abu Umaymah tace.
“Alhamdulillah Allah ya kawo mana su lfy”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Haka dai akayi wunin sunan jiki a mace da abinda ya faru.
Sai can da yamma ne da Afreen ɗin ta farka daga baccin suka ganta lfy lau kafin hankalin kowa ya kwanta.
Nan Umaymah suka fito da kayan suna na gani na burgewa, da aka haɗawa mai jego da Ɗiyarta.
Kayan da Sheykh yayi musu kuwa abin sai dai ace son barka.
Gaba ɗaya wunin yau shima ya kasa fita ko nan da can tunda akayi sallan Jumma’a ya shigo ya wuce Side ɗinsa.
Bini-bini ya kira Shatu ko Umaymah ya tambayi jikin yarinya.
Bayan sun dawo sallan la’asar ne.
Jalal ya biyoshi har cikin falonshi, gefen Haroon ya zauna kana a hankali yace.
“Shima sarkin al’adun sunan harda shi a sahun Magauta sai dai biya shi Hajia Mama tayi da dubu ɗari bakwai daga baya yace min tace in ƴar ta rasu zata cikata mishi dubu ɗari uku ya zama one million”.
Cikin mamaki Haroon yace.
“Ikon Allah ikon gaske, wai ita wannan shegiyar matar meyasa bazamu fito mata a fili bane mu nuna mata mun san komai mu kuma juyo kanta”.
Cikin taune lips Sheykh yace.
“Uhumm bazaku gane bane,”.
Da sauri Umaymah dake shigowa tace.
“Ni na gaji bazamu gane me ɗin ba kuma”.
Cikin wani irin yanayi mai rauni cikin sanyi murya na rawa yace.
“Affan ina ɗagawa Hajia Mama kafane sabida Affan ina jin takaici in na tuno a cikinta Affan ya fito, ku kun san waye Affan kun kuma san asalin zahirin gskyar so da ƙaunar da yake mana, kunsan yadda yake faman faɗa da yaƙin sauya mahaifiyarshi daga mummunan ɗabi’a eh zuwa kekkyawan ɗabi’a.
Ta yaya zanci zarafin ta al’halin Affan ya ɗaukeni matsayin Uba ya ɗaukeni ciki ɗaya muka fito,kada ku manta son da Affan kewa Mameynmu Jalal ka duba tarin son da Affan yakeyi muku kaida Jamil.
Ko a lahira wani kanci al’barkacin wani.
Ina barine sabida ko Affan zai samu nasarar juya halinta”.
Ya ƙarashe mgnar hawaye na zubo mishi.
Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi tabbas sun san waye Affan ko su Jalal basa so da shaƙuwa dashi kamar Affan.
A hankali yace.
“Duk abinda nasa Affan zaiyi minshi babu musu koda baya son abin duk inda na aikeshi zaije min duk abinda na bashi zaɓi zaɓina yake bi, Affan da kanshi ya fara nuna min baya son inci abincin Hajia Mama wacce take uwace a garesa, yayi hakane sabida zargin tana samin abu a cikin abinci.
Yasha yin kuka yana mgiya in ya tareta tana wani abun me zanyiwa Affan in nuna mishi halaccin ɗan uwantaka banda in rufawa mahaifiyarshi asiri”.
Shiru yayi ganin kiran Affan daya shigo wayarshi.
Jiki a mace itama Umaymah ta zauna.
A hankali ya kara wayar a kunne bayan a amsa kiran.
“Assalamu alaikum Hamma Jabeer”.
Affan ya faɗa cikin tsananin so da ladabi ga ɗan uwan nasa.
“Wa alaikassalam Affan kana lfy”.
Sheykh yayi mgn yana mai jin wasu zafafan hawaye na tsastsafo mishi.
Murmushi Affan yayi cikin yanayin shi na Happy mood yace.
“Alhamdulillah Hamma Dr Akarmakallu Yah Sheykh, mun sauƙo lfy”.
Jingina bayan sa yayi da kujera tare da cewa.
“Alhamdulillah Affan Allah yayi ma al’baka”.
Da sauri yace.
“Amin Hammana”.
Sai kuma yace.
“Jamil ne yazo ya daukomu a airport to yanzu mun biya mun sauƙe Yah Sulaiman da Malam Abubakar.
To gani tare dasu Giɗi ɗin yanzu su ina zamu kaisu, umarni nake jira Hamma?”.
Cikin sanyi yace.
“Alhamdulillah Affan ku dawo dasu masarautar Joɗa ku wuce dasu Part ɗinsu Jalal a sauƙesu a can.
Bawa Jamil wayar”.
Da sauri yace.
“An gama sir yadda kace haka za’ayi ga Jamil ɗin”.
Ya kare mgnar yana miƙawa Jamil wayar.
Saƙale wayar yayi da kafaɗarsa tare da cewa.
“Assalamu alaikum Yah Sheykh”.
Gyaɗa al’kyabbar jikinshi yayi tare da cewa.
“Wa alaikassalam Jamil ka kaisu part ɗinku ɗakinka ka nuna musu Bathroom suyi wonka.
Aunty Rahma zata kawo musu abinci ka tabbatar sunci sun ƙoshi.
Sannan Jalal zai ɗauki Dr Kabir zaizo ya dubasu in sunada matsalar lfy zai kula da komai”.
Cikin gamsuwa Jamil yace to yana kallon kekyawar fuskar Giɗi ta madubin motar.
Shi kuwa Sheykh a hankali yace.
“Toh Umaymah a hakan ta yaya zan tozarta mahaifiyar Affan wanda duk munin halinta uwa dai uwace.”
Cikin rauni Umaymah tace.
“Wannan hakane Jazlaan amman Hajia Mama tanayi mana illa a rayuwa”.
Sosai jikin Haroon yayi sanyi.
Shi kuwa Sheykh Jalal ya kalla tare da cewa.
“Kaje Valli ka taho da Dr Kabir”.
Jiki a mace Jalal yace to kana ya miƙe ya fita.
Umaymah na biye dashi a baya, har taje bakin ƙofar fita a hankali yace.
“Ayyah Umaymah Ɗiyar taki ta kawo min ɗiyar tawa mana in ganta”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Toh”.
Shi kuwa Haroon da sauri yace.
“To bari in baka wuri dan nasan dai uwar ɗiya za’a gani ba ɗiyaba”.
A hankali yace.
“Mutun da abinsa”.
Dariya Haroon yayi kana ya nufi ƙofar da zata sadashi da Garden.
A hankali ta turo ƙofar Bedroom ɗinsa.
Tare da cewa.
“Assalamu alaikum”.
Cikin wani irin happy yace.
“Wa alaikissalam”.
sai kuma ya juyo ya fuskanceta tare da buɗe mata hannunshi.
Cikin sauri ta faɗa jikinshi ruggume da Afreen haɗe su yayi ya ruggume tare da cewa.
“Alhamdulillah ya Allah ka tsare min ahlinna ka cika mana farin cikinmu”.
“Amin ya Allah”. Ta faɗa a hankali sai kuma ya jawo hannunta suka zauna a bakin gadon.
Cikin narke fuska yace.
“Nayi fushi Aish tun ɗazufa na aika kizo baki zoba sai yanzu”.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah Malam sallan la’asar nakeyi”.
Cikin sauri ya kalleta tare da cewa.
“Kai haba dai Aish da gaske shine baki gaya minba yaushe kika fara salla”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Yoh ai dama ina salla”.
Lakace hancinta yayi tare da cewa.
“Batun gsky dai my dear yaushe kika samu tsarki?”.
Cikin nitsuwa tace.
“Yau da safe, nai wonka naci gaba da salla tunda naga jinin biƙin ya ɗauke na samu tsarki”.
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“Masha Allah, jego yayi kyau kenan Boɗɗo na, dama wasu matan kafin satin sunama sun samu tsarki sun fara salla, kinga kema kina ɗaya daga cikinsu wasu kuma sai anyi arba’in ma, wasu har hamsin suna likin.
Koda yake ke dama al’adarma kwana uku kikeyi ko”.
Kai ta gyaɗa mishi.
Hannunshi ya cusa ƙasan pillow’nshi tare da zaro key ɗin sabuwar mota dal a leda.
Kamo hannun ta yayi ya danƙa mata key ɗin tare da cewa.
“Al’ada kwana uku baƙi kwana bakwai kai naji daɗi na, na more”.
Da sauri ta buɗe tafin hannunta tare da kallon key ɗin sai kuma ta lumshe idonta jin ya manna mata tattausan lips ɗinsa a goshi ya sake mata sassayan kiss.
Tare da cewa.
“Taki ce motar sai dai bani son kiyi tuƙi nafi son a jamin ke, sai daifa bana miji zai jamin keba.
Sara taki zata zama yar rakiyarki mai jan mota da tayaki kula da Babynmu, duk inda kuke in bana kusa daku.
Gimbiya Aminatu zata bamu wata mai girki”.
Cikin wani irin farin cikin ta ruggumeshi gam-gam a jikinta.
Da sauri yace.
“Wayyo Aish zaki danne Mimi na”.
Da sauri ta kwantar da Afreen gefe, kana ta faɗa jikinshi ta rungume shi.
Murmushi yayi mai cike da farin ciki cikin wasa yace.
“Zaki bani abin daɗi?”.
Da sauri tace.
“Ban workeba”.
Dariya mai ɗan sauti yayi tare da haɗe bakinsu wuri guda.