GARKUWA PART 3

Cikin yanayin happy take sarrafa alaƙarsu har tsawon 15min.
Shi kuwa Sheykh gaba ɗaya ya gama gigicewa.
A hankali yake shafa cikin dan tsoron duk abinda zai cutar dashi yake.
Ya kuma lura yau Shatu farin cikinta yasata, ƙarin ƙaimi.
A hankali ya kai bakinshi kusa da kunnenta cikin daburtacciyar murya mafi rauni yace.
“Hashhhhh thanks my dear Aish. Babyna fa”.
Tsawon lokaci kana ta narke a jikinshi cikin tarin gajiya da maida numfashi.
Murmushi mai cike da jin daɗi da tarin gamsuwa yayi.
Kana ya shafa fuskarta sannan ya tallabeta suka wuce bedroom ɗin sa.
Shi ya fara shiga yayi wanka ita kuwa tana konce, saida ya fito ta shiga tayi tuni lokacin kuma magriba tayi.
A can ƙasar Cameroon kuwa, ɓangaren su
Junaina kuwa kallon Ummey tayi jin yadda take jiyo hayaniya da dariyar mutane da muryar Ummu dake cewa Shatu kada ki gudufa.
Mikawa Ummey wayar tayi tana cewa.
“Ummey sai dariya suke yi”.
karɓar wayar Ummey tayi takashe, kana ta miƙa dan yin al’wala.
A ɓangaren su Shatu kuwa washe garin ranar ma tashayar da Sheykh zallar madarar daɗi dan kuwa yau kusan ita tayi tukin.
Washegari
Dasafe Sheykh yashirya cikin shigarsa ta al’farma yanufi General Hospital Ɓadayama wanda dama yake zuwa duk ƙarshen mako.
Yau kuma saura kwana biyu su Ummey su dawo.
Alhamdulillah tuni su iro sun iso da garken shanun da Appa Alhaji Abboi kenan ya sake haɗawa Bappa kama daga shanu tumaki awaki.
Raƙuma da dawakai.
Sai kaji da zabbi da aka sassakasu cikin kwandunan saƙar mari aka ratayesu a jikin dawakai.
Alhamdulillah Arɗo Bani da Alhaji Haro da Alhaji Umaru da dai sauran daddatawan garin su, suka tarbi su iro suka nuna musu tsohon garken Bappa, nan suka sauƙa, kana suka gyara duk wani abu daya kamata su gyara.
Arɗo Bani kuwa da kanshi ya turo uwargidansa Maman Ya Salmanu, da kuma matar Alhaji Haro Maman Junaidu sukazo suka buɗe gidan Bappa suka kimtsa musu komai suka share komai yayi gwanin ban sha’awa.
Kana daga gidan Arɗo Bani ake kawowa su Iro abinci, in sunyi tatsa kuma sadaka suke rawaba al’majirai na cikin Shikan.
Alhamdulillah a can Kamaru kuma su Ummey da Bappa da Inna amaryar Bappa da Junainah duk sun gama shirinsu.
Tuni Al’ameeen ya gama musu komai na tafiya.
A ɓankaren Shatu kuwa itama sai shiri take tayi, Sheikh da kansa ya gayawa Umaymah nan ita kuma ta gayawa Lamiɗo.
Yau Al’hamis. Kuma yaune su Ummey zasu dawo.
Sheykh ne zaune a office ɗin shi na Valli.
Haka nan yaji zuciyarsa na sinkewa.
Gaba ɗaya sai hankalinsa ya koma kan zantukan Hajia Mama.
Ajiyan zuciya mai nauyi ya ɗan fesar, kana ya jawo wayarshi.
Ɗan lallatsawa yayi kana ya karata a kunne.
Shatu dake tsaye gaban dreesing mirror’n tana kimtsa kayyakin kolliyar ta, cikin yar ƙaramar jakane alamun shirin tafiya, jin wayarta na ringing yasa tasa hannu ta ɗago ganin sunan dake saman wayar.
Habibi Da’iman, murmushi tayi tare da amsa wayar kana ta kara a kunne, cikin sanyi tace.
“Assalamu alaikum Yah mu’allim”.
Sassanyan numfashin ya fesar tare da sauƙe ajiyan zuciya kana yace.
“Wa alaikassalam Mar’atussaliha, kina lfy ko”.
Kai ta gyaɗa kamar tana gabanshi kana a hankali tace.
“Lfy lau Alhamdulillah”
Da sauri yace.
“Baby nafa”.
Murmushi tayi kana tace.
“Alhamdulillah Doctor duk muna lfy, sai dai muna kewarka Yah Sheykh”.
Cikin lumshe ido yace.
“Ina nan tare daku”.
Cikin ta ɗan shafa kana tace.
“Hamma Jabeer nifa na gama shirina”.
Ƴar karamar dariya yayi fahimtar duk sunan da zata kirashi dashi yanada ma’anarsa namusannan kuma ko wanne suna a gaɓar daya dace dashi take kiranshi.
Takan ce mishi Doctor a duk lokacin da yake bincikar lfyarta ko kuma takejin wani abu nata na mata ciwo, to kai tsaye da Dakta take kiranshi da yaji haka kuma yasan akwai abinda zatace mishi na damunta.
Kana duk sanda zata ce mishi Hamma Jabeer takanyi mgna dashi kai tsaye a matsayin Garkuwanta kuma ƴaƴanta ɗan uwa yadda da yaji haka yasan zatayi mishi mgn kan nuna shi matsayin ƴan uwansa natane ƴan uwanta nashine, kuma a kan danginshi zatayi mgn ko nata.
In Kuma yaji tace mishi.
Malam to yasan akan abinda ya shafi addini zatayi mishi mgn ko tambaya da dai makamantansu.
In kuwa yaji Yah Sheykh to yasan fagen da ake ya lura tana jin daɗin sunan, dan takan kira sunan ne cike da shauƙi mai ratsa zuciya.
A hankali yace.
“To Boɗɗon Ummey ki shirya da kyau, dan nima zaki shirya min dare nan ki bani kyautar kwana ukun da zakiyi”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kai Hamma Jabeer bazan hutaba”.
Da sauri yace.
“Zaki huta mana”.
Uhum kawai tace.
Shi kuwa cikin nitsuwa yace.
“Aysha manna wayar a jikin cikin namu ko”.
Da sauri tace.
“Toh Malam ayi addu’ar da ni”.
Tayi mgnar sabida sanin addu’a zaiwa cikin.
Ai kuwa tana manna wayar a cikinta ya fara addu’o’in masu ratsa jiki.
Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
“Laaah Malam kaji Baby tana motsawa”.
Murmushi yayi shima kana yaci gaba da Addu’o’in.
Saida ya ida kana sukayi sallama.
Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k wanda anfi yawan posting in kunaso kiyi min TRANSFER 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa sai kiyi screenshort na Debit alert ɗin ki ki turomin 09097853276 ta whatsapp sai in saki a group akwai Normal group Kuma 300 ne kuma ta ac ɗin zaku biya in baki da halin biya ta ac ki sayi katin Mtn na ɗari uku kacal ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276.
*Yahunde International airport*
By
*GARKUWAR FULANI*
4/6/21, 4:15 PM – &: Ƙarfe huɗu dai-dai, na yamma, wasu irin motoci ne masu masifar kyau da tsaruwa.
Suke kutsa kai cikin airport ɗin, wanda a ƙalla sun kai bakwai.
bisa alamu duk akwai cikekken nasaba da dama, dan har can asalin wurin da jirgi yake biyu daga cikin motocin suka wuce.
Kana biyar kuma suka tsaya a ainihin harabar.
A hankali aka buɗe motocin.
Alhaji Abboi ne ya fara fitowa.
Sai Bappa kana Al’ameen da wasu matasa uku masu kama da Al’ameen sai wata kekkyawar budurwa mai kama da Shatu sak wacce take riƙe da hannun Junainah.
Sai Ummey da Inna Amarya da suka fito.
Bisa alamu duka, sauran rakiya sukayiwa su Bappa.
Gyara tsayuwarsu sukayi dan ganin matafiya nata shiga cikin jirgi, wanda yake ɗauke da tambarin Abboi.
Cikin murmushi Appa ya miƙawa Bappa hannu sukayi musabaha kana a hankali yace.
“Toh Malam Babayo Allah ya maidaku lfy ya kiyaye hanya”.
Cikin jin daɗi Bappa yace.
“Amin Amin Abboi Ubangiji ya saka maka da mafi kyawun sakamako”.
Cikin jin daɗin Addu’a Al’ameen da saura zaratan samarin nan sukace.
“Amin ya Allah”.
Sai kuma sukayi shiru jin Appa na cewa.
“In kun isa ka gaida min Parvina da kyau, kana aci gaba da ɓoye mata abinda mu muka fahimta,
har sai lokacin da ido zaiga ido muna da kekkyawan yaƙinin duk sanda taga wasu cikin masarautar Joɗa mu samman in ya shafi ahlinta in sha Allah zata iya tuno komai na baya”.
Ya ƙarashe mgnar a hankali yadda ko su Al’ameen basu jiba bare su Ummey.
Cikin gyaɗa kai Bappa yace.
“Inama ji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe da izinin ubangiji.
Dan yanzu dai nasan muna komawa Shatu zata zo, to inma batazo da waniba ina zaton zata zo da mijin nata, kuma inma bata zo ɗinba idan ta haihu shine shirinmu ta sanadin haka Ummeynta zata shiga masarautar Joɗa ba tare da an zargi komaiba”.
Kai Appa ya gyaɗa tare da cewa.
“Tabbas komai ya kusa zuwa ƙarshe”.
Yar Kekkyawar budurwar nan kuma mai kama da Shatu hannun Junainah ta sake ganin Bappa na miƙo mata hannu alamun tazo su tafi.
Cikin sanyi Khadijah tace.
“Ayyah Junainah zamuyi kewarki.”
Da sauri Junainah tace.
“Adda Khadijah ina in Adda Shatu na ta haihu zakizo keda Dedde ko?”.
Kai Khadija ta jinjina tare da cewa.
“In sha Allah kuwa, zanzo ki gaida min ita da kyau kinji ko my Junnu kice mata duk Ahlin Abboi muna kewarta.”
Da sauri tace.
“To zan gaya mata, bey-bey Adda Khadijah sai kunzo”.
Tana faɗin haka ita da Bappa suka nufi cikin jirgi.
Ita kuwa Khadijah ruggume Ummey tayi tana zubda hawaye tace.
“Ummey zamuyi kewarki, dake da Junnu”.
Hannu Ummey tasa ta share mata hawayenta kana tace.
“Nanda wata biyu dai Shatuna zata haihu zakuzo mu gana”.