GARKUWA PART 3

Bai wani jima sosai a Nigeria ba yakoma Madina sabida jin yakeyi ya tsani ƙasar Nigeria Especially Masarautar Joɗa.
Koda ya koma sosai ƴan uwan Sitti suka ga canji a rayuwarsa saida aka dage da addu’a kafin ya dawo hayyacinsa.
Daga nan suka ƙara kula ta musamman a kanshi suka zame mishi uwa uba ƙanne yayu sukeyi mishi komai.
Yakanyi shekara uku huɗu bai zoba.
Sai dai yana yawan sawa Jadda yazo mishi da Jamil Jalal Yah Jafar da Affan yawanci duk shekara zasu zo sau biyu hajji da umra wani shekaranma sau uku.
Ya maida hankali sa kan karatunsa da addu’a Allah ya baiya mishi Mameynshi a duk inda take ko a tsuntsuwar Boleru shi zaici gaba da rainonta da kula da ita iya rai da mutuwa.
Daga nan yayi master’s madadin ya dawo ya haɗe. PHD ɗinsa. daga nan yadawo Nigeria’n bisa tirsasawar Lamiɗo da Jadda da Galadima da Umaymah dake matsayin Uwa.
Dole ya yarda ya dawo ya sanyawa ƙannensa ido wajen kula da su dakuma tarbiyyan su dakuma neman hamaifiyar su da kula da yayansa yakuma zame musu Garkuwa Da kuma bincikar Magautansu wanda dalilin haka ya samu matakin SS wanda dama shine burinsa to kuma Alhamdulillah ya gane komai Especially da ya samu damar aikin SS wanda dama burinshi kenan a dole Lamiɗo ya sashi karantan likitancin.
A kwai sabo ƙauna tausayi da shaƙuwa da tsama tsakaninshi da kakanun nashi sosai.
Hajia Mama kuwa da gayya ya barta da wayonta ita tanayi mishi kallon biri shi yana mata kallon ayaba.
Dama kuma malam Musa.
Ya faɗa musu cewa sanadin Sheykh ɗin ne Mamey’n zata dawo yabasu lbrin iya abinda Allah ya sanar mishi cewa bata rasuba tana raye kuma tajuye daga tsuntsuwar dasuke tunani tadawo mutum tuntuni tun bayan tafiyarta da watanni.
(Rayuwa kenan takan iya sauyawa a duk san da Allah yaso domin shi yake juya daƙuƙu i zuwa sa’a wuni zuwa dare kwana zuwa shekara ya fidda matacce a cikin rayayye ko ya fidda rayayye a cikin matacciya)
Ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe baki ɗayansu da suke cikin falon.
Bayan ya Jafar yagama basu labarin yadda akayi da abinda ya sani har Mamey’n su ta juye ta zama tsuntsuwa da kuma yadda akayi shima yakoma baya magana sai kuka da karatu.
Gabaki ɗaya parlour’n ya kaure da ambaton sunan Allah da yiwa uban giji tasbihi.
Ita kam Mamey sai murmushi takeyi tare da maimata.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah alakulli halin”.
Affan kuwa kuka yakeyi tamkar ransa zai bar gangar jikinsa.
Cike da rauni Sheykh ya jawoshi jikinshi ya ruggumeshi suna masu zubda hawaye baki ɗayansu.
Cikin rauni da tausayin irin kukan ƙuncin da Affan keyi Lamiɗo ya gyara zama tare da yin gyaran murya kana ya juyo ya kalli Bappa tare da cewa.
“Ka bamu labarin yadda akayi.
Aishatu tashigo hannun ku”.
Ai kuwa kaf hankalin jamar parlour’n yadawo kan Bappa dan kowa nason jin yadda akayi Mamey’n tashigo hannunsa gaba ɗaya shi suka zuba ido.
A hankali yayi Bappa gyaran murya tare da gyara zamanshi kana ya ɗago hannunshi ya nuna Shatu da yatsarsa manuniya kana yace.
“Shatu itace sanadin.
Dan a lokacin da tashigo hannun mu mu muna mata kallon tsuntsuwar Boleru ne tsawon kusan wata bakwai muna tare da ita muna ganinta Giɗi yarona shike kula da ita saida ya zama tare suke cin abinci.
To Shatu itace ta fara ce mana ba tsuntsuwar Boleru bace mutunce ita a ranar wata jumma’a da tazo tare da mahaifin ta Alhaji Abboi wanda ni makiyayinsa ne.
Nan taga tsuntsuwar yara na son kamata su yaran damu manyan duk muna cewa tsuntsuwa ce.
Ita kuma tana cewa mutum ce.
Wanda haka yasa dole basu koma cikin birnin Yahunde a ranarba ita da mahaifinta suka kwana a gidana a Rugar Arɗo Babayo wanda nanne asalin mahaifata.
haka ta kwana tana gaɗin tsuntsuwar har dai Allah yanuna mana ikon sa da asuba tajuya ta dawo mutum a gaban idonmu,
Sai dai tana cikin larurar naƙuda.
Cikin ikon Allah ta haifu ta sauƙa lfy ta haifi ɗiyarta mace.
To lokacine mukaga sarƙar dake wuyanta.
Mai ɗauke da tambarin masarautar Joɗa kasan cewar masarautar fulɓe ce kuma mahaifin Alhaji Abboi abo kine ga Lamiɗo akan ɗan ziyarci juna kaɗan kaɗan to sanadin hakane Alhaji Abboi ya gane tambarin dake jin sarƙar na masarautar Joɗa ce.
Tofa anan muka gane cewa duk yadda akayi ita ahalin masarautar Joɗa ce.
Kuma Sarkin bakanmu ya tabbatar mana ita mutunce aikin sihirine to sai dai babu yadda za’ayi mu fuskanceku da mgnar kai tsaye tunda bamu san komai nakuba.”
Ɗan tsakaita maganar yayi yaɗan ja numfashi kana yaci gaba da faɗin.
“Ni banine mahaifin Shatu ba Alh Abboi shine mahaifinta ga kuma mahaifiyarta.
Ni makiyayin mahaifinta ne.
inayi masa kiwone yana biyan.
Mafi akasari duk karshen wata suna zuwa tare da ita nan Rugar Arɗo Babayo.
To ita Shatu tanason yanayin daji rugarmu shiyasa duk sanda zaizo da ita zai zo, in zai koma kuma wasu lokutan yakan koma yabarta anan Rugarmu da yake ranar Jumma’a yake zuwa, to sai ranar lahadi da yamma Al’ameen ko wani daga cikin yayunta yazo ya ɗauke ta su koma.
Yawan zuwasu shi yasa tasaba da da yarana sosai da mai ɗakina.
To amman zuwansu da Allah ya ƙaddara lamarin Ummey ta juye a gabanta fir babu yadda ba’ayi da ita ta komaba taƙi bin mahaifinta fir taƙi tace ita zata zauna da Ummey ita ta zaɓa Junainah suna.
Wannan yasa dole mahaifinta ya koma ya barta.
To lokacin da Ummey’n Shatu’n ta faɗo hannunmu muka kuma ga wannan sarkar dake wuyanta na masarautar Joɗa shine Alh Abboi yace mu ƙaura mu dawo nan.
Nigeria kusa da masarautar Joɗa cikin Rugar Bani dan tasami kusan ci da masarautar.
to nan fa muka dawo Nigeria har da ita Shatu’n dan taƙi yar da a raba su da Ummey’n ta ashe rabo ke jawota nan.
dole iyayenta suka haƙura suka barta tare dani.
Muna dawowa nan muka sata a makarantar cikin Shikan”.
Nan yaci gaba da basu labarin duk wani bayanin gwa-gwar mayar da
Shatu tayi a ka Ummey
duk sai da ya basu labari.
Ya ƙara da cewa.
“Lokacin da muka zo Nigeria da Ummey
wato (Mamey) Ba’ana naɗan shekaru sha takwas a duniya, lokacin (Parvina) wato Shatu kenan ita kuma du-du shekarun ta takwas ne,
to kafin mu dawo ma Mamey bata dawo daga haiyacin taba bata fara magana ba, lokacin da mukazo.
Nigeria Rugar Bani sai Ba’ana yace zai bata mgnin zata fara mgn kuma zata zama dai-dai sai dai zaiyi wuya ta tuna baya,
Amman zata dawo tayi mgn amman da sharadi. kasan cewar fatanmu ta tuna baya mu maidata ga ahlinta yasa mukace mun amince da sharaɗinsa wanda bamu san menene sharaɗin ba.
Shi saida ya fara bata mgnin kuma yace sai da sharaɗin in Ummey ta worke ta fara mgn muyi al’ƙawarin aura mishi Shatu.
To lokacin mu baƙine bamu san halinsa na ɓoyeba kuma burinmu da fatanmu ta worke mu maidata hannun ƴan uwanta sai muka amince mukayi mishi wannan al’ƙawarin bisa rashin sanin halin daga ranar Mata yake kiran Shatu.
Kullum Shatu ita ke zuwa gidansu Ba’ana da safe tana karɓawa Ummey magani a gunsa, dan shi tun tashin sa yake wannan cacube-cacuben nasa, so kullum.
Shike bawa Shatu magani ta kawo wa
Ummey tana sha har Ummey tadawo tafara magana sai dai bata iya tuna baya ba nan. Ba’ana’n ke ce mana duk randa taga wasu nata ko ƴan uwan ta ko wani abu nata zai yiwu tunanin ta
yadawo ta iya tuna baya.”
Sai kuma ya ɗan tsagaita tare da sauƙe numfashi kana a hankali yaci gaba da cewa.
“Toh tun daga ranar ne muka fara neman hanya da dalilin da zai haɗamu daku mutanen masarautar Joɗa.
Sabida munsan aikin sihirine dole akwai Magauta sannan a gefen Ba’ana kuwa ya addabemu ya hana Shatu salama duk mai sonta sai yaga bayanshi.