GARKUWA PART 3

Ina isa bakin kofar
Mamey natura kofar da sallama nashiga ɗakinta.
Da sauri naja natsaya nan bakin kofar.
Can na hangi Mamey na kwance.
Bisa gado tana bacci da alamun baccin mai nauyi ne.
Hajiya mama kuwa na tsaye a kanta da wata iriyar shiga da tafi kama data bokaye ko ince matsafa.
Da mamaki nake kallon
Hajia Mama dake tsaye bakin gadon sanye da wasu irin jajayen kaya tun daga samanta har ƙasa,
kanta babu ko ɗan kwali
hannunta rike da wani ƙwarya.
Tana yayyafawa Mamey
wani ruwa dake cikin ƙwaryar tare da yin wasu surutai da sukafi kama da surkullen matsafa.
“Innalillahi wa’inanna ilaihirraji’un, nafurta da karfi.
Da sauri nanufo in da Hajia Mama’n ke tsaye cikin ruɗani da kiɗima ina faɗin.
Meye hakan Hajia Mama? me kike mata? me kike zuba mata a jiki haka?.
Dasauri tajuyo kaina tasaka hannunta cikin ƙwaryar taɗibo ruwan tashiga watsamin tana ƙara matsoni,
kaucewa nashiga yi ina matsowa in da Mamey take kwance kamar gawa ko matsi batayi,
itako Hajia Mama masoni tarikayi tana watsamin ruwan,
Baki na buɗe da karfi sabida wani irin masifeffen suka da naji duk inda ruwan ya taɓa a jikina yanayi.
Ƙara watsomin tayi wanda yasa na ƙara kaucewa da sauri tare da buɗe baki da nufin yin ihun zafin da nakeji da kuma fargabar halin da Mamey na ke ciki.
Sai kawai naji harshena yafurta Innalillahi wa’inanna ilaihirraji’un,wannan kalmar narika nanawata da karfi madadin inyi ihu.”
Ita kuwa Hajia Mama da sauri tajuya cikin alamun tsoron tonuwar asirinta.
dan lokacin dare baiyi nisa sosai ba misalin ƙarfe goma ne,
da gudu tafita a ɗaki dan jin yadda na kara sautin salatin da nake.
Ita kuwa Hajia Mama tana fita part ɗinta ta nufa direct bathroom ɗinta ta shiga gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi number’n bokan ta takira yana ɗagawa cikin haki da fargabar a bin da zaije ya da wo tace.
“Boka yanzu nafito daga ɗakin matarnan na samu tayi bacci kamar yadda kace, kuma na watsa mata ruwan bata farka a sai daifa wani yaganni lokacin danake yayyafa mata ruwan maganin nan babban ɗanta Galadiman Masarautar Joɗa kenan ya ganni”.
Wani irin dariya irin nasu na hatsabibai bokan yayi kana yace.
“Toh daya ganki me yakeyi? me kuma yake cewa?”.
cikin rawar baki da soron da ya ziyarce ta gudun kada ai kin ya ɓaci tace.
“Sunan Allah yaketa ambata salati yaketayi babu ko kakkautawa da wasu addu’o’i”.
Cikin ɗan tsagaita dariyar mugayen bokan yace
“To aiki kam zaici amma dai akwai nakasu aciki, amma kada kidamu yanzu shi yaron zamu rufemasa baki zai dauwama kurma ba mgna a bakinsa bazai iya yin maganaba bazai iya furta komai ba haka zai dauwama ba mgn saidai yayi ta mai-mai-ta abinda yake cewa.
Sannan daga nan tagwayen kuma zamu haɗa ɗaya da bin mata ɗaya shaye-shaye shi kuma babban kinga zai zama kamar Mahaukaci, shi kuma wancan Jabeer ɗin na gaya miki tun yana ƙaramin akwai sihirin da wani yayi mishi kada ki damu dashi bazai taɓa yin aureba har gaban abadan ko an mishi bazai zauna da matarba, kinga kenan duk sun zama suna da matsalar da dole baza’a basu mulkiba sai dai a bawa ɗanki Affan tunda kinga shi Imran ɗan ɗaya kishiyar taki shine ƙarami kan Affan.”
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Yauwa boka na gode ni dama fatana ɗana yayi mulki dan bana son mulkin ya bar ɗakina tunda dai kace min tabbas cikin yaran Habibullah ne mijin wani zai gaji kakansa sarauta.
Dariya yayi tare da cewa.
“Kada ki damu mulki na gareki da ɗanki”.
Wa iyazubillah kaɗan kenan daga sharrin tsinannun shaiɗanu maƙiya Allah da Manzonsa bokaye taɓaɓɓu masu sa mai binsu ya taɓe ya gaza sauri a ranar da muminai ke sauri a bisa siraɗi.
Acan cikin ɗakin Mamey kuwa.
Sosai sautin addu’a da karatun da Jafar keyi yatsanan ta yana kankame da Mamey, wacce ke ƙwance ida nunta a rufe, har lokacin bata farka daga.
Baccin sihirin da akasa takeyi ba saboda nauyin. Baccin da suka je fata ciki.
Sheko bakinsa baya iya furta komai sai addu’o’in sai kuma hawaye da keta tsatstsafowa daga cikin ida nunsa sabida fargarba da kuma zafin da yakeji,
Abba kuwa dake can part ɗinsa da yake Part ɗin shi na natsakanin na matan nashi ne.
Yana cikin ɗakinsa dake sama.
Haka yasa yarinƙa jiyo muryar Jafar da irin addu’o’in dayake cikin kiɗima, da kajin addu’ar kasan acikin tsananin firgici da tashin hankali yake yinsa,
Wuf yamike yanufo part in Mamey kasan cewar babu wata tazara sakaninsu.
Gudu-gudu sauri-sauri ya isa.
Cikin hanzari yatura kofar bedroom ɗin Mamey cikin sananin tashin hankali da kaɗuwa ganin yadda Yah Jafar ke rungume da Mamey sai innalillahi yake da karfi hawaye yagama wanke fuskarsa idanunsa sun yi jazir saboda kuka da zafin da yakeji da fargabar ganin tamkar Mamey a mace take a kiɗime yanufo in da suke yana faɗin.
“Subahanallahi kai Jafar meya farune me ya sameta?”.
Yayi tambayar hankali a tashe, tare da miƙa hannu ya ɗago kan Mamey dake kan kafar Ya Jafar yashiga girgizata yana kiran sunan ta.
“Aisha! Aisha!! Ummu Jabeer!.
Gani shiru bata ko matsi sai dai tana numfashi ya tsananta firgicinsa.
Hankali a tashe yakuma kallon ya Jafar wanda keta addu’o’in babu ko kakkautawa.
Mai da kan Mamey’n yayi ya kwantar kan cinyar kafar Jafar.
Kana ya juya a kiɗime ya fita a ɗakin da sauri ya nufi sashin mahaifinsa Lamiɗo.
Shi ko ya Jafar cigaba da maimata innalillahi yakeyi yana zubda hawayen.
A can ɓangaren Hajia Mama kuwa.
fitowar ta daga ɗakinta kenan cike da jin daɗin yadda bokan ya karfafa mata guiwa tanajin daɗi a ranta yanzu komai zai tafi mata yadda take bukata zata rabu da zugar yayan Mamey da ita duk kowa ya huta, tana fita ta hangi Abba ta window yafita daga cikin part ɗinsa hankali a tashe.
Fuska ta ɗan yamusa tazauna saman ɗaya daga cikin kujerun parlour’n, can kuma tamike kamar an tsikareta tabi bayansa da sauri.
Acan shashin Lamiɗo kuwa.
Da sauri Lamiɗo da Galadima suka mike, bayan Abba yagama sanar musu abin da ke faruwa.
A tare suka fito suka nufi part ɗin Mamey’n.
Lamiɗo na gaba Galadima da Abba na biye dashi suka shiga ɗakin, in da Abba yabar Yah Jafar a haka suka iske shi yana ganinsu ya miƙe da sauri Mamey yashiga nuna wasu Lamiɗo da hannu yana kuka yana nuna musu ita da kwatanta musu yadda Hajia Mama tayi mata.
Da sauri Hajia Mama ta turo kofar dan taga shigowar su Lamiɗo’n.
Jafar kuwa yana ganinta yashiga nunata da hannu sai kuma ya nuna Mamey’n yana cigaba da ƙwatanta yadda tayi matan shidai baki kam babu shi sai dai addu’o’in da kuma kukan dayake tayi.
Gaba ɗaya su suka maida kallonsu kan Hajia Mama nan take Lamiɗo da Galadima da Abba suka ɗiga ayar tambaya a kanta.
itako ganin bawai magana Jafar ɗin keyiba sai bata damuba bata kuma fahimci cewa sun zargi meyafaru ba kuma basu gane me. Jafar ɗin yake cewa ba da hakan ba.
Hajia mama kuwa cikeda da karfin hali irin nata na makiran mugaye mata tafara tafa hannu tana masar kwalla tana faɗin
“Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un Jafar me nake gani haka me yasami Mamey’n ku? kayi magana mana”.
Sai kuma tasaki kuka mai haɗe da salati.
Lamiɗo ne yaɗanyi gyaran murya ganin Mamey’n tafara motsawa alamar tafarka daga nannauyan Baccin da take mikewa tayi zaune tare da zuba musu ido.
Da sauri suka ɗan matso gareta kana duk suka mai da hankalin su kanta.
Suna ce mata sannu Aisha, Amman shiru ba amsa.
Cikin tsananin sauri da tsoro Abba ya matso kusa da ita tare da zubawa yatsun kafarta ido mamaki cike da kiɗima yake kallon yatsun kafarta da suka fara sauya kamannin halitta suka koma kamar na tsuntsu.