NOVELS

GARKUWA PART 3

Washe gari ranar asabar yau babu aiki.
Da misalin ƙarfe goma na safe jirginsu Abboi ya sauƙa cikin birnin Ɓadamaya.

Kai tsaye Salmanu yayi musu jagora zuwa Rugar Bani dan a take suna sauƙa wasu tsala-tsalan motoci guda biyar suka iso wanda dama su tun jiya suka iso.
A ƙasan plate number motocin akwai tambarin hatimin kan shanu a ƙasa ansa Abboi, irin tambarin dake jikin jiragen Abboi kenan.

Suna zuwa kuwa babu ɓata lokacin suka isa har cikin gida.
Inda nan Arɗo Bani da kanshi da sauran dattawan sukazo.
Bayan sun gaggaisane Abboi ya ɗan yi gyaran murya tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah lallai komai yayi forko to tabbas yana da ƙarshe, to bayan bincike da bin diddigi dai mun gama fahimtar inane asalin wannan baiwar Allah’n kuma munada yaƙinin daga masararutar Joɗa ta fito.
To yau dai kam ranar data kamata mu shiga da ita ciki da yardar ubangiji tazo.
Kamar yadda muka tsara, yanzu zamu tafi”.
Cikin tsananin jin daɗi da kuma fargabar ko ya al’amarin zai kasance Bappa yace.
“Alhamdulillah mu duk a shirye muke, fatanmu Allah yasa ina munje ta tuna baya, ta tuno ita wacece”.
Da sauri Arɗo Bani yace.
“In Sha Allah ma zata tuna Malam Babayo”.
“Allah yasa haka”.
Al’ameen ya faɗa.
Amin Amin sukace kana duk suka miƙe suka fito.

Kana Bappa yazo yacewa Ummey da Dedde su fito.
Nan suka mara musu baya.

Mota ɗaya Bappa da Abboi da Arɗo Bani suka shiga.
Ummey da Dadde da Al’ameen kuwa suma mota ɗaya suka shiga.
Sauran kuma ƴan tsaronsu ne a ciki sai motar Yah Salmanu da Hafsi ƙanwar Shatu a haka suka fito daga Rugar Bani suka nufi Masarautar Joɗa.

A hankali Ummey ta jingine kanta da jikin kujera tare da dafe ƙahon zuciyarta a hankali ta furta innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Sabida tsananin tsinkewar da zuciyarta keyi Dedde kuwa hankalinta naga makiyayan dake zirya.

A nan cikin birnin Ɓadamaya a tsakiyar Masarautar Joɗa kuwa.

Gaba ɗaya su Umaymah suna falon Shatu.
Aunty Rahma ce da su Sara a kitchin, Aunty Juwairiyya tana part ɗinta da Hibba.

Junainah da Ishma kuwa suna kitchen tare da Aunty Rahma.
Kowa sabgar gabansa keyi.
A hankali Shatu ta miƙe ta nufi ƙofar falon Sheykh da sallama a bakinta.

Shiru ba kowa a falon tray’n breakfast ɗinshi shida Haroon ta ajiye bisa Dinning table.
Ganin ba kowane yasa ta turo kanta cikin bedroom ɗin.

Shiru ba kowa a hankali ta ƙara so ciki tana cewa.
“Salam Yah Sheykh”. Ƙofar bathroom ta matso a hankali ta tura ba kowa a ciki komai yana kimtse tsab-tsab.
“Toh ina yaje kuma yau Lahadi kuma ai babu inda zaije”.
Shiru tayi tare da juyowa ta matso tsakiyar ɗakin jujjuya kanta tayi ba mutun ba alaman mutun a ɗaki.
Har ta juya zata fita, sai kuma tayi sauri ta juyo tazo bakin gadonshi, abun data hanƙo ƙasan pillow’nshi ne yasa ta sunkuyowa da sauri hannunta tasa ta zaronshi.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Ta faɗa jiki na rawa tare da sakin fuskar robar da Sheykh ake amfani da ita a matsayin Jahan.
Da sauri ta juyo da nufin zata fita, sabida tsoron daya rufeta.
Sai kuma tayi sauri taja da baya tare da zare idanunta dai-dai lokacin da ta iso jikin marfin wodurob ɗin sa
Wanda yayi dai-dai da lokacin da Sheykh ya turo marfi ya fito.
A gigice take jujjuya kai tare da zaro ido.
Sai kuma ta juya da sauri ta kalli fuskarnar da ƙarfi ta buɗe baki tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun Yah Sheykh”.
Da sauri yasa hannunshi ya kamo nata ya fizgota jikinshi cikin haɗe fuskarsu wuri ɗaya yace.
“Na’am Aysha please kada kiyi ihu tsaya nitsu nine Muhammad Jabeer Yah Sheykh mijinki Abu Afreen”.
Cikin yanayi kaɗuwa tace.
“Yah Sheykh kai mutum ne ko al’jan”.
Da sauri ya kamo hannunta suka iso gaba durowar.
Buɗe ƙofar yayi, kana a hankali yasa hannunshin ya ture, al’kyabbas ɗin shi dake jere a hanga a saƙale, sai ga wani ƙofa mai kamar glass.
A hankali yace.
“Aysha nitsu ki jini kinji ko”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Toh”.
Kanshi ya gyaɗa kana a hankali yace.
“Kinga wannan wurin ko?”.
Da sauri tace.
“Eh naga kamar ƙofa ne”.
Jawota yayi suka ɗan matso hannunshi yasa ya tura ƙofar da sauri tace.
“Lahh”.
Sabida ganin wata ƴar siririyar hanya mai tsawo.
A hankali yace.
“Ni mutum ne Aish yanayin tsarin masararutar Joɗa ne yasa dole nake amfani da wasu ababen.
Kinga wanan hanyar har cikin bedroom ɗin Lamiɗo da Abba na duk akwai su.
Muna haɗuwa dasu a ɗakin Lamiɗo lokuta da dama.
In kina so anjima zan nuna miki, dan yanzu Lamiɗo ya rufe ƙofarsa ne da yanzu zamuje”.
Da sauri tace.
“Me kukeyi a ɓoyen”.
Jawo ƙofar yayi ya rufe kana a hankali yace.
“Ina wani aikine Aish Kuma aikin sirrine, tsawon shekaru inayi babu wanda ya sani sai Lamiɗo da Abba na da Umaymah sai yau kuma da kika zama ta uku”.
Ya ƙarashe mgnar yana jawota suka zauna bakin gado.
A hankali ta sauƙe numfashi ido ta zuba mishi a hankali tace.
“Kai SS ne ko Yah Sheykh?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ba’a faɗa kiyi shiru kada wani yaji kinji ko sirri ne Boɗɗo na”.
Murmushi mai cike da jijjina tayi mishi.
Shi kuwa ruggume ta yayi ya koma baya ya kwanta.

Dai-dai lokacin kuwa motar Salmanu dake gaban motocin su Abboi ta kusa kai cikin matsarautar Joɗa bayan an wangale musu gate.

Wani irin rumtse ido da ƙarfi Ummey tayi tare dasa kanta bisa guiwowinta sabida wani irin masifeffen tsarawa da kanta yayi da azaban ƙarfi.

Kai tsaye bakin part ɗin su Sheykh Salmanu ya nufa dasu sai dai Motar Abboi da sauran duk a can baya bakin fada suka tsaya inda Bappa ya nuna musu.

Yadda suke ƙara kusanto Part ɗin su haka sarawa da bugun zuciyar da Ummey keyi yake ƙaruwa.

A can cikin falon Shatu ma, da sauri Umaymah da Mamma Suka kalli juna sabida masifar bugawa da ƙirazansu sukayi.

Sheykh kuwa da ƙarfi ya ruggume Shatu sabida ji yayi tamkar zuciyarsa zata faso ƙirjinsa ta fito woje.
Jalal da ke Part ɗin Yah Jafar da sauri ya rumtse idanunshi shida Yah Jafar ɗin.

Hakama Jamil dake tare dasu Gaini.

A hankali motocin sukayi parking.
Ummey kuwa wani irin ƙara rumtse idanunta tayi da masifan karfi.
Dedde kuwa a hankali ta buɗe ƙofar.
Ta sako ƙafarsa cikin shigarta ta al’farma.

Shi kuwa Al’ameen da sauri ya zagayo ya buɗe wa Ummey kofar tare da cewa.
“Ummey mun iso bismillah”.
Cikin tsananin danne sarawar da kanta keyi ta ɗago jajayen idanunta a hankali ta zuro ƙafafuwan woje.

Ras ras Din dab din dab haka zuciyarta ta bada wasu tagwayen bugu.
Da sauri tasa hannunta ta dafe ƙirjinta.
Dedde kuwa a hankali ta zagayo inda take.
Shi kuwa Al’ameen a hankali yace.
“Bismillah ku shiga ga ƙofar”.
A hankali Dedde tace to kana ta nufi ƙofar.
Ita kuwa Ummey cikin rawan jiki ta ɗaga ƙafarta ta dama ta ɗaura kan barandar tare da ƙara dafe ƙirjinta da rumtse idanunta sabida jujjuyawan da kanta ya fara.
Shi kuwa Al’ameeen bayansu yabi.

Shi kuwa Salmanu a hankali ya kalli Hafsi ƙanwar Shatu dake bin Khadijah.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
“Ko in ɗagaki ne in kaiki”.
Cikin jin kunya tace.
“A a Yah Salmanu zan shiga da ƙafata”.

Su Bappa kuwa Sarkin ƙofa ne yayi musu iso zuwa cikin fada.

A hankali Dedde ta kai hannunta ta kama handil ɗin ƙofar falon ta murɗa tare da turawa kana tasa ƙafarta ta dama ciki bakinta ɗauke da sallama.

Aunty Rahma dake fitowa daga kitchen Junainah na biye da ita da sauri ta ɗan juyo ta kalli Dedde tare da cewa.
“Wa alaikassalam”.
Ta ƙarashe amsa sallamar tana matsowa dan ganin wani irin fitinenne kama da Dedde keyi da Shatu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button